JADWA 3

259 17 1
                                    

Amma bari inje wurin jadwa yanzu ka jira ni anan. Kaji ? Sir fahad ya daga kai alamar Eh. Abba ya ka ma hanya da zai kashi parlour daga nan sai ya je dakin jadwa.

Isar shi dakin jadwa yayi sallam ta amsa ya shigo, ya mata baya ni jadwa kasa ce wa komai tayi, Abba yace jadwa tashi kije ki same shi kinji ? Fahad daga gani mutum kirki ne Kuma yayi abinda ya dace ke ma kinyi abinda ya dace kinga rashi tsayar da ba kiyi ba yasa ya biyo ki gida ya nemi izinin ki wannan ne zai tabbatar maki da gaske yake you kinji daughter tashi ki tafi. Toh Abba Amma... Amma mai ? Yi hakuri tashi kinji toh tace ta fara shiryawa shi kuma Abba ya bar dakin. Ya fito wa yayi kicibus da umma daman tunda ya bar guest room Kiran jadwa ta biyo shi domin jin abinda zai fada ma jadwa.

*** Umman yara ya dai ? A'a dai da arrr Alhaji kamar mun yi bako ko ? Sai ta fara kame kame uhmm eh haka ne bakon jadwa ne, Toh Alhaji daga ina, wai lecturer insu ne tooooh tayi ajiyar numfashi dame yazo Alhaji ? Ta tambaya kai tsaya Kuma Abba ya fada mata komai yace Allah ya Sanya Alkhair Amma a zuciya mugun kudirin ta na nan.

***Gama shiryawa tayi tasa hijab inta purple color iya gwiwa sai ta saka Black abaya aciki tayi kyau Amma bata yi wani kwalliya ba sai ta wuce zuwa guest room. Sallama tayi, sai ya dago kai ya amsa Amma mai.. nan take sallamar ta tokare mashi a makogora yasa karasa wa sai cewa kawai yake yi a zuciya tsakiya ya tabbata da ubangijin wannan halittar, karasawa kusa tayi a dai dai lokacin da kulawa mai aikin gidan ta iso da drinks da snacks ta yi sallama ta gaishe su ta aje ta tafi.

** Shi ko gogan sai kallon jadwa yake yi ba ko kibtawa, shiru yayi yawa can sai yace jadwa gaskiya kina da kyau domin yau ne nafara ganin wannan kyaukkyawar fuskar taki amma gaskia bantaba ganin halitta mai kyau irin haka gaskia tsarkira ya tabbata ga Allah ubangijin duka ka kyawawar halittu.
Nagode sir murmushi yayi suka bayyana hakoran sa. Sanna tace kaci abinda aka kawo maka sai yace toh amma kafin nan abban ya fada maki abunda ke tafe dani kuwa ? Eh ya fada mun Kuma kayi Abinda ya dace, hmm koh ? Eh saboda ba mutunci ga maccen da ta tsaya waje sauraren wani mutum, duk namijn da yasan darajan macce kamata yayi idan ya ganta a hanya ya ji yana son ta toh yayi kokarin neman gidan su Amma ba ya tareta a hanya suyi magana ba, toh jadwa Amma ni a a makarantar ku na tare ki ba a hanya ba, toh ai makarantar mu ba gidan mu bane ka ga tamkar a hanya nake. Amma yanzu gashi kayi Abinda ya dace..

**" Kina da gaskia jadwa ita ya mace mutumci ne da ita gaskia. Amma inaso na maki wata tambayan inajin ka sa, idan namiji ya ga macce a hanya Kuma yaji yana son ta toh kenam kar ya mata magana ? A'a sir ni bance ba ya mata sallama idan ta amsa shi sai ya nemi sanin gidan su ko karban numbern ta a gurguje ya nuna mata a hanya suke, idan ta amince wala ba'a sa. Idan kuma bazai iya tare ta ba to ya bita ya ga gidan su, toh naji wannan idan ba gidan su zata ba fa ? Hhh tayi dariya tace toh ai gidan da taje baza a rasa sanin ta ba sai ya aika yaro yasamu details inta 😁 shima dariya yayi yace malama jadwa kenam gaskiya kinyi tace koh ? Yace sosai ma tace nagode.

**Daga nan ya kara sheda mata shifa da gaske yake yi Kuma bada wasa ya zo ba auren ta zai InshaAllah, bata wani bashi matsala ba dun dama sir fahad yayi Mata kawai bai bi ta hayar da yadace ya same ta bane yasa ta wahalar dashi Kuma sai gashi abban ya yaba dashi sosai sai ta karbi soyayyar shi. Gogan yaji dadi sosai Kuma yayi farin ciki.

Anan sukayi yar fira kadan, sannan ya sheda mata afra ce ta bashi address inta, Kuma yana da number duk afra ta bashi, nan ya kira numbern ta, tace ta bar wayar ta a daki amma idan taje zata yi saving number. Nan suka yi sallam ta raka shi har bakin gate ya shiga motor sa ya wuce ita Kuma ta koma ciki

***A bangaren umma Kuma taso ta bita zuwa guest room dun taji zata amince da soyayyar sir fahad koko Amma ina Abba ya je ta zuwa daki yace yana da bukatar fira da ita dole umma tayi hakuri Amma tasan dole idan har ta amince da soyayyar shi ai zata ma sani ne sannan tasan kalar abun yi..

Shortest chappie y'all 🙈🙈 sorry your girl is kinda busy these days, but next chapter will be a longest chappie inshaAllah so stay tuned! ❤️

Xoxo Khadija loves you all

Please votes n comments your girl need itt n she will appreciate lots

#khadijaHarris
Follow me on WordPress pls
@khadsdotblog.wordpress.com

JADWA (Completed)Where stories live. Discover now