JADWA 44

54 7 0
                                    

Yau sati daya da dawowan radiya daga ningi amma jikin umma sai gaba yake yi shi kuma adam ya dame da kira cewa yana so ya zo ya ganta su gana, ta ma mama magana tace ba matsala ya zo idan sun gana taga ya mata sunyi addu'a sai ya tura manyan shi wajen Abba a Bauchi tace toh ta Amince da haka.

Yau ya iso Bauchi ta tarbe shi yana zuwa taji hankalin ta ya kwanta da shi saboda yadda ta ganshi da natsuwa da kamala ga addini da tausayi ko da ta fada mashi tana jinyar umman ta hospital ba karamin damuwa yayi ba haka su kaje ya tausaya ma umman ta sosai yayi addu'a kuma ya bama radiya kudi masu yawa yace a kara cikin magani tayi godiya sosai ya koma gida ya sallami mama. Da zai koma radiya ta mashi izini da ya tura manyan shi wajen Abba ta amince Allah ya tabbatar da alkhairi ba ƙaramin dadi adam yaji ba kamar anyi mashi kyautar kujerar Makka..

Koda ya koma ya sanar da manyan shi Abba ya kira ta ya tambaye tace eh ita ta bashi iznin yayi murna sosai da ta fitar da miji yace shi kenan su je su dawo da shirin su, sunyi murna sosai yadda Abba ya tarbe su.

***
A bangaren su A'isha kuwa tun bayan da wani Alhaji ya kwashe su ya wuce da su akwa ibom suke ganin boni sai wahala suke yi kuma ya kafe su ya masu asiri suna son zuwa gida ba hali ko wayan da radiya ke yi da su a sace suke yi babu abunda yake yi dasu sai zina kuma tare yake yi dasu innalillahi wa'inna ilaihi raju'un kawai zamu ce duk a lokacin da zai sadu da su tare kuma ta annus yake yi abun babu dadin fadi, duk sunyi baki sun rame gashi babu wadatar abinci haka yake barin su da yunwa ko wajen da suke zaune wlh abun tausayi ne, A'isha duk ta shiga tashin hankali saboda yadda take mafarkin gida da kuma umman ta ma shi yafi damunta..

Abba ya kai magana wajen yan sanda yadda yayi alqawari dss sun fara bincike ranar da A'isha ta kunna waya aka yi trekking in layin ta aka ga location da sauran abubuwan da suke bukata.. haka suka fada ma Abba ya basu kudi suka zabi wa'inda zasu je akwai ibom don aje a wuto dasu..

Koda suka je anyi nasarar samun su don basu sha wahala ba sun bi map amma koda suka isa daidai location in basu taradda da Alhaji ba su so su ka mashi Fatima ta je daji samo ruwa tayi wanka don a gefen gari suke, basu yi 5minutes ba sai gata

Da farko sun tsoro sai da suka kira Abba suka sa handsfree sannan Abba ya masu magana cikin sanyi rai yace Ni ce na turo su kuyi hakuri ku dawo gida hakanan jin hakan suka fashe da kuka suka ce toh Abba.

Haka suka shiga hilux ko kayan su basu tsaya dauka ba dama kuma basu da wasu kayan arziki har suka gama suka bar wurin babu labarin Alhajin acikin mota babu mai ce ma kowa komai sun gaji da kuka har sun yi shiru don ba karamin tafiya suke yi ba.

Kuma jiki ya fi na kullum sai kuka take tana rokon yafiyar mutane ciki harda Abba don mama ta rike shi tace yazo Dan Allah haka ya zo da hidaya, hidaya ganin halin da umma take ciki ba karamin kuka tayi ba, zata fara fada mata abubuwan da ta mata hidaya ta rufe mata baki tace basai kin fada ba na yafe maki cikin kuka koda.

Radiya idon ta ya cika da hawaye ko adam ya kasan gane kanta a ranar, Abba sun koma bauchi da 30minutes haka aka kira su aka ce Allah ya yi ma umma cikawa babu shiri baban ya juya cikin tashin hankali ita kam hidaya harda zazzaɓi sai da ya kamata.

Amarya jadwa suna Saudi Arabia da angon ta suka ji wannan labarin ba karamin kuka jadwa tayi ba haka ango ya ta kwantar mata da hankali suka cigaba da mata addu'a a kasa mai tsarki.

A ranar radiya ba karamin dimau cewa tayi ba koda adam yayi kiran radiya yafi a kirga daga karshe mama ta yi karfi hali ta dauka ta fada mashi abunda ke faruwa..

Yaji abun sosai a ran shi yace ya mama gaisuwa ya kashe waya, a ranar radiya batayi bacci ba ga tunanin umman ta ga na yan uwan ta idan ta tuna cewa yanzu haka zasu dawo suji wannan labarin don Abba da yazo jana'iza ya fada masu cewa an gano inda su A'isha suke har an dauko su suna hanya..

Yadda ta ga rana haka ta ga dare ido duk sun kumbura mata da asuba adam ya kira ta ko da ya kira ta dauka da sallama, muryan ta ma baya ko fitowa amma yana jinta don ko banza radiya akwai sanyin muryan.

Haka yata mata nasiha yana jawo mata aya da hadisai Masha Allah take fada aranta ashe haka abokin rayuwar ta yake lallai tayi dace Alhamdulillah saboda ya kwanta mata da hankali sosai ya tuna mata da wasu abubuwa da ta manta harda wa'inda ma bata sani ba.

Tayi mashi godiya sosai suka yi sallama yace anjima zai zo kuma har da auntyn shi tace zata zo da kawun shi ba karamin nauyi taji ba amma har a ranta wlh taji dadi sosai kuma tace Allah ya kawo su lafiya.

Gari na kara waye wa mutane na kai kawo zuwa gaisuwa Abba haka yasa aka aiko da abinci iri iri daga bauchi ana ba ma mutane sada, jadwa ce ta kira ta tana mata gaisuwa kuma tana kara bata hakuri taji dadi sosai  harda mommyn su fahad da auntyn shi har da shi kanshi fahad in da su sultana da jidda sai da suka kira ta. Haka takara tabbatarwa a ranta lallai jadwa ta samun wajen zama Allah yasa a dore haka. Tayi masu godiya sosai.

It's been a long since I update and it's short chapter
Next one coming soon In'sha'Allah
Pls don't forget to vote and comment.

JADWA (Completed)Where stories live. Discover now