Chapter 31

943 73 0
                                    

🌻🌻🌻🌻🌻🌻🌻🌻

              *ZYNAH*

(An Interesting Luv Story 2017)

By Aisha Muhammad (Mzz Daddy💋)

*BAIWA WRITER'S ASSOCIATION*

QUOTE:-"When someone breaks your trust. Don't' feel stupid for trusting them. You didn't' do anything wrong, they're just an untrustworthy person."

     
                 3⃣1⃣

     *ASHRAF* ya kaiwa mahaifinshi number inda Abba nasa numbern a waya yaga ashe yanada contact din, dan number wani business partner dinshi ne. Kallon *ASHRAF* yayi yace "toh kai wannan numbern Alhaji Muhammad mai dala ne" cike da mamaki yace "Abba kasanshi be?" Abba yace "kwarai kuwa, farin sani ma, ai business partner dina ne, a Lagos yake zaune,  shine ma wanda mukayi deal dashi shekaranjiya akan wasu kaya daza'a shigo mai dashi gobe, yace yanaso ni nafara ganin kayan tukunnan kafin sauran associate dinshi sugani", wani dadi ya ziyarci zuciyan *ASHRAF* ya zuciyarshi yace "shikenan, faduwa tazo daidai da zama", kallon Abba yayi yace "toh Abba ai kaga kaima er kace kenan, baba'a samu matsala inka mishi maganan ba" yace "hakane, ai dama yagaya min akwai er shi da take karatu a ABU  wanda shikaran nan tashi, kenan itace?", "kwarai kuwa Abba itace", "toh ai shikenan, in anjima zan kirashi muyi magana", "yauwa Abba nagode", "ba komai jeka". Fita yayi cike da murna, yana zuwa dakinshi ya fada kan gado yama manta da ciwonshi yace "yesss!!, dis will b my chance to win her heart, *DAMSEL* just hang over der a little long, cus i am urs nd u ar mine".(Allah yasa)

     Abba ya kira mahaifin *ZYNAH* sukayi gaisuwansu irin ta manyan mutane sannan sukayi zancesu akan kayan da za'a shigo musu dashi gobe,  bayan sun gama tautaunawa Abba yace "ammmm, Alhaji Muhammad in bazaka damuba akwai wata maganar da nakesoyi dakai" Daddy ya gyara zama kaman yana gabanshi sannan yace "bismillah in jinka dan fillo", "dama ba wani abu bane illa magana ce akan er ka datake karatu a nan", dammmmm Daddy yaji gabanshi ya fadi, a zuciyar shi yace "Mamana, kodai wani abu yasameta ne", ganin ba amsa yasa yace "ÿata kuma, lfy dai ko?" Abba daya fuskanci kaman hankalinshi ya tashi seya ce "kwantar da hankalinka, ba wani abu yasameta illa dan gurina yazomin da wata zance kan cewar akwai wani yaro dake barazarnar sonta yakeyi a yayinda kowa yama wannan yaron shaidan banza nacewar ba yaron kirki bane dan.....", nan duk ya kwashe lbrn komai da yaji daga bakin *ASHRAF* da Sameer dan ya tuntubi Sameer da maganan KB kuma Sameer ya tabbatar da duka abunda *ASHRAF* ya fada mishi hakanne. Sosai hankalin daddy ya tashi yace "nikam ba abunda ta koro min kuma kullum muna waya sannan ko maihaifiyarta bata fadawa ba", Abba yace "ai bazata iya fada muku ba saboda zataga kaman zaku hanata karatun", Daddy yace "hakane, toh amma yanzu me abunyi tunkan lokacin ya kure", Abba yayi gyaran murya sannan yace "abunyi daya ne, shine tabar zaman hostel, dan komai ze iya faruwa in tana wurin", "toh dan fillo in tabar hostel inzata", "Zato gidana, nida iyalina zamu karbeta hannu bibbiyu mubata kulawan da yakamace ta, batare da takurawa ba, kaga tahaka zatafi samun nutsuwa, kuma muma zamu samuta ido, sannan ku kuma hankalinku zefi kwanciya, kaga advantage uku kenan", seda Abba ya numfasa sannan yace "hakana, amma kana ganin ba takura", Abba yace "haba haba, kar muyi haka dakai mana, wani irin tukara, karka manta inada yara mata a gaba kuma ina ganin zasuyi sa'anni, sannan itama ai ÿata ce", Daddy yace "hakane, shikenan ba matsala, zamu tautauna da maihaifiyarta akai S3 musa rannan da zata koma", sosai Abba yaji dadi yace "badamuwa, Allah ya kara karfin zumunci" Daddy ya amsa da "ameen", tareda mai godiya sannan sukayi sallama suka kashe wayan.

     Daddy na ajiye wayan ya kira Momcy dake kitchen tana kokarin hada dinner yace tazo ta sameshi a daki, ba bata lokaci ta tafi amsa kiran mijinta. Yana zaune a kan gado ya rafka uban tagumi Momcy ta shigo dakin bakinta dauke da sallama, ganin halin da mijinta ke ciki yasa tayi saurin karasa wurinshi tareda zama kusa dashi tace "Daddyn su lfy, meya faru?", ta jero mishi tagwayen tambaya alokaci daya, kallonta yayi ya sauke ajiyan zuciya tareda cewa "Mamana na cikin matsala", arude ta tambaye shi "wani matsala Daddyn su?", dan tasan tabbas *ZYNAH* yake nufi, ba bata lokaci ya zayyane mata komai ba abunda ya boye mata harda zancen koma wanta gidansu *ASHRAF* duk ya fada mata, cikin kuka tasoma cewa "kaga abunda nake gudan mata, duk laifin ka, a lokacin da baka biye mata ai da bamu shiga damuwa irin wannan ba, danace banaso tayi nisa da sunan karatu ai kai ka daure mata gindi kafe ba matsala, toh gashi tun batayi nisa ba anfara shiga matsalan da nake gudar mana" kuka take sosai Daddy kuma ba bakin magana dan duk abunda tafada gaskiya ne, da be amince da tafiyan ta wani garin ba da bazata ba, amma saboda beson bacin ran *ZYNAH* ne yasa tana gaya mishi ga makarantar da tazaba be musa mata ba, janyo Momcy yayi a jikinshi a shiga lallshinta tareda amincewa lefin nashine  sannan daga baya tayi shiru tana kallon shi sannan tace "inaso weekend dinnan muje mu dubata, she needs us ryt nw", be musa mata ba yace ya amince sannan ta tashi tace zata dora girki bari inje induba, Islam dake labe bakin kofa tun shigewar Momcy tafi sauri ta sauka kasa ta zauna kaman dama can anan take, wuce Momcy tazo tayi ta tafi kitchen, tsale Islam tayi ta tashi ta wuce dakin cike da jin tace "wow, i would lyk to sit nd watch dis interesting movie dats abt to begin, i can't believe dat today bcoz of *ZYNAH* d most talented nd brilliant girl, who is loved by everyone is nw d cause of my parents fight, wow it will b interesting i guess".

         *FLASHBACK*

     Tun sanda *ZYNAH* ta tafi school, Islam canza halayenta ganin dukda *ZYNAH* bata nan amma basuda magana da wuce nata wanda wannan yasa takejin tsantsar tsanar yarta kaman ba ciki daya sufa fitoba, gashi yanzu ta zukance daga school har Islamiyya bata mayarda hankali, insukayi test dakyar takecin 8 acikin 20, Daddy, Momcy, Uncle Yusuf sunyi magana, sunyi nasiha harsun gaji,sun samata ido dan duk sun fita harkanta, bame sake mata fuska a gidan, inda itako ko a kwalar rigarta dan ita yanzu batada buri daya wuce taga ta ďana wa *ZYNAH* wutan da bazata iya kashewa ba.  (kunji wata sabowa)

     *BACK TO STORY LINE*

     Su *ZYNAH* sun kusa gama exam dan ran Friday zasu rubuta last paper dinsu, Daddy da Momcy sun kirata akan lbrn da sukaji kuma sun nuna mata basuji dadin rashin gaya musu da batayi ba, hakuri ta basu tareda musu alkawarin bazata sake boye musu wani abu ba, sun ce mata weekend zasuzo amma basu gayamata cewar zata koma gidansu *ASHRAF* ba, Abba ya fadawa *ASHRAF* yanda sukayi da Daddy, dadi wurin *ASHRAF* ba magana, sekace wanda akace mai an bashi kujerar maka.

     _Mzz Daddy💋✍🏻✍🏻_

ZYNAHWhere stories live. Discover now