Chapter 17

1.1K 68 0
                                    

🌻🌻🌻🌻🌻🌻🌻🌻

             *ZYNAH*

(An Interesting Love Story 2017)

By Aisha Muhammad (Mzz Daddy 💋)

*BAIWA WRITERS ASSOCIATION*

QUOTE:- "You know it's love when all you want is that person to be happy, even if you're not part of their happiness."

     _I dedicate dis page to my 2nd bestee *Hauwa'u* Allah ya kaimu February musha biki.😜_

                1⃣7⃣

     Karfe biyar da en mintina jirginsu ya sauka, cikin lokaci kalilan suka gama abunda zasuyi suka fito, can suka hango su Daddy tsaye suna jiransu. Da saurinsu suka karasa wurin cike da murnar ganin juna. Duk ta dinga rungumar su tana jin dadi har ta kai kan Humaira, wani wawan hug ta kai mata tana fadin "my bestee of life i missed u soooo very much" itama Humaira tace "  i missed u more nd more swthrt" su Daddy duk dariya suke musu, sannan Uncle shima ya gaishe su suka amsa,se alokacin *ZYNAH* ta lura ba Islam a wurin se ta tambaya da "ina Islam,ya banganta ba" Momsie ta bata amsa da "She's sick, kanta na ciwo" ,"ehhya my Lil sis, muyi sauri muje gida inganta". Nan duk suka shiga mota suka yau titi zuwa gida cike da nishadi. Sun kai gida sukayi horn gate man ya bude musu gate suka shiga sukayi parking, suna  parking masu aikin gidan suka dinga kwasan gaisuwa suna musu sannu da zuwa suma suna amsawa cikin jin dadi da murnar dawowa gida.

     Islam tana dakinta zaune tana jin hayaniyar su amma ta saura ciki batare da tayi yunkurin fitowa ba, jin hayaniyar na yawa yasa ta taso taje gaban window din dakinta ta tsaya tareda daga curtains din tana lekensu, batasan sanda murmushi ya subuce mataba ganin er uwar ta da tayi tabbas tasan tayi kewar sista dinta kuma tanaso taje ta rungumeta taji dumin jikinta amma shaidanin ta yana hanata, haka tanaji tana gani ta kasa zuwa ta kuma ta zauna kan gado tareda rafka tagumi ta soma hawaye wanda ita kanta batasan dalilin hawayen ta ba. Batasan yawan lokacin da ta deba zauna ba se jin knocking tayi, muryan *ZYNAH* taji tana kiranta tana cewa "Lil sis open up am back", tashi tayi da sauri ta fada bathroom tayi sauri da wanke fuskarta ta goge taje gaban mirror ta shafa powder saboda kar a gane tayi kuka sannan ta bude kofan, tana ganin sista dinta batasan sanda takaimata hug ba tana fadin "sista i  miss u" ,"i miss u too, jikinki yayi zafi, ya kikeji yanzu" ,"don't worry i'm feeling beta" ,"sorry kinsha magani" ,"nasha, muje kasa inga Uncle". Nan suka sauko zuwa parlour taga Uncle zaune kan one sitter taje ta fada jikinshi tana mishi welcome back.

     Sun gama gaishe gaishen su aka basu wuri suje suyi wanka suci abinci dan su samu su huta,nan duk suka shiga dakunan su sukayi wanka sukayi sallah sannan suka fito zuwa dinning duk kowa ya hallara wurin *ZYNAH* kawai akejira bata dade ba itama ta fito ta zauna kusa da Daddy suka fara cin abinci cikin nutsuwa har suka gama suka koma parlour suka zauna aka bude sabodan shafin hira suka dinga bayarda da labarin arewa da kuma Granny harda kukan da ta bayar a kawo da yanda sukayi da kukan duk seda *ZYNAH* ta bada lbrn shi suka dinga dariya suna kyakyatawa, suna cikin haka wayan Uncle yayi ringing ya dauko "Hello sir good evening, am fyn sir, ok sir i will b on my way right now, ok sir" dif ya kashe wayar tareda sauke ajiyan zuciya, Daddy yace "lfy daiko?" yace "ba lfy, wai wasu criminals aka samu suna damun en Lekki da sauran estates dukda akwai securities, sannan kuma basa barin wani trace da za'a iya tracking dinsu dashi,kuma yanzu bannan da sukeyi yana yawa saboda haka yanzu an samo kwararrun criminologist guda biyar which am one of dem ,zamuje mu hadu da wasu professional police muje muga  abunda zamu iya yi" Momsie tace "Allah ya bayyanar dasu cikin sauki" duk suka amsa da "Ameen" sannan ya tashi ya shiga dakinshi yadau laptop dinshi da necessary things dinda dinda zaiyi amfani dasu ya fito ya musu sallama tareda shaida musu ba lalle ya dawo yau ba ze iya kaiwa gobe, suka mishi fatan alheri ya fita ya yashiga motarshi kirar _Toyota Camry 2016_ ya fita ya dau hanya.

     Yana fita Islam ma tace zataje daki tayi excusing kanta ta haura sama, *ZYNAH* da Humaira ma haka suma dakin suka wuce aka bar Momsie da Daddy sukaci gabada hiransu, Su *ZYNAH* na shiga daki Humaira tace "yes, yanzu zaki samu daman bani lbr" *ZYNAH* ta kalle ta tace wani lbr zanbaki" ,"na wannan guy dinnan" ,"guy, wani guy kike fada" ,"d one u told me abt, d one at d airport" tafada tana daga mata gira "oh, u mean dat arrogant jerk" ,"hey stop calling him jerk kikasan inda zaku kara haduwa" ,"ai banama son mukara haduwa, he's so full of himself" ,"hummm don't tell me u don't luv him cos u told me he's handsome" teddy dinta ta dauko ta wurga mata tana cewa "don't say dat cos it's totally d oppsite bcos i hate him" dariya tayi tace "swthrt u ar funny wat if u luv him bt u didn't notice, wat if it was luv at first sight" dariya sukayi gaba dayansu sannan tace ma Humaira "u knw wat, i think it's hate at first sight" tana magana tana dariya Humaira na tayata.  Humaira bata tafi gida ba se past 8 tace driver ya kaita saboda bazata iya tukun dare ba.

**********
              *Zaria*
     Dukka familyn Alh Sagiru fillo ne zaune a parlourn Abba sun hira kowa na karanto matsalar shi Abba na jinsu Fahad yace "Abba anyi posting dinki " Abba yace "toh alhmdllh, wani gari suka tura ka" yace" ai ni nayi lucky Kaduna suka tura ni acan zanyi youth service dina" Ummi tace "ai shikenan naka yazo da sauki kaga zaka iya ka dinga lekomu akai akai" Ammi tace "hakane se a maida hankali" ya sunkuyar da kai yana susa keya yace "In Sha Allahu, ammm Abba dama akwai abunda nakeso ne" ,"Ina jinka me kakeso" seda ya kalli Ammi sannan yace "Mota nakeso na canza" kafin Abba yayi magana Ammi ta rigashi tace "baza'a canza ba, yaushe yaushe aka baka wannan din da zakace a canza maka, kai har wani son mota kake sosai ba kafi son bike ba" Ummi ta katse da "ki kyale shi kila ya samu canjin ra'ayi ne" shiko cikin zuciyar shi cewa  yake "dis woman will neva stop getting on my nerves" (kujifa wai da mahaifiyar shi yake), amma a fili cewa yayi "shikenan ba komai duk hukuncin da kuka yanke daidai ne" Abba yace "nima na goyi bayan Ammin ku ka bari in ka gama service dinka nama alkawarin latest car in town" murmushi yayi yace "nagode Abba".

     Sannan Abba ya juya wurin *ASHRAF* da yayi shiru yana jinsu yace "kaifa me kakeso?" yace "Abba ba komai illa kudin account dina da yayi kasa gashi next week zamu koma sch" Abba yace "shikenan ai kai nasan bakada matsala" yayi murmushi sannan Abba ya juya wurin Minal yace "Chief tailor" tayi murmushi yace "me kikeso" tace "Abba  keken dinki nakeso ka siyamin na ajiye a gida" yace "an gama,  Basma kefa","Abba waya zaka canza min da makeup kit" Haydar yayi sauri yace "ke kenan make up kullum make up se cancer of d skin ya kamaki" tayi sauri tace "over my dead body, Abba kana jinshi koh" yace " rabu dashi, amma ki rage make up, meyasamu wayanki kikeso ki canza" ,"Abba yana seizing ne baya functioning sosai" ,"Toh naji, kaifa Haydar" ,"Abba kasan ni banda matsala, kayan wardrobe dinna gaba daya kawai za'a canza min" dariya sukayi gaba dayansu Basma tace "kunga me gaba daya ai da se kace kayan dakin gaba daya kakeso a canza ma" yace "Ina ruwanki, ok jokes apart akwai wani shirt dinda nagani da wani takalmi boot a jumia sunakeso" Abba yace "naji, Husna kefa" ,"Abba ni school bag nakeso" ,"shi kadai" ,"eh Abba" ,"toh shikenan, Auta Juwairiyya kefa" ,"Abba nima school bag da barbie doll" ,"An gama, dukkan ku naji abinda kuke bukata ku sauraren zuwa jibi In sha Allah" Ummi tace "Allah ya kara karfin jiki ya kara budi" duk suka amsa da "Ameen". (wannan yana daya daga cikin hakkin yara a wurin iyayensu, akwai wasu yaran suna bukatan abu amma saboda suna jin nauyin iyayensu se su kasa tambaya, shiyasa yake da kyau iyaye sun dinga kula in su basu tambaya ba iyaye sai su tambaya, da haka zaka san abunda ke damun danka ko yake  bukata Allah yasa mudace Ameen).

     _Nasan page dinnan is short kumin uziri hannuna na ciwo ne typing is not easy😥_

          _Mzz Daddy 💋✍🏻✍🏻_

ZYNAHWhere stories live. Discover now