Chapter 20

1.1K 65 0
                                    

🌻🌻🌻🌻🌻🌻🌻🌻

             *ZYNAH*

(An Interesting Love Story 2017)

By Aisha Muhammad (Mzz Daddy💋)

*BAIWA WRITERS ASSOCIATION*

QUOTE:-" Are you bored with life? Then throw yourself into some work you believe in with all your heart, live for it, die for it, and   you will find  happiness that you had thought could  never be yours".

     _I dedicate dis page to *My luvly Momma* luv u so very much sweet mom.❤😍_

               2⃣0⃣

     Yau ya kama Saturday, ranan da *ZYNAH* take jira ta samu ta tafi inda zatayi chasing dream dinta na zama professional medical doctor. Tunda ta tashi bata koma barci ba seda ta kara kimtsa kayanta ta tabbatar bata bar komai ba sannan tashiga wanka, tana fitowa ta tsane jikinta ta shafa mai tasa kaya, jallabiya tasa peach colour da white veil sannan ta fito lokacin karfe tara tayi, tashiga dakin Momsie da sallamanta, Momsie ta amsa suka gaisa, Momsie tace" Yau an tashi da wuri" ,"banson na makara ne shiyasa" ,"ok,Kingama hada kayanki, bakiyi mantuwa ba" ,"banyi ba" ,"toh shikenan, kira Daddynku da Islam breakfast is ready tun dazo" ok tace ta fita, dakin Daddy tafara shiga ta ganshi zaune kan resting chair yana karanta news paper ta gaishe shi tareda gayamai sakon Momsie yace gashinan fitowa sannan ta tashi ta fita ta shiga dakin Islam amma bata ciki ta duddubata amma bata ganta ba, ta fito ta tarar da Momsie wurin dinning tana shirya wurin tace mata bataga Islam ba, Momsie tace "bangane bakiga Islam ba ina zata da sassafen nan" Jummalo dake tsaye wurin tace "ai ta wuce Islamiyya". Tare suka hada baki wurin fadin Islamiyya? Momsie tace "lalle yarinyar nan zan koya mata hankali, wato yanda zata tsaya suyi sallama da er uwar ta take ganin asaranshi amma ba damuwa, zata dawo ta sameni" ita kuwa *ZYNAH* shiru tayi tarasa tacewa haka kwana biyu nan bata gane kan Islam kome matsalanta oho. Da wannan Tunanin ta zaune Daddy ya fito ba dadewa sega Uncle shima ya fito duk sukayi breakfast Daddy yace "ya banga Islam ba,ko bata tashi bane?" Momsie tace "ta tashi,taje Islamiyya ne wai ance suzo yau da wuri saboda wani gasan makarantu na musabaka da zasuyi" *ZYNAH* kallon Momsie tayi yanda ta shirga lbr ta gayawa Daddy.

     Suna gama breakfast suka koma parlour suka zauna Daddy yafara da "Bismillahi Rahmanir Rahim, yau Allah ya kawo mu ranar da mudukanmu nan muke jira, ranan da zamu turaki makaranta badan komai ba sedan kije ki karanto abunda ze amfane ki ya amfani Al'umma gabadaya, Mamana" ya kirata ta juyo ta kalle tareda cewa "na'am Daddy" yace "ni na haifeki, nine mahaifinki, saboda haka nasanki sosai, nasan abunda zaki iya yi da wanda bazaki iya ba, amma wannan baze hanani yimiki guntun nasiha ba, inason kisani duniyar nan ba matabbata bace, mu dukanmu nan bakine acikinta saboda haka watara duk zamu koma inda muka fito, dan haka nakeso komai zekiyi ki dinga sa Allah a lamarin ki In Sha Allahu zakiga daidai a rayuwarki, duk wanda ya rike Allah ya rike Annabi baze taba tabewa ba, ni banda abunda zan baki a duniyar nan illa ingaya miki Allah Annabi suna kadai kike dasu, kinga yanzu zaki inda ba uwa ba uba, se ke kadai se kuma Allahn ki da manzonki, da fantan bazaki bada min kura a ido ki bani kunya ba" yanzu kam ta fara kuka dan ko ba komai zatayi miss din iyayenta tace "Daddy In Sha Allahu bazan bada maka kura a ido ba koma abunda ya kaini shi zanje nayi" yayi murmushi yace "Dats my gurl, nw stop crying, come sit beside me" ta share hawayenta ta tashi ta koma kusa dashi ta zauna ya lallashe ta yace "ki daina kuka, nasan abunda kikema kuka, na miki alkawarin zamu dinga zuwa lokaci lokaci muna dubaki kinji" ta kada kai sannan Daddy ya kalli Momsie yace "da magana" ta girgiza kai tace "ai ka fada komai, koma ko ba komai na yarda da tarbiyan da naba ýata" yace "hakane, Yusuf fa" yace "ni banda abunda zance ka fada duka koma ita *ZYNAH* she's determined so nasan zatayi abunda ya kaita" da haka suka ta mata nasiha basu suka tashi wurinba se to twelve, duk suka shiga su shirya, Momsie taja hannun *ZYNAH* ta kaita daki ta zaunar da ita gefen gado itama ta zauna tana kallon ta tasa hannunta ta goge mata dan guntun hawayen dake idonta tace " *ZYNAH*" ,"na'am Momsie" Momsie ta kalle tace " *ZYNAH* kinga ke macece kuskure daya mace zatayi kiga tana regretting har karshen rayuwanta ba kaman namiji ba da kome yayi ado ne awurin shi saboda haka nakeson ki kare mutuncin kanki, komai yanada lokacin shi kinji, banda biyewa kawaye kinji" ta kada kai saboda ba zata iya bude baki tayi magana ba dan kukan da yaci karfinta. Itama Momsie karfin hali kawai takeyi tace "ki daina kukan, ya isa haka, ko kinaso nima kisani kukan ne" tayi sauri ta girgiza kai , Momsie tace "toh yi shiru" ta janyo ta jikinta ta rungumeta, sun dade a haka harseda Momsie ta tabbatar kukan ta ya saya sannan ta dagota taga har ta fara gyangyadi(jikin uwa dadine dashi😍) murmushi Momsie ta mata sannan ta bude side drawer ta dauko littatafai guda biyu _ASMA'UL LAHIL USNAH DA HUSNUL MUSLIM_ ta bata tace "ki rikesu sosai kinji" tace "nagode Momsie, in Islam ta dawo kice mata nace in laifi na mata ta yafe min amma zan kirata inna kai" ,"zan fada mata, tashi kije ki fito da kayanki lokaci na wucewa" tace toh tareda tashi tayi waje.

ZYNAHWhere stories live. Discover now