JADWA 1

1.9K 34 4
                                    

Sannu a hankali take tafiya a cikin makarantar su, iskan da ke kadawa kadan kadan yasa hijabin ta tashi, bata damu ba sai dai jan shi da take faman yin domin kar ya daga sosai duk da dai ya kasance babban ne har kasa amma tana shakkur hakan. Duk da ya kasan ce yanayi ne na zafi amma iskan na dan kadawa lokaci lokaci, saboda itatuwan da ke hanya da take bi, ita dai sauri ta ke tayi don ganin ta isa masallanci makarantar kafin a kira sallah domin son take ta Isa da wuri, ta samu sahun farko don bata wasa da sallah jadwa kenan..
Kiran sunan ta taji anayi, da alama kaman ta gane mai muryan sai sauri take tayi shi kuma bai daina kira ba.. jadwa! jadwa!! Jadwa!!! Sauri sauri, gudu gudu Amma ta ki tsayawa bata ankara sai taji afra kawarta ta tare, ta sha gaban ta. A'a afra meye haka ? Ke dallah mallam ja can baki ji ana Kiran ki bane ? Ni dake a nisa naji har nasha gaban ki amma ke kin kasa tsaya wa, me hakan yake nufi? Afra bani wuri Dan Allah in wuce masallanci sauri nake yi. Toooh sannu! Ta-sallah 😁 eh nadai ji bani wuri Dan Allah. Naji zan bak wuri Amma amsa mun meyasa kike wulaqanta bawan Allah kuma lecturer ackin makarantar nan jadwa ? Hakan baya daya daga cikin halinki ba faa. Hmm nasani afra amma duk wani magana yanzu munyi bayan na fito daga sallah kinji! Karaf sir fahad ya karbe maganan ya ce afra nagode da kokari, ki barta ta je tayi sallah. Daga afra har jadwa sunyi mamakin ganin shi. Sai dai jadwar ta basar kamar bata san da zuwan shi ba.. sai ta wuce, ita kuwa afra mamaki ta ke ko meyasa jadwa ke wulaqanta sir fahad oho, tsayayyen namiji mai kyau haka a kama wulaqanta shi, ina ma ace ita ya ke bibiya haka da wallahi sai ya ga so har sai ya kusan zaucewa, amma kullum yarinya sai faman lullube fuskar take da niqab da hijab kamar dodo.. mtwsww Wai ita nan mai kyau wawuya. Don taga sir fahad ba lecturer in department insu bane shiyasa take haka ai ko tsayawa tayi ta samu riba.. amm.. afra kin gane ko zan tafi masallaci yanzu nima please idan kin dawo daga masallaci meet me at my office please, I've something very important to talk with you, ke ma ki tafi kije kiyi sallahn koh, maganan da yayi ne ya dawo da afra daga duniyar tunanin da take yi game da jadwa. Okay toh sir insha Allah I'll do just ask you said... Sai ya jiya ya dau hanyan da zata sa dashi da masallacin maza, saboda masallacin maza dana mata ma ba daya bane toh koma daya ne na student daban yake dana lecture's...

******

Ita ko afra bayan wuce warta daga wurin magana ta dinga yi a fili.. Wai toh yau shi ina ruwan sa da sallahn na? Toh ni bana san sa ido ai bazan taba iya sallah a makarantar nan ba sai na koma gida domin bansan takura kai na cikin jama'a mtsww! Bara ma in Kira basma. Ciro waya tayi daga jakka ta kara a kunne can sai naji tana cewa ke yar gari, mutumin ki fa yau ya sake tsayar da jadwa amma ina wallahi bata tsaya ba Allah yaso ina hanya amma ina ya kasa tsayar da ita kin santa da jijjida kai da fifiko ina da ga nisa na fito computer science department naga abunda ke faru nayi sauri na sha gaban ta. Ke!! Dan Allah kibari.. hmm ya zan bari indai kara fada maki.. lallai ba wawuya irin jadwa cewar basma.. hmm katuwar wawuya ma.. ai ko gaskia yau nayi missing in school wallahi dama ina cikin school ma.. wallahi kinyi missing, toh ai kece ba kyason zuwa school kwanan nan... Hmm afra baza ki gane bane kinsan dai ina ji da Alhaji shiyasa kawai yau naga ya kamata in bashi kyaukkyauwar kulawa domin in samu yan canji kafin ya ware ya bar garin nan. Toh yayi shegiya.. yanzu ma bakin office inshi zan tafi domin yace wai inje insame shi akwai magana. Toooooh! Cewar basma sai da ta numfasa tace toh yayi duk yanda kukayi kya fada mun kinji. Toh ba matsala. Sai ta yanke wayar sauri sauri ta nufi wurin da zai sadata da office in sir fahad.. zuwan ta yayi dai dai da isowarsa. A!!! Barka da isowa sir ka dawo? Eh Afra sa'ad sale koh ? Eh sir, Ashe ban manta da full names in ki ba toh Bismillah shigo. Toh sir! Sai ya bar shiga ta bi bayan shi.. sanyi da ya ratsa sassan jikin ta tare da kamshin office in da ya gaure ka gaba daya taji ta cikin wani yanayi mara misaltuwa sosai. Sannu a hankali ya zauna wurin zaman sa, sannan ya nuna mata waje yace afra zauna mana ya mata nuni da wajen zaman baki... Tsab ta zauna ta na kare ma office in kallon amma fa ya tsaru.. lallai abun sai wanda ya gani office in ya dace da mai ilimi kamar sir fahad gaskia.. maganan da yayi ne ya katse mata tunanin ta...

JADWA (Completed)Where stories live. Discover now