Chapter 9

1.4K 82 0
                                    

🌻🌻🌻🌻🌻🌻🌻🌻

*ZYNAH*

(An Interesting Love Story 2017)

By Aisha Muhammad (Mzz Daddy 💋)

QUOTE:- "It's a very dangerous state. You are inclined to recklessness and kind of tune out the rest of your life and everything that's been important to you. It's actually not all that pleasurable. I don't know who the hell wants to get in a situation where you can't bear an hour without somebody's company."

_I dedicate dis page to *SAMRAH* I hrt u babe❤._

0⃣9⃣

*ASHRAF*
Tuki yake amma gaba daya hankalinshi na kan gurl dinda yagani a airport , tunda yake be taba ganin yarinyar da ta birgeshi wit lots of confidence ba sai wannan , wacce batada tsoro tunda ta iya daga kai ta kalli idon shi tafada abunda ke ranta ba tareda taji tsoro ko shaken wani abu ba. Da haka yaci gaba da tukinshi har suka kai gida cike ta tinanin ta , suna shiga gida tin daga compound Minal da Basma suka rugu a guje kaman ba en mata ba suka rungume Abbansu suna mishi sannu da zuwa, shima cikin murna ya amsa musu sannan suka shiga bangaren shi wanda yake ginin sama ne.

Suna shiga matanshi suka tarbeshi cike da fara'a, shima yayi farin cikin ganinsu. Nan Ummi tafara gaida shi "sanda zuwa Alhaji, ya hanya da gajiyan hanya" ya amsa da "Alhmdllh , amma gajiya na nan tukun har se na samu hutu" Ammi tace"sannu Alhaji, ai irin wannan tafiyan dole da gajiya" yace "gaskiya kam" Ummi tace "ba ka daiyi zaman jira a airport ba ko, dan beyi saurin tafiya ba","ko kadan shine ma ya jira ni" yana cikin magana sai ga *ASHRAF* ya shigo Ummi tace "kaci sa'a ka kai kan lokaci da nayi maganin ka yau" yana sosa keya yace " amin afuwa ranki ya dade ,tuba nake , next tym bazan makara ba" duk suka kwashe da dariya saboda yanda yayi maganan , shima dariyan yayi tareda zama kusa da Ammi, Abba yace "ina sauran yara na" Minal ta bashi amsa da cewar "Husna da Juwairiyya na makaranta , Hamma Fahad kuma wai golf stick dinshi ya karye, yaje shiyo sabo, Haydar kuma yaje bookshop ", "Allah ya dawo dasu duka lfy" duk suka amsa da Amin banda *ASHRAF* da bemasan me ake ciki ba. Basma ce tace " Abba my birthday is around d corner" yace " ok, any plans for d birthday" kafin tayi magana Ammi ta katse ta da cewar "yaran nan ku bari yayi wanka yaci abinci ya huta mana sai kuyi hira yanda kukeso inya tashi" Abba yace "a'a , bar min yarana sunyi miss din Abbansu ne kuma shima Abban yayi miss dinsu, saboda haka ku bari naji matsalan su" Ummi ta tace "inka biyewa yaran nan sai ku kai dare a nan wurin" yace yaji sannan ya juya wurin Basma yace "ina jinki wani plans kike dashi" tace "dama kawai ina so in hada small party ne, ni da frnds dina kawai","ok, bari zamuyi magana anjima, inna manta ki tuna min","toh Abba" kefa Minal "Abba zamuyi magana anjima, nt nw","toh shikenan".

Be gama rufe baki Hamma Fahad yayi sallama tareda Husna da Juwairiyya da yake ya biya islamiyyansu ya dauko su , suna ganinshi suka sake ihun murna tareda kaimai wani wawan hug amma banda Hamma Fahad ( as in babban yaya lol) shima rungume yaranshi yayi tareda da tambayansu ya makaranta, suka amsa da lfy, sai a lokacin yadago ya kalli Fahad yayinda su Husna ke zaune akan cinyarshi "Abba ka dawo lfy","Lfy lau Fahad","ya hanya da gajiyan hanya","Alhmdllh" sannan ya kalli *ASHRAF* yace "kai kuma lfy ka zauna kayi shiru kaman me daukan darasi" se a lokacin dukkan su suka ankara dashi dan harga Allah sun manta yana parlourn saboda yanda yayi shiru , kallon fuskan Hamma Fahad yayi, yayi murmushi sannan yace "lfy lau, me ka gani","naga kayi shiru ne , ko miskilancin ya motsa ne" yafada yana dariya, Ummi ta karba da cewar "ai kuwa, saidai miskilanci irin wannan shiru haka","ba wani miskilanci, kawai en maganan ne basa kusa,ko son?"cewar Ammi, shidai murmushi kawai yakeyi dan shi kadai yasan abunda yake ji tinda yabar airport ,ji yake inama ze kara ganin wannan *DAMSEL* din (sunan da zuciyarshi yasa mata) da yafi kowa farin ciki (ni kuwa nace sha kurumin ka indai *ZYNAH* ce zaku hadu) yana cikin tinani sukaji sallaman Haydar.

ZYNAHWhere stories live. Discover now