Chapter 29

874 60 0
                                    

🌻🌻🌻🌻🌻🌻🌻🌻

             *ZYNAH*

(An interesting luv story 2017)

By Aisha Muhammad (Mzz Daddy 💋)

*BAIWA WRITER'S ASSOCIATION*

QUOTE:-"Flexibility is an essential ingredient to building a more robust, tough and resilient you. You got to be able to adjust, adapt, change and thrive no matter what circumstance you find yourself in. Be awesome, be tough and be resilient."

     _I dedicate dis page to *Khadija (Mzz Adam) nd Salma Hadi (Allah ya bar miki Korea 😜)*_

                 2⃣9⃣

      *4:30pm*
     *ASHRAF* ya farfado amma kowa ya ganshi yasan yana jin jiki, seda Abba yaje yayi sallan la'asar ya dawo sannan Fahad da Sameer suka tafi, suna fita *ASHRAF* ya kira Abbanshi "Abba" yace "na'am *ASHRAF* me kakeso?" yace "Abba matso ka zauna nan akwai abunda nakeso in gayama", kujera ya ja ya zauna kusa da gadon yana fuskantar shi, yace "inajin ka" yace "Abba akwai wani course mate dina me suna Kabiru amma anfi saninshi da KB, Abba ba yaron kirki bane, ya kware a wurin yaudaran yaran mata" se yayi  shiru dan yaji me Abba zece, "toh kai me hadin ka dashi?" cewar Abba, nan yafara tunanin ta ina ze fara, amma kuma for him to save *ZYNAH* dole ya fadawa Abba komai, gyara zamanshi yayi ya jingina sosai jikin gadon sannan yace "Abba akwai wata sabuwar student, yanzu take level one nd dis guy is trying to destroy her, kuma gata kamilan mace ce, banda karatun ta ba abunda ta sa a gaba, kuma...... " Abba yayi sauri ya katse shi da "tsaya, tsaya *ASHRAF* na riga na gane inda ka dosa, koh baka fada ba na gane akan yarinyar ka shiga fada har aka maka wannan dukan koh?" ,"eh Abba, amma ni bashine matsala na ba, Abba yarinyar nan batada kowa a garin nan, karatu ne ya kawota, ni ina mata kallon kanwata ne, saboda inna ganta kaman Basma nake ganinta, kuma Abba da ace Basma ce a wannan halin dole muyi wani abu tunda bazamu samata ido rayuwarta ta gurbace ba", "hmmm" seda Abba ya sauke numfashi sannan yace "toh me kakeso nayi yanzu?" ,"Abba ta dawo gidanmu da zama har ta kammalla karatun ta", cike da mamaki Abba ke kallon *ASHRAF* sannan ya gyara zama yace " *ASHRAF* kasan abunda kake fada kuwa?, ya zamu dauko er mutane mu ajiye a gida, saboda me, kana ganin iyayenta zasu yarda?" ,"Abba zaka iya, nasan zaka iya, ni zan samuma number iyayenta, seka kirasu, kafada musu komai, nasan zasu fahimci ka" ," *ASHRAF* i don't think dis is possible" ,"it is Abba, please, try, dis girl needs our help, batada kowa, Abba dan Allah" Abba ganin yadda muryan *ASHRAF* ke rawa kaman zemai kuka yasa yace "shikenan zanyi tunanin akai" ai kuwa jin Abba yace zeyi tunani yasa *ASHRAF* jin dadi har yakasa buyewa.

     Zaune suka daga ita se Uncle Yusuf su Ashanty  sun wuce, doctor ne ya shigo dakin dubata yace "madam lfy yazo koh", tayi murmushi tace "gaskiya naji sauki", yace " ai naga alama saboda hakama yanzu zanyi discharge dinku, wannan Uncle dinki ne koh" ,"eh doctor" ,"Ok, toh dan Allah Uncle asa mata ido sosai ta rage shan kayan zaki dan ba karamin illa yake mata ba" Uncle Yusuf yace "In Sha Allahu doctor, zata daina" sannan doctor din yace "ina zuwa, yanzu za'ayi discharge dinta", ai dadi wurin *ZYNAH* ba magana dan dama asibitin ya gama gundurarta, kafin doctor ya dawo har tagama hada kayanta, shidai Uncle kallonta kawai yakeyi, yanda take zumudin barin asibitin. Ba jimawa doctor ya dawo da discharge papers dinta da magunguna ya sallame su suka mishi godiya ya fita suma ba dadewa suka fito wanda fito wansu yayi daidai da su Sameer zasu wuce, dukda ita bata gane shi ba amma shi ya gane ta, har zata wuce yayi sauri ya kirata " *ZYNAH*" juyowa sukayi itada Uncle, shiko Sameer koh shakkan Uncle beji ya karasa wurinta danshi a ganinshi tunda ta dalilinta ne *ASHRAF* ke cikin wannan situation din toh dole ta sani. Karasawa yayi wurin yace " *ZYNAH* kwana dayawa, baki ganeni ba koh" tace "yi hakuri amma ganeka ba" se kuma tace "amma kaman nasan face dinnan" jin haka yasa yace "eh, kinsani, abokin *ASHRAF* ne" tace "ohhh, hakane amma me kakeyi a nan", " *ASHRAF* ne ba lfy", batasan sanda tace " *ASHRAF!!* " ba tareda gwalo ido waje tace "meya sameshi garin yaya", "calm down zo muje ki ganshi in kinaso, in yaso sena fada miki kuma meya faru", juyawa tayi ta kalli Uncle wanda yake kallonsu tundazu yace mata "jeki" dan dama yaji lbrn *ASHRAF* din a wurin ta. Juyawa tayi tabi Sameer wanda shikuma Fahad tundazu yana tsaye shima yana kallon *ZYNAH* wacce tagama tafiya da imanin shi (toh fa😳, wannan shine ana wata ga wata, amma muje zuwa.)

     A hanyan zuwa dakin Sameer yafada mata duka abunda yasamu *ASHRAF* tace " amma ko ba'a fada ba nasan KB ne" yace "shine, amma *ASHRAF* yace beson a tunkare shi tukunnan" da haka suka karasa dakin Fahad na bayansu ba abunda yakeyi banda tunani, suna shiga taga Abba zaune kusa da *ASHRAF* ta gaishe shi  ya amsa ta tambaye mai jiki yace "jiki da sauki", shikuwa *ASHRAF* ba abunda yakeyi banda kallonta, tashi Abba yayi ya fita sannan taja kujera ta zauna Sameer ya fita shi Fahad dama chan be shigo ba, dakin seya rage daga *ZYNAH* se *ASHRAF* shiru sukayi na en dakiku sannan ta daure ta bude baki tace "ya jiki", maimakon ya amsa ta seya zuba mata na mujiya yana kallon ta, seda ta maimaita "ya jikin", sannan yace "da sauki", "Allah ya kara sauki" ,"Ameen", se kuma wani shirun ya biyo baya, ba dadewa ta tashi tace zata wuce ya ruko hannunta yace "ya naki jikin" tace "naji sauki, amma yi discharge dina" yace "Ok, take care of urself" tace "i will" sannan ta fita daga dakin, bataga Sameer ba saboda haka tayi tafiyarta wanda Fahad yananan yana kallonta, itako koh  lura dashi batayi ba. Wurin Uncle ta wuce suka samu abun hawa sukayi tafiyarsu, Fahad na shiga dakin ya zauna yace " *ASHRAF* wacece wacce ta fita yanzu", "oh *ZYNAH*, she's a frnd", Fahad a ranshi yace "a frnd, dats gud" sannan yayi murmushi'' ya tashi yace "ina zuwa", ya fita yana nemanta amma ba ita ba alamunta. Har school Uncle ya kaita sannan yace mata shi yanzu Kaduna  zashi dan a yau ze wuce, ba yanda ta iya dole ya tafi ya barta cike da kewa bayan en nasiha da yamata.

     _Mzz Daddy 💋✍🏻✍🏻_

ZYNAHWhere stories live. Discover now