JADWA 14

62 4 0
                                    

𝑨𝒍𝒉𝒂𝒎𝒅𝒖𝒍𝒊𝒍𝒍𝒂𝒉 𝒊'𝒗𝒆 𝒓𝒆𝒄𝒐𝒗𝒆𝒓𝒆𝒅 𝒕𝒉𝒂𝒏𝒌 𝒚𝒐𝒖 𝒇𝒐𝒓 𝒚𝒐𝒖𝒓 𝒑𝒓𝒂𝒚𝒆𝒓𝒔... 𝒙𝒐𝒙𝒐

Ko da ta isa shagon shima ta tayi sallama ta tambaye shi amma cewa tayi ita yar uwanshi ce, yayi mamaki sosai mai shagon yace mata ai jiya yazo amma gyara yayi ya wuce. Sai yana tunanin toh meyasa take tambaya? Abun ya daure mashi kai kamar me
Ita kuma sai taso ta ka gane don taga yanayin shi sai tayi saurin ce mashi sai anjima sai ta wuce kafin ta wuce sai ta kama dube dube ko zata ga idan ake zubar da shata ko Allah yasa taga dattin gashin mutane ko tasan akwai mutane da yawa da yayi ma aski jiya ba Alhaji kade bane bare yace gyara kawai yayi tasan yau dole ya zubar tunda bazai zauna da datti ba koda bai cika ba.
Haka ta fara zagaye can ta hango wani wuri mai datti alam shara ake zubawa, hmm da saurin ta harda haɗawa da gudu nan taje ta fara duba wa ta hango gashi amma a hade suke ta yama za'ayi ta gane na Alhaji Yusuf tabbas nasan me zanyi ta fada a ranta da gudu ta duba ta faki idon mutane samu leda ta kwashe duka gashin da ta gani wurin addu'a take yi Allah yasa akwai na Alhaji aciki shi boka yasan yadda zai yi ya cire na Alhaji ciki. Da wannan tunanin ta gama abunda take yi ta tashi ta fara tafiya ta je idan zata hau mota dadi fal a ranta.

****

Da isar ta bauchi sai gidan umma ita kuma umma tana ganin ta sai tayi sauri ta aiki yaranta gidan iyayen ta acewa bata so su san abunda suke kullawa sai komai ya kammala. Hmm da haka tabawa ta fara ba ma umma labarin irin wahalan da ta sha umma ta jinjina mata sosai kuma tayi murna harda rungume ta tayi.
Haka suka ta farin ciki suka shirya komawa wajen boka gobe da safe da haka tabawa ta koma gida.

Yau Lahadi sun shirya sun sha gwagwarmaya shiga garin da boka yake kamar yadda suka saba kullum suna isa yace tabawa tayi kokari acikin gashin da samo kadan na Alhaji ke ciki amma za'a yi aiki dashi idan sunyi aure dole ta cigaba da samo gashin Alhaji don a karasa aiki don zaman yayi lasting.. tabawa ta washe baki ta ce ba matsala yace toh shikenan kuje ku dawo nan da kwana biyu zan fada maku abunda zakuyi..

***Bayan kwana biyu suka koma boka ya ba ma umma kwalli da turare yace taje ta samu Alhaji kafin taje ta shafawa turaren sannan ta sa kwallin zata ga abunda zai biyo baya..

Haka suka karba suka koma gida tabawa ta umma suka fara shirya yadda zata je wurin Alhaji Bauchi sai tabawa ta ce idan yaje tace tazo godiya ne kuma sana'a komai na tafiya daidai.

Yau umma ta shirya tsaf zata je bauchi wajen Alhaji su umma ansa na kasan kwati an kure adaka, ido ya dau kwalli Masha Allah Amma ni dai banji kamshin turare ba kilan Alhaji kawai zai ji wannan kamshin kuma ta fashe jikin ta dashi.. ba laifi ita ma umma tana da kyau tunda bafullatana ne amma fah baza taba hada kanta da matan Alhaji Yusuf ba hidaya yar kasan Tanzania.

**Tana isa Bauchi sai comapany idan ta saba ganin Alhaji, ta na zuwa ace mata yanzu ya tafi gida haka ta fita taje ta hau abun hawa ana kofar gida suka hadu da ita lokaci ya sauka yana magana da wani da yazo neman taimako. Nan da ya ga umma sai yaji gaban shi ya fadi sai ya karan toh hasbiyallahu alaihi ta walkatu wa hu rabur arshir Azeem.. Yana kallon ta sai ya ga tayi mashi kyau sosai sai kawai yaji yana jin wani farin ciki wanda bai taba jin shi ba.. hmm da fara'a suka fara magana yana mata sannu da zuwa nan suka fara magana da sauri yace ta shigo gida. Anan ya kai ta dakin a baki alokacin ma hidaya ita ma ta sallame bakin ta mata kenan da suka zo wajen ta, nan koh kawai yanda taga Alhaji yana mata dariya suna fara'a sai abun ya bata mata rai toh ita wannan mai tazo yi haka shine suka shigo tare suna dariya bayan rannan ba haka suka yi ba tana fada a ranta tana hade rai.
Anan ya ma hidaya magana wai mai aiki ta kawo mata abinci nan hidaya tace ba tana nan ta wuce saman abun ta, nan umma ta harare ta tace duk kin bari tun kafin na shigo kin fara iyaye zaki ci ubanki, ai naga aikin boka ya fara tunda ya rikici sai surutu yace zuba mun, nan umma ta bashi labarin kasuwan ci na karya nan Alhaji yaji dadi yace zai kara mata kudi, haka dai suka ta fira abunda bu su taba yi ba, nan Alhaji ya tashi da ganshi yaje kitchen wai zai kawo mata abinci taji haka ya jera abinci harda lemu nan suka hadu da hidaya take tambayar shi nan ya fada mata tace wai ita wannan matan har yanzu bata wuce ba toh wai ma mai tazo yi ? Nan ya kama dariya yace godiya yazo yi mana yana fadar hakan ya wuce abinsa ita koh hidaya abun mamaki ya bata hade da daure mata kai.

Yana saukowa ya tare shi da karban abinci na mashi dariya wai yana kokari wlh nan dai ta fara ci tana mashi fira shi kuma sai dariya yake yi kamar ya ga wawan zama😂 da haka suka gama ya tura ma umma kudi dubu dari biyar yace ta kara jari sai dariya take tana godiya, nan tayi tunanin mai zai hana ta karbi numbern Alhaji tunda ta ga ya fara fadawa. Nan ta fara mashi bayani wai zata so numbern shi koda zata nemi shawara na sana'ar ta ba sai ta ta zuwa ba yau ma ta ga Hajiya kamar bata ji dadin zuwan ta ba yace kina da gaskiya umma amma karka damu da hajiya bata da lafiya ne. Nan ya karbi wayan ta yasa mata numbern shi umma taji dadi sosai tayi godiya, ana cikin haka sai ga wata kyakkyawar yarinya ta fito suma har kadon baya duk da kullar da ta sa akai bai hana gashin ta fitowa ba tace "daddy mommy na Kiran ka" nan tabawa ta sake baki tana kallon ta don yayi tayi mata kama da irin yaran nan da ake sawa acikin tv yaran larabawa. Duka yarinyar bazata wuce shekara goma sha uku ba.. hmm nan yace ma umma kin ga yata nan, nan kuma ta gama yaba kyaun yarinya tana jawo ta jiki kamar zata cinye, ita ko jadwa sai baya baya take yi, nan dai suka yi sallama ya hau sama , ita kuma umma ta jiya ana farin ciki za'a koma ningi da labari mai daɗi...

Not edited..
Sorry it's short chapter manager it pls
Don't forget to vote and comment..

JADWA (Completed)Where stories live. Discover now