JADWA 28

52 5 2
                                    

Cigaban labari..

Bismillahir Rahmanir Rahim

Sir fahad yadda students ke kira shin a Bauchi kenan Amma a Abuja inda yake aiki da kuma Adamawa ko wa Doctor fahad yake ce mashi sai yan gidan su da suke kiran shi da yaya fahad.

Bayan ya koma gida yaji dadin yadda jadwa ta sake jiki dashi har da abokin shi sai da ya ba ma labari yadda komai ya faru, shima ya taya shi murnar kuma ya mashi addu'a Allah ya tabbatar da alkhairi kuma yaji dadi sosai.
A daren sun dade suna waya sosai yana tambaye ta abinda ta ke so da banda bata so na zamantakewa rayuwar daga amsar da take mashi ya gane cewa hakika ita mai sauki kai ne tabbas idan son shu ya ginu a zuciyar ta ba ƙaramin dacen mata zai yi, ya lura bata san hayaniya kuma ga iya magana cikin sanyi rai, gata kyakkyawa ga ilimin addini da na boko amma yana so ya kara sanin labarin ta da kyau shi ina mahaifiyar ta tana a raye? Ko ko duk suna magana ne yake wannan tunanin amma sai yace ba zai tambaye ta yanzu shi dai bari ya jira sai ta kara tambayen shi labarin shi da kyau da kyau shima sai ya tambaye ta.

Na ko samu karɓuwa shin zuciyar ki ta amince dani ? Tambayar da sir Fahad yayi mata kenan cikin waya, hmm kayi abunda ya dace kamar yadda na fada maka amma dole sai ka bani lokaci nayi istihara domin neman zabi wajen Allah.. kina gaskiya jadwa kyawon ɗabi'un ki suke kara burge ni da ke kuma nake ji sonki sosai acikin zuciya na amma ina so na tambaye ki ko kina da saurayi ne ? A'a bani da kowa wlh kuma ko da na fara makaranta babu wanda ya zo waje na da da sunan soyayya bantaba magana da kowa ba idan ba mata ba suma akwai wa'inda ke mun kallon matar aure watakila saboda irin shigar da nake yi ne amma baya damuna Saboda ina jin dadin when I covered myself properly wearing jilbab wallahi I feel very comfort and safe, shi yasa nake jin dadin hakan. Nayi mamaki da kazo gareni a haka, naga maza da yawa suna son macce wanda ta ke bude surar jikin ta. Wannan tunanin wasu mazan kenan amma ni wallahi jadwa komai naki yayi mun kuma zan yi alfahari da ke a matsayin matata.. idan na fahimce kenan baki taba soyayya ba ta daga kai tana kamar tana kusa dashi yace Jadwa naji kinyi shiru tace eh ban taba soyayya ba yace wow wow toh Allah yasa mu dace naji dadi sosai.. sai ya rasa mai zai ce mata daga nan dai suka yi sallama yace mata gobe zai kira ta da safe In'sha'Allah sai tace mashi ita ma tana so yayi istihara idan ta tashi yin Sallahn Tahajjud da dare zata kira shi. Haka ba karamin dadi yayi mashi ba yace toh shikenan naji dadi sosai jadwa Allah ya kai mu ya fada yana murmushi suka yi sallama.

Karfe 4:00am jadwa ta farka ta je toilet tayi tsaki ta yi alwala ya fito ta dauko waya ta fara duba numbern sir fahad kira daya ya kare bai dauka ba ta sake kira sai gashi ya dauka, Assalamu alaikum ya fada muryan shi kasa kasa ta amsa wa alaikumus salam Dr na tashi za mu iya yi yanzu kayi addu'a sosai kaji. Toh yace mata yace lallai kin cika alqawari kuma zanyi kamar yadda kika ce tace toh Allah ya zaba mana duk abunda yafi zama alkhairi a rayuwar mu Ameen ya fada yana jin dadin Maganar ta.
Yadda tayi maganar ba karamin dadi yaji ba da kuma yadda ta kira shi Dr tun da farko da kuma addu'a da ta nemi yayi wow kawai ya ce a zuciya ba shiri ya mike shi ma sai toilet don dole ya roki Ubangijin shi domin samun jadwa sai ka haɗa sallahn dare sai gashi kuma itace da kanta ta tace karfafa hakan.

Yayi alwala ya zo zuwa jallabiyar shi ya fuskanci gaban ya sa dadduma ya ta fara sallah ya roki Allah zabi ita ma jadwa haka tayi a bangaren ta. Bayan ya idar ya kira ta tace zata yi karatu ta cigaba da azkar sai lokacin sallah asuba yayi sannan tayi ta kwana yace shima zai yi hakan In'sha'Allah komai tare zasu yi duk da kasancewar basu tare Amma zuciyoyin na tare da juna ta ji dadin hakan tace toh shikenan.
Shi ko a ranshi bayan ta yanke wayan sai tunani yake yi iri iri wai daman akwai irin jadwa kuwa ? Gaskiya yarinya ta haɗa duk abunda ake son macce shi addinin ta ma ya fi burge shi kata da kyau gaskiya dole ya dage da rokon Allah don idan ta amince shi bazai bata lokaci ba kafin ya koma Abuja sai yaje Adamawa azo a nema mashi auren ta idan ya so karatun ta karasa gidan shi ko kuma ya mata transfer ta dawo Nile University ta karasa karatun ta da haka yake ta wannan tunanin yana kuma azkar yana ambaton Allah har lokacin sallah ya yayi bayan ya yayi Sallah da idar sai ya kira ta sun gaisa ta gaishe shi cikin sanyayyen murya ba su yi fira mai tsawo ba ya tambaye zata shigo makaranta ne tace ai sai 2pm take da lecture yace toh Allah ya kai mu tace Amin atakaice sai su kayi sallama shi kuma ya dauki Qur'an ya fara karatu da ya gama sai ya kwanta.

JADWA (Completed)Where stories live. Discover now