JADWA 17

65 5 0
                                    

Alhaji Yusuf yace ma umma zata je kasar su ne, kamar yadda na taba fada maki ko kuma nace kika tambaya mommyn jadwa yar kasar Tanzania yace, zata can tayi wata uku sannan ta dawo, nan umma ta sake baki tace toh Alhaji wata uku baiyi yawa ba, hidaya ko abun mamaki yake bata toh ita ina ruwan ta ma. Alhaji Yusuf dariya yayi yace ai ita bata ki tayi shekara ba ma, nan hidaya da kama dariya tace wlh kuwa.. nan dai ya gama nasiha har shi yace toh shi kam sai da safe, sai ya wuce bangaren shi, ita kuma umma ta raka su A'isha bangaren su taje tana tunanin toh ita wannan matar meye na wuce wa? Can tace oho dai ai zata dawo, Ni da nake so mu saba da ita zuwa nan da wasu watanni daga nan ta sake jiki dani in samu kanta in fara aiki kamar yadda tabawa tayi mani huduba, hmm ta fada a ranta koma dai menene gobe munyi magana da tabawa.
Da wannan tunanin tayi sauri taje ta shirya don ta nufi dakin Alhaji asha amarci, ita ko hidaya tana koma wa daki ta kai jadwa room inta tace tayi addu'a kafin ta kwanta kamar yadda ta saba ita kuma ta wuce nata room in tayi alwalla ta fara sallah tana rokon Allah da yaye mata damuwa kuma ya basu zaman lafiya..

***
Koda umma aka isa dakin Alhaji da sallama ya amsa shima angon namu ya matsu ya ga amaryen sa.. yace amarya bakya laifi amma yanzu kinyi tace a gafarce ni ranka ya dade yace toh shikenan na yafe.. yace ta zo ta zauna umma cikin zumudi taje ta zauna ya jawo ta ya rungume hmm abun sai wanda ya gani nan suka fara zuba soyayya..

***
Koda gari ya waye, Alhaji Yusuf yace zai je yayi Sallah tace toh, ita ma zata yi nata, umma dai tun lokacin da boka ya hana ta sallah koda yazo yace ta fara da can sallah ba ya dame ta bane, haka dai take yi wani lokaci wani lokaci kuma koh oho, yau ma haka dai tace ma Alhaji zata yi amma ba tayi ba, hmm koda ya dawo tace ai tayi..

***
Bayan karfe goma tayi lokacin hidaya ta karya Alhaji ya shigo, ya gansu tare da jadwa sun gaisa jadwa taje ta hugging in dad inta kamar yadda ta saba ta gaishe shi, ya amsa yana farin ciki, nan dai hidaya ta fara mashi ban kwana yace ai shi zai kai su airport In'sha'Allah.. Ita kuwa umma tana koma wa part inta ta dauki baya taje ta kira tabawa ta fada mata komai akan cewa hidaya zaje kasar su sannan har wata uku zatayi, nan tabawa tace wannan ai ba matsala ba dai zata dawo ba? Idan ta dawo ai sai a fara aiki.. nan tace mata zata zo gobe kuma dole ta samu kudi a kai ma boka saboda aka nuna mashi farin cikin aiki yayi, umma tace ba matsala.. tabawa ta aci gama da shan amarci yar gari, duka suka kyalkace da dariya suka yi sallama.

***
Karfe uku Alhaji ya shiga part in umma ya samu yara da umma zaune, suka gaishe shi ya amsa, daga nan suka tashi zasu wuce side insu, nan yace su zauna tukun sai ya fada ma umma cewa ta fito suyi sallama da hidaya zai wuce kai ta airport yanzu, sannan idan ya dawo yana so za'ayi magana makarantar islamiya yaran nan su fara zuwa harda na boko gaba daya amma yanzu dai za'a fara na islamiya, yace islamiyar yana nan bayan layin su, radiya tayi murna kamar me harda tsalle amma su A'isha haushi abun ya basu a ran su suka ce tun basu gama hutawa ba? Hmm nan umma tace toh madallah sannu da kokari Alhaji Allah yasa da alkhairi ya bani ikon kyautata maka har abada, yace Amin gimbiyata.. nan yace yara su tafi, suma suka ce zasu je su sallami mommyn jadwa nan ko Alhaji ya ji dadin yadda suka nuna kenan sun dauki nasihar nashi da yayi jiya kenan.. lallai zasu hada kan su, ace acikin zuciya..

Haka suka jera suka wuce sai side in hidaya, ta shirya tsab tana jiran Alhaji Yusuf, nan ta gansu tare da umma da yaran ta umma ta fara yace gaskiya zamu sha kewa, hidaya tayi yar dariya tace ai yanzu lokaci gudu suke yi ba wuya za kuga mun gama watanni uku mun dawo, umm tace hakane fah.. nan dai suka yi sallama da Allah ya kiyaye hanya a gaida mutanen tanzania har da A'isha suka rungume jadwa suna mata bye bye wai tazo masu da tsaraba, tace toh a takaice tana dariya ita ma..

***
Haka suka shiga mota sai airport ita kuma umma taja yaran ta suka part insu.. acikin ran Alhaji Yusuf yaji dadi sosai yadda matar nashi suka fara sabawa da juna yaji dadi yadda yaran ma suka fara sabawa da juna yayi mamaki yadda hidaya ta sake da sauri, duk da yasan halin ta yasan mata ce ta gari amma dai duk da hakan, ya kasa boye maganar sai da yayi ma hidaya firan, wlh sweetheart naji dadi yadda kika sake da umma, ita kuma take baki girma ga yara sun fara sabawa ji fa yadda suka yi da jadwa.. hakika zan ji dadi kuma zanyi alfahari daku idan kuka zama mata masu fahimtar juna idan kuka ci gaba da kwanta mu da hankali kuma kuka samar da zaman lafiya gidana, wai meye ma sirri ne iye? Ya tambaye ta.. tace hmm sirrin kenan addu'a, da addu'a da shawarwarin zainab.. shiyasa na kwantar da hankali na matukar zata cigaba da yin yarda ta nuna Ni wlh ba'a samu matsala da Ni ba kuma zan rike girma ma na In'sha'Allah.. gaskiya naji dadi sosai, ai zainab yar uwa ce ta gari. Toh Allah ya maku albarka kuma ya baku yi ikon yi abu nagari tace Ameen...

Suna shiga airport yayi dai dai da lokaci yayi nan tayi sauri da sauka, ma aikatar airport in suka dauki kayan ta, nan dai ya kara masu ban kwana ya rungume yar shi jadwa har baya san sakin ta, yace ta gaida kowa da kowa, zai kara sa mata kudi a waya saboda yaji dadin maganganun da suka yi a mota.

Haka suka wuce ya kama masu bye bye, nan ya tsaya har sai da aka gama screening jirgin su tashi sannan ya kama hanya gida

Not edited
It's short manager it pls
Vote and comment pls
Enjoy ❤️❤️

JADWA (Completed)Where stories live. Discover now