JADWA 19

60 5 0
                                    

Koda ta juya taga Abba sai jikin ta yayi sanyi amma shi ko kadan bai ma gane idan maganar ta ya nufa ba ko kuma nace ko dai so ne ya dauke mashi hankali haka? Oho.
Sai yace gimbiya ya kike tace lafiya lau mijina, nan taji sanyi cikin zuciyarsa ta ita kam tunda Abba bai gane maganar da take yi ba... Bayan ta suka gama gaisawa sai yace mata shi kan zai fita, tace sai ya dawo.

Da yamma bayan hidaya ta gama sauke gajiya sai ta kira su umma ta raba ma kowa tsaraba har da mutanen babban gida sai da aka kai masu har dasu zainab duka.. yaran umma an kwashi tsaraba su don bayan na hidaya itama jadwa ta saya masu su chocolates da perfumes da mini hijabs da fashion school bags haka suka ta jin dadi don kayan suna da kyau sai wanda ya gani wlh..
Nan umma baki yayi shiru don ba karamin tsaraba ta sha ba a zuciyar ta tace wannan bashi zai hana ta fara aiki ba, haka ta kira tabawa ta bata labarin komai kuma tace ita ma zata aiko mata da nata.. tayi godiya tace harda ni kuma tace ai ta basu da yawa kar ta damu ita kuma babu abunda bazata iya mata ba..

***
Kwana a tashi haka rayuwa ya cigaba da tafiya su hidaya yanzu ta sake jiki da umma sosai yara kuma sun saba da jadwa tare suke zuwa schl da islamiya duka.. haka su umma da jadwa ake fira kullum wannan zata je part in wannan, haka dai kowa na zuwa.. Abba kuwa dadi yake ji yana samun farin ciki sosai ita dai umma na ciki na ciki.. amma su A'isha har ga Allah suna don jadwa sosai basu kuma don kowa ya ta bata saboda yadda itama take ji dasu kuma take basu duk wani abun da mommyn ta zata bata..
Yau watan sun biyar da aure kenan wato umma da Alhaji Yusuf.. nan umma ke tambayar tabawa ya kamata ace sun fara karban magani wajen boka tun yanzu har abinci suke ci tare da hidaya, tabawa tace ta dai kara hakuri.. ita tasan lokacin da ya dace a fara aiki..
Haka rayuwa ya cigaba da masu sai kara shakuwa suke yi da juna amma ita umma bata da farin jini cikin family insu Alhaji Yusuf.. kwata kwata ko babban gida suka je ba mai sake jiki dasu, ita da yaran ta amma hidaya kan kowa yana son ta dama, jadwa kuma babyn of the family kowa yana ji da ita don yarinya yace mai wayau ga ta fara tas kamar mommyn ta, ga ta yar doguwa da ita kuma gashi kusan dai wata ƙasa mommyn jadwa ta fito fadan kyaun jadwa zai cika shafi.. don da kaga jadwa to kaga mahaifiyar ta...

****
Gobe juma'a umma ta nemi izini wajen Abba tana so taje ningi, a lokacin ma baya kasa don yanzu arziki sai karuwa yake yi su ko su A'isha jin kansu suke yi kamar Abba ya haife su don basu ma son asan ba yan gidan bane.. 😛 hmm kowa schl sai dai auce ai su yan gidan ne., Sai ata mamaki toh ya surname insu ba daya ba?
Sai ji da kai suke yi kamar me, toh ko da umma suka yi waya yayi mata izinin kuma ya bada mota a kai ta, su A'isha sun ce baza su je su yanzu basu son zuwa ningi su sun zama big girls.. 😁 Haka washe gari yayi umma ta shirya sai ningi, ta sallame hidaya kuma tace ta gaida su mama harda kaya ta bayar ana su mama ta karba tayi godiya ta wuce amma Allah kadai yasan abun da ke cikin zuciyar ta..

***
Koda ta isa ningi bata sauka ko ina ba sai gidan tabawa anan ta yada zango, sun sha fira sosai nan ta raba kayan da hidaya ta bata taɓa ma tabawa kaya ne masu kyau atamfofi masu tsadar gaske amma sai da taba ma tabawa.. nan tashe da mata gobe zasu shirya su je wajen boka don da shirin ta tazo, don umma kam ana kwasan kudi wajen Abba kamar bai don kuma shi mai bayar wa ne.. bayan da su ka gama fira ta wuce gidan su koda taje ta tarar da baba ba lafiya nan take ta kira waya Abba ya turo da likita har ningi anyi mashi treatment masu kyau kuma tace ma Abba zata kwana biyu saboda ta kula da jikin baba bai ce a'a ba yace Allah ya bashi lafiya ba matsala. Ta ba ma mama sauaran kayan da hidaya bata, mama tayi godiya sosai wlh kuma tace ta kira mata ita a waya ta mata godiya haka akayi hidaya tace ba komai har kunya ya kamata ta kashe waya saboda yadda taga mama nata godiya..

Yau tabawa tayi sammako tazo gidan su umma, mama tayi mamaki, sai tabawa tace fditar ta ne ba lafiya zasu je gaida ita, tayi mama karya don ta ma rasa mai zata ce mata, ita kam mama sai addu'a ta ke tayi..
Daganan umma ta shirya ta kimtsa suka kama hanya sai wajen boka..
Suna isa ya daka masu tsawa don basu sallama kuma wannan ihun da yake yi duk sun saba..
Daganan yace yasan me ya kawo su, za'a mai suke so ayi ma hidaya? Umma tace tabawa tayi magana, ta fara magana kamar haka, mu dai muna so a fara bamu abunda zamu sa mata cikin abinci wanda zata ta wahala kuma a rasa abunda yake damunta..
Daganan kuma muna so dai idan ta gama wahala sai a mata wanda zata haukace kuma wanda baza... Kee!!!!! Dakata hakanan nafi ku sannin abun da ya dace, tace tohtootoh jikin ta na rabawa don taga yau ya chanza, zuwa yayi ya shiga bukkan shi ya ciro wasu kullin magani guda biyu sai layu guda biyu yace wannan maganin a zuba mata a miyan kan rago, taci sannan wannan layu ta gina rami ko a ina acikin gidan su ta kira sunan ta sau biyu sai ta sa layu duka a rami daya, bayan tayi haka sai ta rufe kuma kar ta juya baya idan ta gama.. yace kunji bayani na da karfi su ka hada baki suka ce ehh munji nan umma ta tambaye cikin tsoro tace idan nayi miyan kan ragon za mu iya ci tare yace eh ai ita zai kama ba ke ba kowa ma zai iya ci amma sai dai ya kamata ba wa'inda suka ci ba tace toh Nagode tace da wani lokaci zan sa layun yace da asuba ya fada a takaice.. nan suka bashi dubu dari biyar yace su aje su fice su kama gudu kar su juya sai sun fita dajin don yau aljannun ransu a bace yake, za'a iya samun matsala. Toh suka ce suka tsaya suna kallon juna ya daga masu tsawa yace ku tafi mana!!!! Da gudu zuka fece 😂
Ko da suka kai kar shan fita dajin, nan suka kama nishi umma kamar zata sume, an fara shan dadi gidan Abba yau an kwashi gudu😂😂 kamar za'a mutu.. hmm ita ko tabawa sai nishi daya daya.. nan dai suka huta ba mai ce ma kowa komai sun kusan kai 30minutes haka ba abunda suke buƙata sai ruwa don ko gudun da suka kwasa wajen fitowa dajin yafi 30minutes, nan suka ga wata yarinya ta fito da tulu daga wani hanya saman kanta.. aiko da sauri umma ta kwala mata kira bata ji sai tabawa ta ta shi ta bita, ko da tace ta ma yarinya magana wai ta taimaka masu da ruwa nan yarinya tace to amma ba kofi tabawa tace ba matsala suke can wajen yar uwan ta ta ita gajiyan da kishin da suka kwaso bai bata ma ta iya tashi ba, yarinyar ta tausaya masu haka tabi bayan tabawa suka isa wajen umma nan tabawa ta tara hannu tace yarinyar ta zuba masu, aiko haka tayi ita ma umma tayi haka bayan da suka sha suka koshi, nan umma ta dauko kudi dubu daya ta bata amma ina yarinyar ta ki karbar tace ita saboda Allah tayi.. sun mata godiya sosai, sai ta wuce suna suka fara shin tafiya su je inda zasu hau mashin su shiga ningi..
Baya sun isa ningi mama ta masu sannu tana tambayar ya mai jiki haka suka ta karya suna ai taji sauki sosai..

***
Washe gari umma tayi waya da Abba ya tambayi jikin baba tace yaji sauki nan yace zai sa mata kudi yanzu a kara saya ma baba kayan abinci da fruits haka tace sun gode haka ko yasa masu kudi dubu dari biyu aiko umma dubu hamsin ta ba ma baba tace Abba ya turo shikam baba yayi godiya sosai yaji dadi yace ta kira waya ya ma baba godiya tace ai basai tayi mashi godiya ba yana ƙasashen waje ba'a cika samun shi a waya ba idan ta samu sun yi waya zata mashi godiya tace toh..
Nan Abba ya turo mata mota ranar yace ta shirya ta koma gida, ko da ta shirya tsab sai ga driver ya iso.. haka ta sallame su mama tace masu zasu wuce kowa ya sallame ta har da kawar ta tabawa tazo sallaman ta tace mata zata turo mata da wasu kudi tasamu na shan ruwa tana kokari tace baki gajiya Aminiya? Tace haba kai baki gaji dani ba ni zan gaji dake? Tace toh yanzu dai idan kin koma gida kinyi aikin sai ki fada mun.. tace toh ba matsala duk yadda ake ciki zan kira ki, tace toh Allah ya kiyaye hanya.. ta fita waje ta shige mota sai bauchi..

Not edited as always

Please comment and vote

Let's meet in next chapter

Yours khads ❤️🦋🦋

JADWA (Completed)Donde viven las historias. Descúbrelo ahora