JADWA 13

73 3 2
                                    

Haka tuka koma gida da isar su ningi, gidan tabawa direct su ka wuce koda suka isa nan suka fara tunanin yadda zasu ɓullo ma lamarin. Sai umma tace Ni tabawa lokacin da boka ya diba mana yayi yawa duka ina zan samu wannan abubuwan na Alhaji cikin kwana hudu, gaskiya abun yayi yawa. Hmm gaskiya abunda wahala wlh, nan tabawa tace ai yanzu wannan aikin ya koma waje na kuma yanzu idan kika cigaba da bibiyar Alhaji Yusuf ai zai iya tunanin wani abu a kan ki tace haka ne wlh. Toh yanzu kai idan kinje ta ina zaki fara zan san ta inda zan fara kawai sauran canjin da ya rage mana cikin dubu goma ki bani zan shiga takalmin bazai yi wuya ba haraba masallaci da ke cikin Company zan je idan sun shiga sallah sai duk na kwashe masu takalmomin, zanyi shigar mahaukaciya ne daga nan kuma zan bincika inda yake zuwa aski ko kuma zan sa ido sosai nayi maki alƙawari In'sha'Allah cikin kwana uku ni zan hada komai ai ni jan wuya ce, nan suka bushe da dariya, umma tace Nagode ke kawar arziki ce In'sha'Allah idan abun nan ya tabbatar zaki ji dadi sosai.. tace ai dole toh da wannan shawara umma ta koma gida...

****

Washegari tabawa ta wuce bauchi haka yake tayi kuwa sai Allah ya bata sa'a taje Company kuma ta gasu Alhaji har ta nan aka kira sallah taga sun shiga Masallaci duka tabi ta koshe takalmomin su, kuma kamar yadda tace za tayi shigar mahaukaciya haka tayi, kuma hikimar shigar mahaukaciya da nayi saboda kar ayi suspecting komai da sace duka takalmomin da tayi saboda bata so ace na Alhaji ne kawai aka sace dole za'ayi zargi, amma tunda duka ta dauka kuma ta lura da na shi Alhaji shikenan idan tabi hanya zata yar da nasu ta cire mai amfani kuma sai da ta tabbatar da tayi shawagi ta wajen Company har sai da wasu ma'aikata suka kore ta amma taki, tare da kwalla saman kai.. kai!! Tabawa yar drama ce....

***

Da suka fito sallah babu takalmomin su kowa sai sake baki yake yi.. nan dai aka fara zargin wannan mahaukaciyar ne da aka ga ta dauki kwalla saman kai kuma ana ta korenta taki wuce, nan Alhaji Yusuf yace Allah sarki idan ita ce ai kar ku ga laifin ta, bata da lafiya ne mai lafiya ai bazai yi haka bah.. nan wani ma'aikaci yace wlh Alhaji itace ma saboda jar da kwalla saman kai take yawo ba mamaki nan ta zuba su shegiya Allah yasa ta zo gobe sai na zane ta tunda kora bai mata. Nan Alhaji yace ashh! Mai yayi zafi hafizu ai bai kai can ba dan Allah... Idan ma tazo gobe idan akwai yanda za'a taimaka mata ai idan tana magana sai ka haɗa ta da sani suyi magana bai kai a zane matar mutane ba bawai Allah baya san ta bane taga kanta cikin wannan hali koma da menene Allah yafi mu sanin daidai yanzu kowa ya bada size inshi kaje kasu ko sayo takalmi.

****
Nan hafizu ya karbi kudi da kuma sizes ya wuce yana tunani Alhaji a kanshi gaskiya da ace akwai mutane irin Alhaji Yusuf kamar 50 a Nigeria toh za'aji sauki, kirkin shi yayi yawa...

*** Ita a bangaren tabawa kuwa tayi nisa da wurin, sai ta canza kaya ta sa hijab har kasa sai taje wani shagon askin wai tana tambayen koh ina ne Company Alhaji Yusuf? Ita yar uwan shi ne ku yana zuwa nan aski? Yace mata ya san Alhaji Yusuf in Amma ya mata kwatacen Company yace mata baya zuwa aski nan kuma.. nan tabawa ta fara zuba dama tasan gashin Alhaji zai yi wuya kuma bata so ta ba wa umma kunya kuma boka baya magana biyu. Hmm sai ta kara gaba ta ga wani mai shagon aski shima sai taje zata tambaye shi..

Shortest chappie

Your author is sick pls if you come across this say a prayer.. JazakAllahu khair as you do so❤️❤️😢

Next chapter coming In'sha'Allah as soon as I recovered..
Not edited pls ignore mistakes.
Xoxo

JADWA (Completed)Where stories live. Discover now