JADWA 46

48 5 0
                                    

Abba yace jadwa na gidan mijin ta karu damu ta yafe maku sai A'isha tace Abba ina zamu ganta yace zata zo ai ku kwantar da hankalin ku...

Shiru yayi can ya fara masu nasiha ma shiga jiki dagana ya nuna masu cewa duk yadda za'a saka hanyar da bashi da kyau kayi kokarin kujewa kuma idan ka rike Allah da addinin ka tabbas duk wata ƙaddara zata zo maka da sauki, ya basu misali da radiya yace ciki daya kuka fito amma sai ta fita daban ku ta rike addinin ta kuma ta kokarin kuje ma duk wasu abubuwan da basu da kyau.. bayan da ya gama masu nasiha ya fara masu na samu da rashi daga bisa yace masu munyi babban rashi kuma haka Allah ya tsara kwana ya kare ba magani ya fada masu umma ta rasu, babu abunda suke furta wa sai innalillahi wa'inna ilaihi raju'un.. sai hawaye tabbas sun yu imani duk yadda abba yayi tunanin za su firgita da jin al'amarin sai imani ya shigo masu, mommy sai hawaye take yi don ita ma nasihar abba ya shige ta babu abunda bau dawo masu da shi har ciwon da mommy tayi sai da ya fada masu kuma yace umma ce sillar komai saboda ta fada kuma Alhamdullilah ta roke su yafiya kuma suma abunda yasa ya basu labari saboda su kara yin nadama..

Sosai sunyi nadama kuwa saboda ya nuna a idon su sai dai a gani a aikace, bayan sun gama kukan su abban ya basu waya yace suyi magana da radiya zai je ya kai mommy hospital.

Akan hanya su na zuwa hospital mommy take rokon Abba da ya bari su cigaba da zama nan Bauchi tunda radiya zata dawo idan kuma tayi aure shikenan suma Allah ya basu miji suyi aure. Ameen ya fada yace kamar tunanin mu daya ma Ni cewa nayi harda mama ta dawo nan Bauchi zan bata gida anan unguwar sannan zan sa mata masu kula da ita su kuma su A'isha zasu ci gaba da zama gidana idan a tsayar da ranar auren radiya shikenan sai tayi aure ta huta Suma da sun samu miji zan auran dasu duka..

Mommy tace Alhamdulillah naji dadin wannan decision in da ka yanke Masha Allah Allah ya kara maka lafiya da imani habibiy nah yace Ameen habibty..

Da haka suka kawo hospital, wannan time in ba hospital inshi yaje ba wani ya kai ta, ita kuma bata tambayi dalilin hakan ba, suna isa suka shiga direct wajen doctor duk ta ma doctor bayanin duk symptoms da take ji, ya kira nurse yace mata su je lab ayi mata test, sun je anyi mata..

Koda nurse ta kawo result doctor yayi murmushi yace Alhaji congratulations fahh abunda muka dade muna so yau Allah ya bamu sai Abba ya tashi da karfi yace mai kenan yace your wife is six weeks pregnant...

Abba sai da yayi sujood ya daugo yana hamdalah tabbas yaji dadi sosai ba ko kadan ma yau shine Allah ya yayi ma baiwa haka..

Mommy ko ji tayi kanta ya daure tace a ranta ciki fah ? Hmm Alhamdulillah Allah na gode maka ya zanyi da kunya jama'a, yata tayi aure idan ance ma yanzu haka jadwa na da ciki ai bazan ce a'a ba, sannan kuma yanzu ace nice da ciki ohhni Allah ban rena wannan kyautar ba Nagode..

Yanayin da Abba ya ganta ne yace lafiya ? Tace Alhamdulillah sai ya rike mata hannu yace kema kina jin irin yadda nake ji ashe zan sake ganin wannan ranar ashe kunne na zasu sake jin wannan ? Tace eh gashi yanzu kaji Alhamdulillah yace Masha Allah

Tayi kokarin boye damuwan ta ne amma tabbas tana cikin damu ya mutane zasu dube ta ?

Doctor yace tana da allura kumaa zata je pharmacy a bata magani Abba yace suje tare duk ta takura tace ya jira ta yace a'a, abban na biye da ita kamar yarinya duk shi ke wannan abun ita ke jin kunya..

Sun gama komai zasu koma gida cikin mota yake tambayar ko lafiya, don yaga yanayin ta ya chanza ? Ko ta na bukatar wani abu ne ?

Fada mashi tayi tace wlh ita duk kunya ya kama ta ace ita ke da ciki kuma yanzu yarta tayi aure idan itama ta samu ciki a ga uwa da ciki diya ma ciki?

SubhanAllah Abba yace yanzu da abunda zaki saka ma Allah kenan hidaya? Ina haka ya zama laifi a addini? Don yar tayi aure tayi ciki, ke ma kin samu ciki shine laifi? Duk ba sunan Manzo SAW muka raya ba.

Gaskiya ki chanza tunani, kin manta lokacin da kike rokon Allah ya sake baki ciki ki haihu, yanzu kin samu ki ce kunya ikon Allah shi Abba duk abun ya daure mashi kai, musamman yayi parking in mota yana mata nasiha cikin kwanciyar hankali.

Ta gamsu sosai kuma ta roki yafiyar Ubangiji nan take, nan yake ce mata jadwa na da ciki ne ban sani ba ? Tace a'a amma ai zata samu tunda tayi aure murmushi yayi yace toh Allah ya kawo mata ita ma sai ya kalle ta yayi murmushi sai ta rufe ido, shi dai Allah ya sani kullum son hidaya sabo yake kara zama mashi, sai yace yanzu me kike so ne? Tace pizza take so taci yace an gama hajiyata sai tayi murmushi yace pizza kawai tace eh. Aran shi yana tunanin wani gift zai bata.

Koda suka koma gida haka suka ga su A'isha rakube kamar basu taba zama gidan ba, nan Abba yayi waya yace ma mama albishiri yace mata zata bar ningi da zama gaba-daya tunda baba ne kuma ya rasu toh su A'isha zasu tsaya nan gidan shi su koma makarantar, radiya kuma zai tsayar da ranar auren ta tare da yan uwan mijin ta.

Mama taji dadi amma kuma ita Allah ya sani bata son barin ningi. Bata nuna mashi ba tayi godiya sosai. Tana kashe waya take fada ma radiya abunda Abba yace radiya ba karamin dadi taji ba nan ta fara rarrashin mama tace ta amince don Allah.

Tace toh yana iya ai baza a maka kyauta kace baka so ba.  A duniya ba taba ganin mai hali na gari irin Abba ba gaskiya Allah ya bashi aljanna ya jikan iyayen sa kawai amma ya cika ɗa nagari ya iya mayar da alkhairi akan sharri. Ameen radiya ta fada.

Sati biyu da rasuwar umma, Abba ya aiko da mota yace a kwaso su, ya hana su A'isha zuwa ningi yace su yi hakuri su mama zasu dawo nan ai haka suka yi hakuri ko. Kuma suma a ran su sunji dadi mai zasu je yi ningi tunda ba umma. Sai dai don mama da radiya tunda zata dawo kuma ai shikenan.

Ma'assalama ❤️

Next chapter coming soon In'sha'Allah

Pls vote and comment

JADWA (Completed)Where stories live. Discover now