JADWA 12

73 3 0
                                    

A kwana a tashi ba wuya a wajen Allah. Yau sati biyu Alhaji Yusuf da iyalansa su dawo daga kasa mai tsaki, ita ko umma na shirin kara kwana biyu taje ta samu Alhaji da maganan ta dawo tayi nazarin sana'ar yi, sallah ko tuni ta daina yi kamar yadda boka ya bata umurni.

**

Shiga tayi ta sallama gidan tabawa ita ko lokacin ta shirin zuwa gidan yar ta da ke bakin kasuwa don ita ba ranar da bata zuwa gidan yar ta tana kisa mata kisisina iri iri. Tace yau kece a gidan shegiya mata wato mako biyu yayi kenan toh kinji labarin ya dawo ne ? Tace ina fah Ni dai ai nasan tunda ba nan zai tare dole ya dawo ko don kasuwanci shi amma nikam yau nake shirin shiga garin bauchi ko zan dace, sai tabawa tayi shiru kamar tana nazarin tace ya naji kunyi shiru? Hmm tace ai dole ina tunanin yadda zaki samu abubuwan da boka yace kisamo na Alhaji ne kamar zasuyi wuya amma nasan kudi basu yi wuya ba tunda shine ma ya maki alqawari.. sai umma tayi shiru tace nima ina tunanin haka wallahi amma In'sha'Allah bazai gagara ba zanyi kokari inta bibiyar shi har na samu abubuwan kamar yadda boka ya bukata. Tace toh Allah yasa suka hada baki suka ce Amin..

**
Bayan sallaman su ta wuce ta shirya sai Bauchi da isar ta, taje Company akace Alhaji yana gida bai zo ba yana huta saboda bai dade da ya dawo umrah ba. Tace toh ayi mata kwantancen gidan, mai aikacin da ke cikin Company Alhaji wanda take tambaya kamar bazai mata ba cen kuma sai ya mata.
Nan umma tace ta gane sosai haka ta nufi GRA kamar yadda aka fada mata gidan ta bi layin gidajen amma ko da ta isa ta tarar da mai gadi kwance tayi sallama ya amsa tace toh zo wajen mai gidan ne yace toh yana ciki yana hutawa sai dai ta dawo gobe, nan koh umma tasa kuka don Allah ya taimaka mata ta shiga daga kauyen ningi ta fito kuma taimako ta ke nema, hmm mai gadi yace mata umurni yake bi shikam sai dai tayi hakuri. Haka umma take ta rakube gefe guda shi ko mai gadi ya fita batun da tunda ya fada mata gaskiya. Kuma tace wlh yau ko kwana zanyi nan sai dai nayi ban iya koma wa Bauchi da bakin ciki tunda dai yana cikin gida ai ko matsalan cin da ke haɗa da gidan shi ya fito yayi Sallah. Da wannan tunanin umma ta ci gaba da zama. Haka rana ta kare mata kofar gidan shi ko mai gadi ko kallo bata ishe shi ba. Toh da yake da unguwar manya ne mind your business bata ganin kowa sai mota ke wuce wa ta gefen gidan gefi gefi kuma ba ruwan su da ita. Ko da yamma ta fara yi rana ya fadi umma yunwa sai kwakwalan ta yake yi tana zane ta ga mai gadi ya shiga ya fito da fried rice da naman kaza da su drinks umma sai hada yawu, hmm sai umma tayi rau rau da ido taso tace mashi ya sanmata ko da cikin marfin kula ne amma yanda taga ya hade rai sai ta kyale shi yana gamawa yaje ya mara alwala hmm umma sai ta fara tunanin gida tana ta roki Allah yasa Alhaji ya fito sallah. Yana gama alwala ya shiga Masallaci ya fara kiran sallah sai ga Mutane sun fara fito yin Sallah. Anan can sai ga umma ta ga fitowar Alhaji da sauri ya shige masallaci aiko nan umma ta fara washe haƙora tana jin dadi.

***

Ta fitowar Alhaji masallaci nan ta bishi tana Alhaji Alhaji Alhaji koda ya juyi ya ganta hmm yayi mamaki sosai ta fara mashi sannu da dawowa nan ta fara sheda mashi yanda tazo nan da kuma yanda suka yi da mai gadi, da iya awannin da tayi anan kofar gidan. Ya bata hakuri sosai yace ba laifin mai gadi bane shine ya bashi umurni saboda yana so ya samu bacci kuma idan ya biye ma mutane bazai yi bacci shiyasa tace bakomai ai ita yanzu tunda ta ganshi tayi farin ciki sosai da suka dawo lafiya nan yace mata ta shigo gida tana shiga ta fara kallon gidan irin kyaun gidan sai wanda ya gani nan kuma tafa imaging gashi ta zama matar gidan 😂 hmm Aiko ya hada da mai aiki ita da taga mai aiki ta dauka matar gidan ne yanda ta ganta cikin yanayi na jin dadi tsaf tsaf kamar mai aiki ba sai da yace ta kai ta dakin baki da dauko mata abinci taci sannan ta fara tunanin wannan mai aiki ne don yadda taji tana amsa mashi ta toh Alhaji angama..

** Haka mai aikin idan tayi kamar yadda ya umurta, koda aka ke umma dakin baki hmm wankagale Baki rayi wai wannan ne dakin baki lallai mai ko yaji dadin sa umma sai kuka da taga an koma mata abinci kala kala cikin kuloli na alfarma ita duk tunanin ta ina ma ace yau ita ce acikin wannan daulan.. hmm da ko sai tayi tsiyar iri iri.. nan umma ta fara cin abincin kamar wata manyen abinci..

** Shi ko Alhaji zuwa sama yayi ya je yayi ma hidaya labarin ta, hidaya taji tausayin ta sosai har da mata kuka sai Alhaji Yusuf ya jawo ta ya rungume abunshi yana bata hakuri.. yace su fito su kara gani ta haka suka sauko kasa koda suka isa daki baki da sallama hannu su rike da na juna.

*** A lokacin umma anyi balance anyi one one kamar dakin babanta, tana ganin Alhaji Yusuf da balaraba sai ta gamtsare, wannan wacece a ranta take fadan haka? Hmm sai nan hidaya ta gaishe ta anan.. ta amsa ta zuba mata gaisuwa da tambaya ya yara kamar wata sabuwar mai maula..
Anan Alhaji Yusuf ya fada ma umma wannan iyalin shi nan umma ta washe baki na ciki na ciki. Tana kara gaishe ta tana fadi wannan daga gani balaraba ce killan acan Makka ya samo ta.. hmm bata ra da mata lokacin Alhaji ya tambayi umma akan sana'ar da zata ta mashi karya iri iri ta na shinka take ta fara yi, anything rice dai zata sauro buhuhun nan shinka tana ba masu shago da masu da abinci dai haka. Nan aka yanke magana Alhaji yace bari a fara da kadan nan kuma tace mashi har da shago take so ta kama hmmm nan dai Alhaji yace duka zai bata dubu dari biyar ta fara da kadan a ganin, kuma ta so ya bata fita da haka amma ba yanda ta iya nan ta fara zuba mashi godiya da sa albarka bayan ya bata dubu dari biyar ya kawo dubu goma ya bata yace wannan ta rike a hannun sosai taji dadin kudin ta kara kudi ta kuma ma hidaya godiya sosai da haka dai Alhaji ya kirawo drivern shi yace ya maida ita ningi saboda dare yayi lokacin haka suka yi sallama ta wuce ta je ta shiga motar driver.

*** A ningi kuwa hankalin yaran umma ya tashi har gidan su tabawa sai da suka je amma shiru yabawa tace lallai tazo sunyi sallama amma In'sha'Allah su kwantar da hankalin su komai lafiya lau. A haka ta kwantar masu da hankali suka koma gida da isar su gida sai ga umma ta dawo nan suka je suka rungume ta suna tambayen ta meyasa ta dade ta fara basu labarin bata samu ganin shi bane sai da yamma ita kuma tace bazata dawo ba sai ta ganshi. Da haka tabawa ta shigo tace ke duk kin tayar ma mutane da hankali nan umma ta fara ba ma tabawa labari, tabawa tace dai mun dai kodai tunda an samu kuma kin dawo lafiya. Tace yanzu tabawa ki tafi da kudin gidan ki gobe sai mu shirya mu je wajen boka ai bata lokaci wai an daura ma kare aure.

Haka tabawa ta juya ta wuce da kudin, washe gari nayi suka fara shirin zuwa kauyen da boka yake. Haka ta kara sallaman yara ta bar masu kudi tace suyi abinci. Hmm haka suka karbi kudin. Da isar ta idan su tabawa sai suka fito tare sai suka samu mashin sai kauye. Suna isa kauyen suka fara tafi cikin daji kamar yadda suka sabo da isar su boka ya daka masu tasowa yace kun samo kudi kin daina sallah kin samo gashin kashin da takalmin shi ? Nan umma ta juya ta kalli tabawa ido cikin ido su har sun fara mantawa da abubuwan da boka yace a samo bayan kudi. Nan ya kara daga masu tsawa yace ku juya ku wuce na baku kwana hudu ko samo wa'innan abubuwan idan bahaka ba bani ba aikin ku bana son Ina daukon dogon lokaci a aiki..

Nan suka juya suka wuce suna tunani da kowa a kanshi

Not edited ignore mistakes pls
Don't forget to vote and comment

JADWA (Completed)Where stories live. Discover now