JADWA 50

108 4 0
                                    

Alhamdulillah and this is the last chapter of this novel no matter what I'm ending the novel here 🥺

    Godiya ya tabbata ga Allah madaukakin sarki.. mai kowa mai komai ❣️🥺🤲

Amare na zaune gidan su lafiya lau sai son barka, komai na tafiya dade

Ita A'isha da Ahmad suna fahimtar juna kuma har an tsayar masu da rana wata biyu kacal za'a daura masu aure.

Cikin mommy yanzu ya shiga 9months kula take samu sosai wajen Abba kamar mommy bata taɓa haihuwa ba.

Abubuwa sai gaba sai keyi ma amma zuwa yanzu harkan kasuwanci babu wanda bai son shi idan maganar kayan abincin ne da na companies babu wanda bai son da sunan Abba ba, kuma taimaka ko baka buka sai yayi maka shi.

Shi ko Dr fahad a ranar bai yi bacci sai da yaki Aunty ya fada mata, ita ma tayi murna sosai haka ta fada ma daddyn shi kowa yayi murna harda mommy, kamar yadda yayi alkawari yace zai zo ya dauki jadwa haka ko yayi.

Mommy ta bata shawarwari akan yadda zata kula da babyn da ke cikin ta. Ta ji kuma ta gamsu haka ya dauki matar shi ya wuce da ita abuja yana kula da ita.

Yau Saturday mommy ta tashi da ciwon mara Abba ma baya kasa ya je Benin republic, driver ta kira da mama da su fatima da sauran yan aiki a ka wuce da ita hospital ko abba bata kira ba tunda ta san bai gari.

Shi kan shi Abba bai so yaje tafiyar ba saboda yasan cikin hidaya ya tsufa amma dole ne yasa yaje.

Koda suka isa tayi labour na 8hours Allah ya sauke ta lafiya ta haifi santalelan yaron ta mai kama da Abba.

Mama ce ta kira Abba ta mashi albishiri ba karamin dadi yaji yace ya ba mama kujerar Makka tace Alhamdulillah a she zata ga kasa mai tsarki tace amma zata iya zuwa Makka da tsufan ta kuwa Abba yace wa'inda ma suka fiki tsofe wa sun je sai tayi dariya yace shima nan da 2hours zai sauka Bauchi In'sha'Allah tace toh Allah ya yarda.

2hours later sa ga Abba ya dira hospital lokacin suna hada kaya zasu koma gida, ko da ya dauki yaron lalle Allah mai kyauta da kari yace alhamdulillah yanzu wannan nawa ne. Allah nagode maka harda sujood yayi.

An kira yan Tanzania suma sun fara shirin zuwa naija asha suna dasu.

Jadwa da taji an haifar mata gani ba karamin murna tayi ba koda aka tura mata pics inshi bai mata ba ita so take yi tazo Dr fahad yace a'a sai ta kara kwari saboda har da birth rest ta dauka jiki ba kwari ko school ta daina zuwa sai da su fita office tare idan ya tashi aiki su tsaya restaurant suyi take away su dawo gida.

Haka ta hakura ranar suna harda kuka tayi kasancewar yana son abun da jadwa take so ya lallaɓa su, suka je bauchi hakanan, Abba yace zai sa mashi suna Yusuf wata tunda yana kama dashi kuma magajin shi ya kasance ma sunan su daya jadwa harda kuka wai ita Jawad take so a sa mashi.

Wannan cikin na jadwa yasa mata shagwaba sosai dama can akwai shi hmm haka Abba ya karbi bukatar aka ma yaro huduba da Jawad.

Dr fahad ya jira aka gama suna ya lallaɓa matar shi ya koma da ita abuja ya cigaba da rainon cikin shi.

Yan Tanzania kuwa kamar kar su koma saboda yadda suke jin dadin zama gidan kuma ga yaron gwanin ban sha'awa tubul tubul Masha Allah.

Sati biyu da sunan Jawad Ahmad ya matsa ma babban shi akan aure aure da a matso dashi baya a daura masu aure sati mai zuwa, Alhaji Abubakar yayi mamakin hakan wai yau ne Ahmad ya samu mata har yana damu da azo a daura masu aure, duk miskilanci ɗan nashi kuwa ya san shi da kunya.

You've reached the end of published parts.

⏰ Last updated: Feb 21 ⏰

Add this story to your Library to get notified about new parts!

JADWA (Completed)Where stories live. Discover now