JADWA 7

110 5 10
                                    

Haka dai yan uwa da abokanan arziki ana ta murnan haihuwa a Tanzania kuwa yayan hidaya ce da wata sistern mamanta suka zo Nigeria anan bauchi wajen hidaya domin ganin jariri da kuma taya ta hidima haka.. kwana uku suka yi a hospital akayi discharging insu suka koma gida aranan ne yan uwan hidaya suka iso yusuf yaje airport dauko su.. zainab kuwa kullum nan gidan su Yusuf take yini sai dare abban su marwa watau mijin ta kenan yake zuwa yana daukan su koma wa gida tana taya hidaya aikin jego.

***

Musa ya samu labarin haihuwa yace zai zo wani sati yaga yan uwa dama ya kwana biyu bai zo ba. Haka dai aka ma yarinyar huduba tare tare da shawarar hidaya tace ita tana son a saka mata jadwa Yusuf taso ya mata huduba da saudat watau sunan Hajiya mahaifiyar shi kenan da ta rasu kafin Mallam amma yadda hidaya ta nuna yadda takeson sunan sai ya hakura yace ai akwai gaba InshaAllah.. shikenan yarinyar dai sunan ta jadwa Yusuf kyakkyawa da ita Masha Allah. A daren aranar da aka mata huduba akace akace washe gari za'ayi walima a cikin gidan Yusuf babban gida ne daman an sheda ma makwabta yan uwa da abokanan arziki duka anyi taro anyi wa'azi ansa ma yarinya albarka sosai kuma anci an sha yarinya tayi goshe ta samu kyaututtuka sosai harda yan wajen aikin su Yusuf na Lagos sai suka bashi kyauta Bama kamar cikin garin bauchi yan kasuwan tasha kyauta kam sai son barka..

***
Yau jumma'a ne Musa yace ma Hajiya babba zai zo gida, lokacin jadwa na da sauti daya da kwana biyu, Hajiya ta tambaye shi ko da matar shi zai zo amma Yace a'a daman musa yana da mata salamatu kuma tare suke zama waje daya da dan su guda daya mai sunan Mallam watau Muhammad amma suna ce mashi abbee, amma sai yace A'a shi kadai zai zo tace toh. Ya iso gida banyan sallah juma'a kuma yaje gidan su Yusuf yayi ma jadwa murna tare da Yusuf daga bisani ya wuce kasuwa daganan yaga irin arzikin da dukiyar da Yusuf yake dashi anan ya fara hassada da kuma nadamar da yayi na rashin tsayawa gari kamar Yadda Mallam ya bukata... Bai bari Yusuf ya gane abun da ake ciki ba sai ya sanya mashi albarka amma har shaidan ya fara zugashi yana mashi hudubar banzan game da arzikin dan uwan shi yana cewa karka yarda ya fika dukiya kuma ai kai me babba kayi duk yadda zaka yi wannan arziki nashi su zama mallakin ka.. da wannan tunanin ne ya samu relief, haka dai suka rabu ya koma gida..

***

Yau sunday Musa yayi sallam da yan uwan shi ya kama hanya komawa garin da yake aiki, suko a bangaren su hidaya kuwa sai murna take yi domin jadwa sai wayau take karawa ga kuma yan uwan ta kusa da ita iyayenta kuma na Tanzania kullum sai su yi video call tare harda sistern ta da suka zo wajen ta ita ko zainab su saba da ita sosai, wannan kenan!!!

*** A bangaren Musa ko koda ya isa gida haka ya sanar da matar shi salamatu abinda ya tarar gida ita ma hankalin ta ya tashi sosai haka suka zauna suka ta shawara yadda zasu ɓullo ma abun. Can dai bayan kwana biyu taje wajen wata kawar ta yar kano haka ta fada mata halin da suke ciki da mijin ta anan ta basu shawara da suje kano zata basu address in wani boka zai iya kwashe arzikin Yusuf duka ya dawo wajen musa idan ma kashe shi yake so ayi duk yana yi, anan ta zaro ido😲😲 tace a'a banda kisa. Tace toh ga dai address innan kije kuyi shawara ke da mijin ki, haka ta koma gida da dare yayi Musa ya dawo ta bashi labarin yadda suka yi da kawarta yaji dadi sosai amma yace basai an kashe shi kawai dai ya tsiyace ya koma talautalau har sai yazo roko waje na kuma sai na gadama zan bashi, nan suka kwashe da dariya 🤣🤣 Hmm 😥😥 Rayuwa kenan Allah ya kare mu da mugayen yan uwa 🤲🏻.

****
Yau sati Daya kenan da amso address in boka suka sa date shi da salamatu za suje Kano washe gari zuwa wajen boka, haka ko suka je kano tare da abbee amma abi karami ne shekaran shi 8. Bayan sun isa Kano basu sha wahala ba wajen gane inda boka yake domin sun bi address in sosai..

Da isar su boka yace ya san abunda ke tafe da su ( Ni Ko nace Allah Sarki Albasa batayi halin ruwa ba don gaskiya ba haka halin Hajiya babba yake ba amma banga laifin sa ba rashin samun mata ta gari ne da ace matar shi nada halin kwarai da da yazo mata da wannan maganar da tayi mashi wa'azi da nasiha mai ratsa jiki har jikin shi yayi sanyi ya saduda amma ina bai yi dacen mata ba) haka boka ya fada masu abinda ke tafe dasu kuma suka ce haka ne kam ko shakka babu na boka ya kwashe da dariya kuma yace za'a biya maku bukatar ku, kuka ma zaku biya suka ce boka ya fadi abinda yake so yace za'a saya mashi katon gida a Abuja maitama, kuma za'a bashi 25M Haka Musa ya zaro ido yace idan basu iya ba su wuce ba dole, ( Ni khadee mamaki nake yi nace mai boka zai yi da gida a Abuja shi da yake a daji kuma mai zai yi da kudi har 25M Lallai) nan Musa ya bashi hakuri yace za'a bashi Amma sai sun koma gida zasu dawo da shi.. boka yace za'a mayar da Yusuf matsaya ci ko Naira biyar sai ta koma bashi sha'awa shi ko ba arzikin kaidai zai yi har suna sai sunyi shi da Dangote sai da a goga jiki haka Musa ya kama washe baki yaga banza anan suka yi sallama ya aje ma boka 100k su ka wuce..

***
A hanyan su na koma wa suke ta fira a mota yana ce ma salamatu shi ina zai samu wanannan makuden kudi haka anan ta bashi shawara tace ai da kudi aike sayan kudi ka sayar da duka kaddarorin shi da shagunan da ya mallaka na wajen Mallam ya bada haya yanzu duk ya sayar ai kudin dawowa zasuyi haka yaji dadi don da har ya fara tunanin ya je bank ya aro kudi da wannan shawaran suka koma gida..

Ma'assalam ❤️
Xo khadee

Not edited, ignore mistakes
Please vote and drop a comment..

JADWA (Completed)Where stories live. Discover now