JADWA 4

276 13 6
                                    


    ~~Tushen labari~~

Gidan Alhaji Yusuf muh'd, gida ne na alfarama. Kuma Alhaji Yusuf muh'd ya fito da ga idan mallam muh'd haifaffen Dan garin bauchi su biyu ne kacal wajen mahaifiyar shi Hajiya saudat. Sai Hajiya babba wato ita ce uwar gidan mallam muh'd. Tana da yara biyar dashi mata biyu maza uku sai Hajiya saudat mahaifiyar su Alhaji Yusuf. Yaranta biyu Yusuf na farko sai zainab...

***

Ba laifi sun taso cikin tarbiya da kaunar juna basa nuna bambanci tsakanin iyalensu hakan yasa mallam muh'd ya ke jin dadin matan shi, duk unguwan su ana kwantace da gidan shi, babban nan kasuwa ne, yana da shagogi da dama acikin garin bauchi da store, store sannan ya gajin mallamcin shi wajen mahaifin shi yana karatu sosai, haka yaranshi idan sun gama makaranta suna zuwa gaba idan sun gama gaba sai su nemi aiki idan da akwai masu shawa'awan yin kasuwacin dama ya daurasu akai sai su ci gaba, lokacin na tafiya yan matan gidan shi sunyi aure maza kuma biyu suna aikin office, daya na kasuwacin, sai dai Yusuf da ya taso dason zama pilot tun yana yaro yanzu haka mallam muh'd ya tura shi China yana karatun shi, wannan kenan!

Shekaru sun jan, kullum ana kwana ana tashi, rannan da Yusuf ya dawo China ya kammala makarantar shi a ranar mahaifiyar shi Hajiya saudat ta tashi da matsananciyar ciwo, kafin kace mai Allah yayi mata rasuwa, ba mallam muh'd ba kowa na gidan da mutanen unguwan sun girgiza, haka ake ta fadan kirkin ta a na yabon ta. Koda Yusuf ya iso bauchi an rufe mahaifiyar shi sai dai haka yayi kuka da bakin cikin rashin ta ya je kabarin ta ya mata addu'a

Haka Yusuf yayi zaman wata shidda yan uwanshi yaran Hajiya babba na bashi shawara akan ya rage tunani, sai yace toh, shi ko mallam muh'd tun sanda ya rasa Hajiya saudat ya koma wani kalan tausayi mara lafiya lafiya, haka Hajiya babba tayi magana har ta gaji sai tayi tunanin kodai dama ashe mallam yafi son saudat akan ta ne🤔 sai can tace toh ai Kuma saudat na da kirki dole mallam ya shiga damuwa da yawa Allah dai ya kara mana hakuri....

Lokaci lokaci hidaya na dauke ma Yusuf damuwa ta jasu da hiran soyayya, Hidaya buduwar yarinyar yar kasan Tanzania da ya hadu da ita a lokacin da suka kawo kakarta asibiti a China. Anan suka hadu a lokacin ya je raka abokin shi asibiti, suka yi exchanging number, hidaya is friendly and fun to be with, ya yaba da halayen ta sosai daga nan sai soyayya mai karfi ta shiga tsakanin su, wannan kenan!

Ya Yusuf congrats!!! Thank you lil sis, zainab kenam da tazo gida ganin mallam bashi da lafiya a lokacin shi Kuma Yusuf ya samu aiki a Lagos zai fara tukin jirgin sama...

Lil sis kinzo gaida mallam ne? Eh yaya ya jikin shi? Ya ji sauki sosai zee sai dai kinsan mallam baya son zuwa asibiti sai a bashi ruwa a kofi yayi addu'a ya sha ya shafa. Toh yaya ai gwara haka ba abunda yafi addu'a. Hakane lil sis kina da gaskia.
Toh kawo marwa karki shiga da ita Naga tana kuka Kuma kinsan mallam baya son kuka barai kuma bashi da lafiya yanzu.. toh gata, oya je uncle Yusuf sai ta mika mashi marwah diyar ta ta biyu kenam akwai marwan sai ita marwa. Can kafin ta shiga dakin mallam tace yaya bara na dawo akwai magana. Toh a fito lafiya!

Mintin 15 tayi acikin dakin da gaishe Kuma sun yi yar fira ta tashi tayi mashi sallama sannan ta bar wajen ya kara bata shawarwari kamar kullun tare da nasiha, tayi godiya tayi mashi fatan samun lafiya.

Koda zainab ta koma har Yusuf ya lallashi marwa tayi baccin a kan kirjin shi. Tace yaya har wannan kasan tayi bacci, haba zee, baby tace kasa kuma, toh yaya idan ba kasa ba bacci yanzu yanzu.. hmm ke dai ina marwan ? Oh sun je gidan mama da shi da Daddyn shi sai yamma zai biyo dashi tanan sai mu wuce gida. Yace Allah ya kai mu, tace ameen....

Yawwa yaya wallahi tunanin hajiya ya maka yawa ka rame sosai, hmm yaya ba hmm zaka ce ba rage wa zakayi ni kana ganin kamar bana yi ne koh? Eh ko dai kina yi baza ki kai ni ba zee.

JADWA (Completed)Where stories live. Discover now