Chapter 27

977 64 2
                                    

🌻🌻🌻🌻🌻🌻🌻🌻

              *ZYNAH*

(An interesting luv story  2017)

By Aisha Muhammad (Mzz daddy 💋)

*BAIWA WRITRE'S ASSOCIATION*

QUOTE:- "A child on a farm sees a plane fly overhead & dreams of flyin, but pilot on d plane sees d farm house & dreams of returning home.Dats life!"

     _I dedicate dis page all members of *ZYNAH FAN'S CLUB* wit much luv.❤_

                2⃣7⃣

     Sun kai asibitin direct ER (emergency room) akayi dashi, doctor uku ne akan *ASHRAF* dan ba karamin rauni suka mishi ba. Ummi, Ammi, Minal da Basma ne zaune, kowa hankalinshi a tashe, bame cewa wani kala, kowa da tunanin da yake. Awa daya da rabi suka dauka sega doctors sun fito, gaba dayansu sukaje wurin babban likitan tareda tambaye halinda *ASHRAF* ke ciki "ku kwantar da hankalinku, ba wani abunda zaku daga hankalinku akai bane, rauni yaji sakamakon dukan da aka mishi, wanda anfi kaiwa cikinshi duka, wanda sanadiyar hakan Cervical rib dinshi ya goce", Ammi tayi karfin halin cewa "me kuma cervical rib doctor" ,"ina nufin kashin gefen cikinshi,wato hakarkarin shi ya goce", gabadayansu suka hada baki wurin cewa "Innallihi wa inna ilaihi raji'un" Ummi tace "doctor hakarkari fa kace" yace "eh, amma karku damu mun riga mun dashi mazaunin shi, yanzu haka mun mishi alluran barci, ze samu barci kaman na awa biyu, seya tashi zamu samu mu gane ko kashin ya zauna sosai", Ammi tace "shikenan doctor mun gode, zamu iya ganin shi?" ,"eh, amma in kun shiga banda surutu".

     Dakin yake suka shiga, private room ne, saboda haka shikadai ne aciki, halinda yake ciki abun tausayi ne dan gabadaya ya canza kaman ba handsome *ASHRAF* dinnan me ji da kanshi ba, wuni daya amma duk ya rame ya zabge kaman bashi ba, ga fuskanshi ya kara fari fat dashi, ga labbanshi duk sunyi fari sun bushe,(Allah sarki *ASHARF*). Ganinshi da su Ummi sukayi seda suka zubda kwalla saboda tausaya masa banda Minal da ita kuka takeyi sosai kaman danshi aka aiko ta ganin dan uwanta wanda tafi ji dashi akan kowa kwance a gadon asibiti ga drip ana kara mishi. Can bayan duk sunyi shiru dakin yayi tsit Ummi takatse shirun da cewa "Allah sarki babana dukda nasan kanada sauri zuciya amma baka fada, tun tasowar ka ban taba ji ko gani ba wai gaka kana fada, amma yau kaine ka dawo haka saboda fada" seta fashe da kuka, Minal ma tasa wani kukan itama Basma seta tayasu bame lallashin wani dan Ammi bata dakin tafita ta kira Abba tagaya mishi halinda ake ciki. Shigowanta taga dakin ya hargitse da kuka, nan tashiga lallashin su tareda tausaya Ummi dan tasan yanda Ummi keson *ASHRAF*, magana goma in zatayi seta sako shi sau tara, kuma ko ba komai tasan duk wanda yasamu *ASHRAF* a matsayin ďa to kuwa yayi dace, dan haka Ummi ba karamin dace tayi ba kaman ita da danta Fahad banda shaye shaye ba abunda  ya Iya, nan dai ta kawar da wannan tunanin taci gaba da lallashin su harta samu sukayi shiru.

     Zaune take a kan gado tana tunanin karfin hali irin KB, ita tsoronshi ma takeji ta rasa dalili, ko kadan batason ganin shi, se yanzu tafara regretting rashin jin maganar maihaifiyarta da tayi, yanzu take dana sanin kin zama a Lagos tayi karatun ta a wurin, gashi yanzu tazo garin ba dagin iya bare na uba, ga ta kwance a gadon asibiti amma ba familyn ta ko daya kusa da ita seka mara gata alhalin ba haka bane, ga wannan KB din yazo yana takura mata (ai dama duk wanda baya daukan shawaran mahaifa toh yana tareda wahala). Jin karar bude kofa yasa ta dago kai dan ganin ko waye, su Shaheeda ne suka shigo, Ashanty ta gaya mata ta kira Uncle  Yusuf yace gobe zezo, "meyasa kika kirashi? ze iya gayawa su momcy" ,"yace baze fada musu ba, so kwantar da hankalinki", ajiyar zuciya ta sauke sannan tace "kunga KB?" Shaheeda tace "ai muna nan yazo, yace mufita ze miki magana", nan ta kallesu tace "tsoronshi nakeyi, he doesn't seem normal, infact he's nt normal, dinshi kadai ma abun tsoro ne", Ashanty tace "karki damu, ba abunda ze faru In Sha Allah, dan akuya ne shi, shegen son mata ne dashi, amma indan kikayi taka tsantsan dashi ba abunda ze miki", "gaskiya bana ganin zan iya chigaba da zaman hostel, dan in ina wurin komai ze iya faruwa, yanzu i need protection, dan naga alaman he's dangerous"  Shaheeda tayi saurin cewa "in kika bar hostel  ina zaki, ni a wurin Uncle dina nake, i don't think he will take u in" murmushi *ZYNAH* tayi dan ta gane inda Shaheeda ta nufa sannan tace "don't worry, am nt going to move in wit u", Ashanty tace "toh ina zaki" ,"I think i will hav to rent an apartment" gabadayansu suka hada baki wurin cewa "wat", Ashanty tace "dat will even b more dangerous dan am sure he will keep following u, nd in yagane u ar living in an apartment kuma kedai, he will definitely find his way", kallonsu tayi tace "toh ya zanyi yanzu", Shaheeda tace "d bst thing yanzu shine kiyi hakuri ki cigaba da zaman hostel tunda saura 3weeks semester  ya kare, in kin koma gida hutu se kuyi discussing issue din tare da parents dinki", Ashanty tace "abunda ya dace kenan". Girgiza kai tayi tace "no, dat won't work, in iyayena suka gane a guy is after me dey can stop me frm coming back her" nan duk sukayi shiru dan basusan me zasuce ba kuma, ganin haka yasa tayi murmushi tareda ce musu "don't worry i will just keep avoiding him,were is my phone" se alokacin Ashanty tace "na manta Uncle dinki wai ki kira mom dinki cos she's worried" *ZYNAH* tace "dama ita zan kira" nan ta kira gida suka gaggaisa tareda musu karyan tayi busy ne shiyasa bata kira ba, sukayi sallama take kira Humaira tana gaya mata abunda ya faru na zuwan *ASHRAF* da kuma zuwan KB.

     Abba najin kiran Ammi rabar duka abunda yakeyi yazo asibitin, ganin halinda *ASHRAF* ba karamin daga mishi hankali yayi  ba, toh wa ze mai haka? Abunda ya dinga tambayan kanshi kenan, ganin ba amsa yasa ya bar tunanin, ya zauna suna jiran farfadowan shi. Yanayin da yaga Ummi ciki yasa ta bashi tausayi sosai dan kuwa ta taba rasa danta wanda shima kisan wulakanci aka mai sanda suke Maiduguri, wannan dalilin kadai ya isa yasa hankalinta ya tashi. Nan dai dakin ya dau shiru bame magana se karan fanka dake juyawa. Wayan Minal ne yafara ringing, ganin numbern Sameer yasa ta fita dan amsa wayan, "Hello Yaya Sameer" ,"na, am Minal ya kk?, lfy naji muryanki a dashe", seta fashe da kuka, in hankalinshi yayi dubu ya tashi jin kukan Minal a waya, cikin tashin hankali yace "Minal lfy?", "Yaya *ASHRAF* ne ba lfy" ,"subhanallahi me yasame, dan inata kiran wayanshi ba'a dauka" ,"ganinshi mukayi a motanshi.......... nan ta koro mishi duka abunda ya faru wanda ta sani", yace "Allah ya bashi lfy,  ina hanya ne yanzu zan shigo Zaria, dana karaso zan shigo asibitin" nan suka kashe wayan, Sameer da ajiye wayanshi yace "KB, ba wanda zema *ASHRAF* wannan aika aikan se KB, amma bari zanyi magananshi"(nidai Sameer dama ka rufawa kanka asiri, *ASHRAF* ma bega draw ba bare kai).

     Sameer basamu shigowa Zaria da wuri se bayan isha wanda straight hospital din ya nufa, Minal ya kira ta fada mishi dakinda suke, direct dakin ya nufa gayasu Abba zaune kowa da abunda yake tunani, ya gaishe su tareda tambayan su tareda mai halinda suka amsa da jiki sauki, nan ya juya wurin *ASHRAF* wanda har yanzu be tashiba, kallinshi yakeyi besan yana hawaye seda yaji zuban ruwa akan kumatunshi dan halinda yaga *ASHRAF* ciki ya girgiza shi, tabbas ko waye yama *ASHRAF* wannan aika aikan beda imani, goge hawayenshi yayi yasamu wuri gefen gadon ya zauna, Abba ya kalleshi yace "Sameer, ba kada masaniya akan abunda yasamu abokinka? ", "Wlh Abba banda masaniya, ni yau namaje Kano dawowa na kenan" ,"kuma bashida abokin fada" har zece mai akwai KB amma kuma seya fasa yace "babu", Abba yace "shikenan" tareda kallon agogonshi yace "Minal ga iyayenku kuje gida dare yayi, gobe da safe seka dawo" basawa mahaifinsu musu saboda haka duk suka tashi sukama Abba da Sameer seda safe sannan suka wuce dakin ya saura daga Abba se Sameer.

     Karfe goma *ASHRAF* ya farfado, kadan kadan yake bude ido har ya budesu gabadaya, yana gama budewa hawaye suka biyo baya, kallon dakin da yake ne yasa ya gane a hospital yake, nan take ya tuno duka abunda ya faru tundaga lokacin da GIANT yayi kidnapping dinshi har zuwa dukan da KB ya mishi. Jin muryan mutane sama sama yasa ya kalli direction din wurin, Abba da Sameer ya ganin zaune kan couch, murya chan kasa kasa yace "Abba", Abba jin kaman ana kiranshi yasa ya dago kai ganin idon *ASHRAF* akanshi yasa ya taso da sauri tareda jan kujeran kusa da gadon yace " *ASHRAF*" ,"Abba ruwa" , Sameer dake tsaye kusa da Abba yayi sauri ya bashi ruwa tareda taimaka mishi yasha ruwan, sannan ya koma ya kwanta, Abba ya "Sannu, ya kakejin jikin" yace "Abba jiri nakeji, kuma gefen cikina namin ciwo", Sameer yace "Sannu bari na kira doctor", ya fita ba dadewa suka dawo tareda doctor din yadan dudduba shi sannan yacewa Abba "Alhaji yanzu dai he's stable, amma zuwa gobe da safe zamuyi scanning cikin, muga ainihin abunda abunda ke damun shi" ,"ok doctor, ba matsala, Allah ya kaimu goben" doctor yace "ameen, yanzu a samo mai wani abu yaci kafin inmai alluran da zanmai. Nan Sameer ya hada mishi tea, sannan yace yana zuwa, ya fita dan siyo fruit. *ASHRAF* ne ya kalli mahaifinshi yace "Abba, akwai abunda nakeso in fada maka" ,"Abba yayi saurin katse shi yace "bakada lfy yanzu, ka bari gobe in kaji sauki sosai se muyi maganan" ,"shikenan Abba duk yadda kace", Sameer ne yashigo rike da leda wanda kayan fruits ne aciki yaje ya ajiye kan table, yace "Abba naga dare yayi, kaje gida, ni se na kwana a nan", Abba be musa ba dan yana bukatar hutu yace "shikenan Sameer, Allah ya ma albarka", ya amsa da ameen sannan Abba yamusu sallama ya wuce. Zama Sameer yayi akan kujeran da Abba ya tashi daga kai sannan yace "wannan aikin KB ne koh?", kai kadai *ASHRAF* ya daga mishi, Sameer yace "dis guy is nw getting on my nerves nd am going to deal wit him" shidai *AHSRAF* shiru kawai yayi dan yanda yakejin jiki ba abunda ze iyayi. Beci kayan fruits din sosai ba Sameer ya kira doctor aka zo aka mishi allura ba jimawa barci ya daukeshi.
  (Se muce asuba take gari).

      _Mzz Daddy 💋✍🏻✍🏻_

ZYNAHWhere stories live. Discover now