JADWA 10

93 5 0
                                    

Ko salamatu ta fara bada labarin abun da ya faru tana fadi tana kuka sosai kowa yayi mamaki harda yan uwan ta Hajiya babba haka taji abun babu dadi shi ko Yusuf idon shi sun yi jajir yana kallon ta.. cikin yan uwar yarda masu kuka kamar zai su zainab idon haka yayi ja kamar tankwa hmm rayuwa kenan.. Yusuf yace haba salamatu yanzu abunda kuka a kata kenan nan take Hajiya babba ta katse shi ta ce basai yayi magana ba.. tasan abun babu dadin ji amma kuma karya mata da halin shi na yafiya da kuma taimako da tausayi shiyasa Allah bai bari sunyi nasara ba ita ma kata a kasa tana neman ma ɗan ta yafiya tunda baya raye hmm. Nan Yusuf yace haba Hajiya ki tashi mana.. da haka dai Yusuf yayi godiya ma Allah da ya kubtar dashi daga sherin masu sheri haka ya masu nasiya kuma yaje ma salamatu kunne yace yanzu ya zama izina a gare ta hmm shikenan yace ya yafe masu kuma zai ci gaba da kula da ita da abbee kuma zata zauna gidan ta kuma zai bata kudi za'a fara mata kasuwanci kuma zai bata shago daya ko da abbee ya girma na shine halak malak duk wata kuma za'a rika kawo mata kudi shima zai rika kawo mata kudi na chefane da sauran hidiman gida kuma yana so wannan maganan za'a binne shi anan a rufe bayaso wani ya bare yasan da wannan maganar ko da wasa a haka kowa yaji dadin abunda Yusuf yayi kowa ya dauki darasi.. wannan kenan.

****A kwana a tashi ba wuya haka rayuwa ta cigaba ta tafiya abubuwan Yusuf sai kara tafiya suke yi yazama shahararren dan kasuwa sai bude companies yake yi iri iri ya bude na taki, na shinkafa, na gishiri har da na man ja.. arziki sai gaba yake yi Alhamdulillah zamu ce ita ma hidaya na aiki a karkashin Company inshi na daki ita je director manager. Jadwa ko tayi wayau yanzu tana primary 6 zata shiga jss1 ita ko Hajiya babba jikin tsufa kullun sai kara wa yake yi... Hidaya tana zuwa Tanzania idan su jadwa na hutu aje ayi hutu acan har sai hutu ya kare a dawo watarana kuma Yusuf yana zuwa dasu tare har gida ya saya a Tanzania idan sun je can suke sauka sai dai ake gidan yan uwa..

** Kwatsam wata rana Hajiya umma ta zo neman taimako wajen Abba (Alhaji Yusuf) ta same shi har Company inshi na manja.. duk lokacin da zata zo bata samun shi haka dai ranar taci daga ta tarar da Abba yana sauri an yi mashi kiran gaggawa zasu je meeting na manyan yan kasuwan garin. Abba bai so ya tsaya ba amma saboda bai so taga kamar ya wulaqanta ta haka ya tsaya sai yace mata zai bata time tayi hakuri yana da meeting Amma ka lokacin da ya ka tamata yazo ta same shi. Haka taji dadi tayi Godiya ta wuce amma ya fara tausaya mata hanayin da ya ganta gashi kuma lokaci bai bashi daman yin magana da ita ba. Hmm ita ko a bangare umma dadi Pal a ranta haka ta wuce gida taje tana bma yaran ta mata yan shekaru goma sha huɗu sha biyar labarin ta same shi yau amma bai tsaya ba yana sauri zai je meeting Amma ya bata lokacin da zata dawo ta same shi.. haka suka ji dadin

***Labarin wacece Hajiya Umma***

Kuma dai yar mata ce mai shekara 49 lokacin yar asalin garin Bauchi ce acikin kauyen ningi ana ta tashi take rayuwar ta da mijin ta kafin taulaci da rashi yasa ya guda ya bar ta da yara yan mata guda 4 lokacin akwai mai shekara goma sha biyu sha uku sha hudu da kuma sha biyar.. Haka su ke rayuwa wata rana a kwana ba'a ci ba wata rana kuma a kwana ba'a koshi ba hmm . Anta nema mijin umma har an gaji yan uwan shi kuma ba'a kauyen suke ba ciki ma zan ce dan uwan shi daya kawai su umma ta sani ita da iyayen ta ko shi ana tunanin ba dan uwan shi bane kawai dai lokacin ta sa nacin ziya sai ta aure shi haka akayi hakuri aka aura mata shi.. amma yace daga Chadi suka fi neman abinci a lokacin da ya gudu nemi shi wannan da yace dan uwan shi ne amma an rasa haka akayi tunanin ko tare suka gudu.. dama government schl yaran umma suke dole ta cire su 🥺 idan taje gidan iyayen ta su Korea ta suce suma suna fama da kansu ita bata taimaka masu yanzu kuma tazo ta sa masu wahala ai sai da aka fada mata aki ji tace sai shi yanzu gashi ya aure ta ya barta da yara tana wahala.. hmm umma har bara ta fara yi ta shiga garin bauchi taje tayi Bara idan Yamma yayi ta koma ningi haka dai take ta yi.. watarana a kasuwa ta take bara Abba yazo yana raba kudi dubu hamsin hamsin yana ba ma mabarata, Kowa ya samu harta da umma ai ranar da koma ningi sai murna take yi a hanya da ta shiga Mota taji ana labarin irin kudin Alhaji Yusuf watau Abba kenan hmm umma ta fara raya ma kanta mugun abu.. anyi labarin shi sosai akace yana taimakon talakawa kuma yana da tarin duki, anan ko umma ta lashi takobi sai taje wajen shi ya taimaka mata kuma da kudin shi zata shiga ta ban zama ta mashi asiri wanda zai aure ta kuma taji ance yana da mata da yarinya daya ita duk sai ta raba su dashi ta jawo yaran ta cikin gata sun zama yan gata da kyau da kyau tace yanzu ko tace zata je wajen malamai ita kam bata da kudin da zata basu gwara taje ta roko kudin wajen shi sannan ta fara shiga tana fita ta gaji da wannan rayuwar talauci 💔 SubhanAllah nikam nace Allah baya daura ma bawa abunda yasan bazai iya ba. Ana cikin haka taji ace an kawo ta sauka. Ta sauka mota ta ta samu mai mashi ya ke ta gida dama umma anyi sayayyan kayan dadi 😁 su shinkafa da kayan miya harda kan akuya aka farfasa ma umma yau ita da yan matan ta za'aci dadi.. haka ta ita isa cikin gida tana basu labari suma sa dadi suke ji yau daga ci shinkafa yaushe rabo. Haka suka fara hada kayan girki aka daura girk, amma umma ko ta tuna da iyayenta ta kai masu ina ita daga ita sai yaran ta tasani. Sai ta basu labarin ma zata je wajen shi neman taimako, amma bata fada masu mugun nufin ta ba a cewa tayi har yanzu yara ne zuwa gaba zasu sani, suka ce lallai kam umma gwara ki je ita dai daya daga cikin su radiya kenan tace umma ni dai idan kinje ki taimaka kice ya cire Ni makarantar gwamnati ya sani ta kudi wallahi cikin aji munyi yawa mu kusan 70 dan Allah ya za'ayi mutum ya fahimta.. su yan uwan mamaki abun yake basu ita bata da wani magana sai na karatu karatu.. tace toh karni damu autana In'sha'Allah har kasan waje ma sai kinyi karatu haka ta koma jin dadi..

** A yau ne ranar da Abba yace ma umma ta dawo ta same shi.. haka umma keta sauri karta makara tayi sauri shirya ta bama yara kudi tace suyi chafane suyi abinci. Ita kam yau har wajen Alhaji zata je suna ta mata addu'a Allah yasa a dace.. tace Ameen haka ta je gareji ta samu mota ta hau sai bauchi daganan kuma daga saukar ta bauchi ba bata lokaci ta samu abun hawa sai Company Alhaji Yusuf.. ko mai zai faru ? 🤔 Ni kai na ina son sani

Vote and comment pls..
Next chapter coming soon In'sha'Allah

JADWA (Completed)Where stories live. Discover now