Chapter 33

1K 68 0
                                    

🌻🌻🌻🌻🌻🌻🌻🌻

             *ZYNAH*

(An Interesting Luv Story 2017)

By Aisha Muhammad (Mzz Daddy 💋)

*BAIWA WRITER'S ASSOCIATION*

QUOTE:-"Great personality will always make you more attractive than someone who only has a great face."😎😊

              3⃣3⃣

     Suna shiga gida suka shirya suka fito, Abba yace *ASHRAF* ya dauki mota ya kaisu hotel su kwaso kayansu daga nan ya kaisu airport, ai kuwa nan da nan yaje ya fito da mota kirar Honda accord dan a wurin shi alfarma aka mishi, dan ze raka sahibarsa airport, sunzo tafiya Juwairiya tasa kuka ita seta bisu, da kyar aka lallasheta tayi shiru sannan su Daddy sukayi sallama suka kama gabansu, tafiya sukeyi a hankankali wanda duk dagowa in *ZYNAH* zatayi seta hada ido da *ASHRAF* ta mirror, suna hada ido ze sakar mata murmushi itama ta mayar mai da martani, a haka har suka karasa hotel din. Duka wannan bidirin da akeyi Fahad beda masaniya akai dan wannan weekend din besamu zuwa gida ba.

Sunkai hotel din matan kawai ne suka shiga ciki inda *ASHRAF* da Daddy suka wuce masallaci dan yin  sallar la'asar sannan duk suka sauko da kayansu, jirgin karfe 6 na yamma zasubi saboda haka 5 sukeso ya musu a airport, ai kuwa Allah ya taimake su rannan Sunday ne saboda haka ba'ayi hold up sosai a Kaduna ba ranan, kafin 5:30 har sungama abunda zasuyi suna jira a fara kiran masu tafiya, *ASHRAF* yaki tafiya ya tsaya yana hira da *ZYNAH* harseda Daddy ya lura dashi yace yakamata ya dau hanya saboda kar dare ya mishi a hanya, se a lokacin ya musu sallama tareda fita ya shiga motanshi ya dau hanya cike da kewan *DAMSEL* dinshi. Suma ba dadewa jirgin su ya tashi, *ZYNAH* dukda ta fara kewan *ASHRAF* wannan be hanata jin dadin yau zatayi kwanan gidansu ba, zata kwana a dakin ta, tayi barcin yanda takeso,(gida gidane, duk wanda yabar gida gida ta barshi).

     *ASHRAF* na kaiwa gida yafadawa  mahaifinshi cewar ya kaisu, kuma yanajin yanzu jirginsu ya tashi, Abba yasa mishi albarka sannan ya koma dakinshi, ai yana shiga ya tarar da Sameer a kan gadon shi yace "kai kuma shikenan dakina beda privacy, kashigo duk sanda kaga dama ka fita duk sanda kaga dama", Sameer ya mike zaune yace "mallam daga dawowanka ko hutawa bakayi ba zaka fara harzuko min, ni zo ka zauna, da magana nazo shiyasa na jiraka har kadawo", *ASHRAF* zuwa yayi yaja kujeran dressing mirror dinshi ya zauna yana facing din Sameer yace ina jinka, kallonshi Sameer yayi yace "naji wai Abba da mahaifin *ZYNAH* frnds ne?", "wannan shine maganan da zaka min, amma bakada serious", mikewa *ASHRAF* yayi ze bar wurin Sameer yayi saurin rikemai hannu yace "tsaya mana, ni ba wannan ba, to b serious akwai maganan da zanma, nd i hope u will give me a helping hand", zama *ASHRAF* yayi tareda cewa "y nt, indai befi karfina ba am willing to help", "befi karfinka bama, kasan wani abu, i hav a crush on ur sister", "i already knw abt dat", "wat, hw did u knw", "ai ni na dade da sanin kanason Minal, dama jira nake naji zaka fito ka fada ko kuwa", sauke kai Sameer yayi sannan ya dago ya kalli *ASHRAF* yace "u ar mistaking, ni ba Minal nakeso ba", cike da mamaki *ASHRAF* yace "inba Minal kakeso ba toh wa", kai tsaye yace mishi "Basma", kallonshi *ASHRAF* keyi sannan daga bisani yace "all dis while u've been fond of Minal, in ka ganta kata janta da wasa kenan kuna hira kuna dariya, den y all of a sudden kace Basma kakeso?", "look *ASHRAF* i want u to understand something, ina wasa da dariya da Minal ne badan komai sedan u guys a close nd abunda yasa nima nayi close da ita kenan bawai dan inasonta ba, whereas Basma kuma tun tasowanta nake dauke da dakon sonta a zuciya na, kuma naga yanzu ne lokacin da ya kamata in fito in gayamata kar wani ya rigani, kagane", ajiyar zuciya *ASHRAF* ya sauke sannan yace "na fahimci ka dari bisa dari amma zaka iya fada min abunda yasa kakeson Basma?", "well,  ba komai yaja hankali na zuwa ga Basma ba illa, Basma akwai gayu, ga kyau, ga iyayi,ga tsiwa sannan uwa uba ka jan aji", dariya  *ASHRAF* yayi yace "Lalle kanada jan aiki dan in Basma ce zakaga iyayi da tsiwa, nidai nabaka go ahead kaje ka sameta kuyi magana", "a'a *ASHRAF* ba haka zamuyi da kai ba, inaso kai kafara zuwa mata da maganan sannan daga baya ni se inje", "a'a baza'ayi haka dani ba dan banson raini, kaje kamata magana wannan tsakaninku ne", yana gama fadan haka ya tashi yasoma cire kayan jikinshi dan ya watsa ruwa, shikuwa Sameer tunani ya shigayi na yanda ze tunkari Basma dan yaga alaman *ASHRAF* ba taimaka mishi zeyi ba.

ZYNAHDonde viven las historias. Descúbrelo ahora