Chapter 48

1K 65 0
                                    

🌻🌻🌻🌻🌻🌻🌻🌻

               *ZYNAH*

(An Interesting Luv Story 2017)

By Aisha Muhammad (Mzz Daddy 💋)

*BAIWA WRITER'S ASSOCIATION*

QUOTE:-"The greatest thing in life is finding someone who knows all your mistakes and weaknesses and still loves you and thinks your the best thing in there life!"

              4⃣8⃣

*BAYAN WATA BIYU*

     Biki ya matso kowa kanshi yayi zafi ana shirye shiryen biki, iyayen Uncle da Momsie sunzo daga Ethiopia bikin dansu wanda ya rikide ya zama ba haushen Nigeria karfi da yaji, Momsie da Ammi da Minal ne sukaje suka hado lefe nagani na fada dan kusan duka kayan ma Minal ce tazaba kayanta, Uncle yace gado da kwaba kawai iyayenta zasuyi dan a Lagos iyayen amarya basa kayan kujeru ango keyi amma Abba yace sam be yarda ba, yanda akewa kowace y'a mace itama haka za'a mata, Barrister Hafsa (babbar yarsu Minal a mata),  tazo da danta da ita za'a fara duka events din, inda Doc Jamal (Babban yayansu kwata kwata), yace se saura three days daurin aure zezo, amma matarshi tazo da yaran ta biyu. Haidar ma yazo dan yace baza'ayi bashi ba.  En uwan Abba, Ummi da Ammi duk sunzo daga Maidugiri, inda wata kanwar Ummi ce tayiwa Minal gyara ciki da waje duk da ba'a fara mata gyaran da wuriba amma tayi kyau, jikinta kaman ka taba jini ya fito abinka da fara wacce tasha gyaran en Maiduguri, sosai tayi kyau abunta, gashi duk abunda ake bata ba musu take karba tasha, dan tace duk wannan playing girls din da Uncle keyi seya dai nashi, duk da ya dade da bari dan tun sanda suka sasanta da Minal ya sallame duka en matanshi, amma ita Minal tana gani kaman har yanzu akwai en matan.

     Event biyar suka shirya, saboda haka tun Wednesday zasu fara bikin su sugama ran Sunday, ranan Wednesday bridal shower sukayi inda amarya tasa white gown, sosai tayi kyau kaman ka sace ta ka gudu, ga fara'a se murmushi takeyi, ango dai a hotuna yaga amaryar tashi inda yakeji ina ma ace tana kusa dashi, washegari Thursday sukayi Fulani day inda amarya da kawayenta sukayi shigan Fulani, sosai tayi kyau dama kuma fulanin ce, zanso kuga *ZYNAH* yanda kayan fulanin ta suka tsaya mata das a jiki kaman dama can fulanin ce, ranan Friday kuma kamu sukayi inda amarya taci kwalliyan ta cikin shadda gizna lemon wanda yaji bead work a jiki aka mata cool makeup, sosai tayi kyau abunta inda kenan amarya kuma sukayi kwaliyan su cikin atampa super holland ja me ratsin cream a jiki, sosai atampa yama *ZYNAH* kyau dama gata ba gwanan sa native ba, su Ammi da Ummi da Momsie yayi sukayi cikin wani swiss lace cream suka hada da head brown suma sunyi kyau abunsu, anyi kamu anyi shagali anci ansha sannan aka tashi kowa na yaba yanda ake kashe kudi a kamun akayi komai a wadace, ran Saturday kuma biki sukayi jigi jigi na azo a gani inda Minal tayi shiga cikin wani material lace peach da head gold sosai tayi kyau abun ba'a magana, inda kannen amarya sukayi shiga cikin less lemon da pink head suma sunyi kyau, biki yayi biki, inda akayi barin naira, a hannun uncle kuwa naira tayi kuka, shima material lace din da amarya tasa shiyasa, anyi biki lfy an watse lfy inda duk wanda yazo baya tafiya hannu rabbana atina seya tafi da memo ko jaka da dai sauransu wanda hoton amarya da ango ke kai.

     Rana bata karya sedai in ba'asa ba, yau Allah ya kawomu ranan da dubunan jama'a daga kasashe daban daban suka shaida daurin aure YUSUF USMAN da MINAL SAGIRU FILLO akan sadaki naira dubu dari lakadan ba ajalan ba wanda tarone da ya hada manyan mutanen kasa dan ko shugaban kasa be yarda yayi missing din auren ba, ana daura aure Uncle wani hamdala yayi tareda sujjada na godewa Allah daya bashi Minal a matsayin matanshi ta sunna, ita kuwa Minal tana gida cikin kawayenta da kannenta da kanwar mahaifiyarta data gyara ta taji gabanta ya fadi, dafe kirji tayi suka kalle ta Hajara kanwar mahaifiyarta tace "ke lfy", "jinayi gabana ya tsinke ya fadi", ai kuwa nan da nan tafara guda suma kawayen suka tayata, Basma kuma dan iskanci gabanta tazo ta tsaya tana mata wakan "tazama tazama dauko riga, tazama tazama dauko wando, tazama tazama dauko hula, tazama tazama dauko buta.......", haka ta dinga  mata tsiya itakuwa Minal mezatayi banda kuka, kuka takeyi na hakika tana rufe fuskanta da mayafin, kallonta suka tsaya yi suna mamakin meyasata kuka, Ammi ce tashigo tace tafito ga angwaye nan sunzo,  seda suka gyara mata fuska sannan suka fito da ita fuskanta lullube da mayafi, tsakar gida sukaje inda su uncle ke jiran amarya aka fara daukan hotunan, tunda suka fito *ASHRAF* idonshi ke kan *ZYNAH* wacce kanta ke kasa saboda maza da sukayi yawa a wurin,  sanye take da shadda pink an mishi aiki da purple, hotuna suka dinga dauka inda daga karshe aka dauki Uncle Yusuf da Minal tareda *ASHRAF* da *ZYNAH* juyawa tayi zata koma ciki *ASHRAF* ya riko ta yace "ban yarda kishiga motan wani ba, komin dare kijirani ni zan kaiki dinner din", murmushi tayi tace "zan jira ka", sannan ya barta ta shiga ciki.

     Karfe biyu aka fara walima inda aka kira malama Zainab tazo tayi wa'azi me ratsa jiki wanda kalau jikin amarya da duk wani wanda yake gurin yayi sanyi, se karfe hudu aka tashi daga waliman sannan aka fara shirye shiryen zuwa dinner inda kawayen amarya suka samo me makeup dinsu daban haka su Basma ma inda da kyar *ZYNAH* ta bari aka mata, amarya tayi kyau cikin shiganta na material silver da head komai silver tasa, inda kannen amarya sukasa material lace blue da red head sosai *ZYNAH* tayi kyau kace itace amaryan, karfe takwas da en mintina aka fara zuwa daukan mutane zuwa hall din da za'ayi dinner din inda *ASHRAF* shima yana cikin masu daukan, iyaye duk an tafi saura en mata inda suma haka aka dinga kwasan su, duk an watse saura su Basma da Humaira da *ZYNAH*, Sameer ne yazo daukansu amma *ZYNAH* taki shiga tace musu suje zata biyo bayansu, dama sunsan da zuwan *ASHRAF* saboda haka sukayi tafiyansu, basu dade da tafiya *ASHRAF* yazo daukan ta, hakuri yabata na dadewan da yayi sannan ya bude mata motan ta shiga, koda ya  shiga kin tada motan yayi ya zauna yayi relax yana kallonta, "B.FRND kana kallona lokaci ba wucewa", sauke ajiyar zuciya yayi yace "G.FRND kinyi kyau dayawa, hankali ba be kwanta da zuwanki wurin nan ba", murmushi tayi tace "Hmmm wani na tsoron a mishi snatching budurwar shi", kala bece mata ba sema gyara zama da yayi ya jingina jikin kujeran ya zuba mata na mujiya, ganin kallon bame karewa bane yasa tace " Mine don't worry, ni nakace kaima ka sani, in kuma kanaso zan iya zuwa in wanke makeup din", "no need, barshi, i trust u", tada motan yayi suka bar gidan, tafiyan 15min ya kaisu hall din inda ko amarya da ango basu ma shiga ba tukun, kallon *ASHRAF* tayi tace am off", "take care", "i will", sannan ta fita, kasa fitowa yayi saboda gabadaya ji yayi hankalinshi be kwanta da zuwanta wurin nan ba.


     Ba bata lokaci aka fara gudanar da taro, inda *ZYNAH* duk inda tayi idon *ASHRAF* na kanta, an bada brief history din amarya da ango sannan aka cigaba da taro inda komai a nutse akayinshi, amarya da ango sun fito fili dan taka rawa aka shiga musu liki, amma banda *ASHRAF* dan beson ya tashi daga inda yake saboda kar *ZYNAH* ta bace mishi, juyawan da zeyi ne ya hango wani kaman KB a wurin window, kallon direction dinda meshi ke kallo ya kalla, nan yaga ba kowa yake kallo ba inba *ZYNAH* ba, sosai hankalinshi ya tashi ganin KB a wurin, toh ya akayi yasan akwai dinner a nan kuma *ZYNAH* na nan, abunda ya tambaye kanshi kenan, ganin ba amsa yasa ya tashi ya fita amma beganshi ba bega alamanshi ba, ba inda be duba ba amma be ganshi ba, ganin hankalinshi be kwanta bane yasa ya koma hall din wurin *ZYNAH* ya ruko hannunta, ba yanda batayi ba dan yasake amma  yaki, duk inda zashi yana rike da ita, de damu da masu kallonsu ba, a haka har aka gama dinner yana rike da hannunta kaman yakama prisoner. Suna komawa gida tace "Mine meyasa ka rikeni hakanan a cikin jama'a kilama su Momsie sun ganmu", kallonta yayi yace "KB na gani a wurin, kuma ke yake hunting, ai nace miki hankalina be kwanta da zuwanki wurin nan ba", "toh amma ai ba abunda KB ze iya mun tunda cikin jama'a nake", "hakane, amma ni hankalina be kwanta ba, KB is still after u", "kwantar da hankalinka, ba abunda ze iya mun", sauke ajiyar zuciya yayi yace "Allah ya shige mana gaba, jeki kwanta", murmushi tayi tace "Ameen", sannan ta bude kofan zata fita ya riko ta yace "karki kashe wayan ki, kuma karki kwana ke kadai", murmushi tayi tace "i won't", sannan ta fita shikuma ya bita da kallo harta shige sannan ya dora kanshi kan steering din motan shi yana tunanin yanda zeyi da KB dan ya tabbata KB yagani, in kuwa shine yasan ba barin *ZYNAH* zeyi ba kuma she's in grt risk.

     _Nt much, a little busy, manage dis, much luv😍_

      _Mzz Daddy 💋✍🏻✍🏻_

ZYNAHWhere stories live. Discover now