JADWA 39

55 5 0
                                    

Karan wake take ji tana daga cikin toilet amam ba hakin fito aranta tace cewa yanzu haka Dr sweet ne inda na fito na kira back haka ta fada aranta ta cigaba da wanka, adaidai lokacin da wani kiran wata ya kara shigowa lokacin ne radiya ta shigo sauƙin da sallama bayan ta dawo wajen mommy. Sauri tayi ta dauki wayan yana dab da yanke wa ta kara a kunnin ta tayi sallama yaji ya gane muryan ta yace sis radiya kin iso ya hanya tace Alhamdulillah ya jikin umma tace lafiya lau da sauki yaya ango sai yayi dariya yace harda ke koh ? Sai tayi shiru ta murmushi kaman yana kusa da ita, yace ina amaryan gidan ku take ? Tace ta shiga wanka tana toilet sai yace toh yayi kyau hakan ai suka yi sallama ta aje wayan ko 1mints bata yi da aje wayan ba sai ga jadwa ta fito toilet radiya tace yaya ango har ya matsu sai da yaki wayar ta fada tana dariya jadwar dariya itama tayi tace lallai kam ya matsu tunda har ya ta kira ba daya ba ba biyu bari na shiryar sai na kira shi muyi waya kafin na zauna a fara mun lalle kuma gashi ina so naje saloon duk a yau ? Sai radiya tace wlh wannan abun da ya faru haka don bana nan ne da na matsu maki munje da wuri ace gobe daurin aure sai yau zaki lalle da gyaran kai duk a yau ? Hmm radiya toh ya zan yi ? Ni ma nasan don baki nan ne Ni yadda zan je wajen saloon na kadai ne nake jin wahala gwara ma mai lalle ita zata zo nan su Aunty zainab ma sunyi rata kilan ma yanzu tazo har ta fara masu toh yanzu abunda zamuyi idan kin shirya wajen mai saloon za mu fara zuwa daga nan idan mun dawo ayi lalle tace hakane kam toh bari na shirya sharp sharp.

Tana gama fadan haka ta dauka silk boubou material in ta sa wani Black color ta shafa mai a jikin ta fashe ko ina da turare. Duk radiya na zauna tana jiranta hatta da abinci da aka kawo mata bata ci ba sai da ta tsaya jiran jadwa da ta gama suka ci jadwa bata ci wani abinci ba tace ta koshi, radiya ta fara matsa mata amma ina ta ki sai ta je ta zauna gefen gado ta kira angon ta suna ta wayan su ita radiya taci abinci ma ishi tayi hamdallah ta sha ruwa bayan da suka gama ta ture hijab in dawo har kasa ta dauki niqab da wayar ta sai key in motar mommy don dashi zata fita. Ita ma radiya ta sa nata hijabi in Amma bai kai dogo har kasa ba.

Suna fita wajen gida aka kama ma jadwa shiri amarya amarya kamar ta bude kasa ta shige kan kunya duk taji wani iri rufe fuska suna ta dariya, Aunty ta ganin don bata ga mommy ba kawai tace mata zasu wuce wajen saloon koda mommy ta tambaye ta toh adawo lafiya amarya tace In'sha'Allah tayi sauri ta wuce parking space ta bude mota radiya ta shiga sai tayi reversing tayi horn aka bude gate sa suka bar gidan.

Koda suka isa haka aka fara gyara mata gashin ta abunka na masu gashi ya kara tsawo sai sheki yake yi Masha Allah ita kanta mai saloon in sai da tayi santin gashin ta, harda radiya aka gyara ma wa itama ba laifi tana da nata gashin bakin gwargwado. Ana gama wa suka bata kudin ta suka shiga mota sai gida. Sun dawo lokacin yamma ya fara yi taso a bar lalle sai gobe amma Aunty zainab tace ba zai yiyu ba gobe daurin aure gaskiya kam ta zo a mata shi cikin daren nan tunda akwai wuta ko ina. Haka ko tayi sallah aka fara ma radiya da aka gama aka je kan amarya... Ana cikin yi ango ya kira radiya ne ta dauki wayan ta sa mata a kunne fada mata yake yi bakin su sun fara sauka bauchi kuka hotel in da ke cikin GRA aka yi masu booking amma shi sai da safe zasu taso da jirgi shi da daddyn shi da friends in shi tace toh ba matsala sai tace ana mata lalle ne nan ya fara santi yace yaso gani tace kar ya samu In'sha'Allah karma ya gama gani ma..

Sunyi sallama cikin wasa da dariya da kuma kaunar juna can ya kashe waya ya turo mata da kudi masu yawa tayi mamaki da ta gani ta kira numbern shi bai je ba sai ta kira Aunty tace tazo garden inda ake mata lalle. Cikin minti 5 sai ga Aunty zainab ko da ta zo ta fada mata cewa baki yan adawa sun fara zuwa suna hotel, Aunty zainab tace toh bari a aika da abinci jadwa tace toh Aunty ta juya ta wuce ta bi hanya da zai kai ta kitchen.

Angama lalle yayi kyau amarya ta fito wata yan India abun ta sai haske da wàrkiya da wani sheki ta ke yi Tabarakallah sai wanda ya gani kam...  Ko sai fadan yake yi tayi kyau. Amma ita kam duk ta gaji haka ta tashi ta wuce daki radiya ta taimaka mata, suna isa daki ta cire ka kaya zata yi wanka sai ga kiran Dr fahad, haka ta dauka cikin raunannar murya yana jin murya ya fara tambayen ta lafiya tace lafiya lau Dr sweet wlh nagaji ne yace sorry my queen tace naji naga missed inki muna magana da da ne I'm sorry for not picking at that moment sai tace ba matsala dama i naga credit alert ne shine nake tambaya yace c'mon naki ne Mana na Kara maki kudin lalle da na saloon ne fa. Sai tayi dariya tace Nagode sosai Dr sweet...

Kwanta tayi ko abinci bata iya ci ba saboda gajiya da kwanta tana cewa kin bacci kamar ance ta farka sai ta farka taji gaban ta na fadu sai tunanin yadda zata bar gidan su gobe take ta koma rayuwa da wasu family in sai naji abun kamar a mafarki wai ita ce gobe za'a daura ma aure toh kuka zata yi ko murna ta rasa abun yi kawai tayi tagumi ta cigaba da tunani ta dauki kamar minti biyar tana wannan tunanin can, ta tashi ta je tayi alwala ta fara sallah.. ta idar ta cigaba da rokon Allah da ya basu zaman lafiya mai daure wa tare da zuriya dayyaba ta kuka ta rasa kukan mai takeyi cikin bacci radiya ta farkon da sautin kukan a hankali take yin shi ma bai hana ya ta da radiya ba ko da radiya ta farka kamar an fada mata labarin komai, kasa magana jadwa tayi radiya tace basai ma kin ce komai ba jadwa I know how you're feeling now Kuma kin kyauta da kika fada ma Allah damuwan ki kuma In'sha'Allah zaki dace a gidan mijin ki ki godema Allah Dr fahad da sauran dangin shi duk suna san ki toh Alhamdulillah kuma a gida irin na su Dr fahad In'sha'Allah babu abun zaki nema ki rasa, haka radiya ta ta fada mata maganganun da suka sanya mata zuciya take jadwa ta rungume ta tace hakika ke ya uwa ce ta gari na gode ma Allah da samun ki kuma na dauki duka maganganun ki Allah yasa mu dace radiya tace Amin ita ma take nan yan uwan ta suka fado mata rai sai ta dauki waya acikin dare ta kira numbern amma duka a kashe, wuce wa toilet tayi tayi alwala ta fara sallah don ita ma take nata matsala wajen Allah ya yaye mata.. jadwa ko baccin ta ta koma tana jin wani sanyi a cikin zuciyar ta..

Yau juma'a kuma yau ne za'a daura auren jadwa da fahad, tun karfe 7 jadwa ta tashi daga bacci tayi wanka Aunty zainab ta kawo mata kayan ta masu kyau bridal lace fari ta sa da mayafi fari sai sakar ta mai kyau kuma mai tawada bayan ta shirya tsaf aka bata breakfast tea kawai ta iya sha aka fara pictures da yan uwa da abokan arziki. Sosai sunyi kyau harda hidaya uwar amarya ba ƙaramin kyau tayi ba Abba ya shigo shima ya shirya zai je airport tarbon baki, haka ya tsaya akayi pictures in da shi jadwa na ganin shi idon ta ya chanza zata fara kuka kenan ya jawo ta yayi hugging inta Yana rarrashin ta ya mika mata tissue sai ta goge fuska dama bata yi makeup so babu abunda ya samu fuskanta kukan da tayi ma glowing ya Kara ma face in.. kowa abun ya taba bashi Musamman hidaya da taso ta daure amma ina ita ma sai da tayi hawaye abbada ya lura da ita ma akwai sai ya bar wurin ya wuce ya shiga mota..

Bayan sun gama pictures in aunty zainab ta kara kawo mata wasu kaya lafaya ce mai kyau ja da ta sa shi ba ƙaramin kyau tayi ba adaidai lokacin angonta ya kira yace amarya ta manta da ango dariya tayi tace wlh a'a ban isa ba ai yace ga mu nan airport jirgin mu zai tashi In'sha'Allah. Tace toh Allah ya htsare ya ka wo ku lafiya yace Ameen.

Basu dade sai ga shi sun sauka Abba yasa anyi masu tarɓo na musamman shima Alhaji Ibrahim da yaga Abba da friends inshi sun zo airport suna jiran su ba ƙaramin dadi yaji ba sai ma da suka sauka hotel yaga irin karramawar da Abba ya masu irin yadda aka hada abinci da abun sha launi launi lallai ya kara tabbatar da cewa fahad gidan mutum ci ya dauko mata kuwa... Lokacin sai tafiya yake yi ana maganar karfe daya haka aka suka fara shiri bayan da suka huta kuma suka ci abinci aka wuce masallaci juma'a na sauko wa masallaci ana aka daura auren jadwa Yusuf da Fahad ibrahim Rashid daurin auren da ya tare manya mutane da sauran jama'an gari masu yawa..

Ana gama wa Abba yace ya haɗa walima anan gidan gonar shi inda aka gyara wurin aka ƙayata shi haka suka karbi tayi ciki ko harda ango da abokanan sa aka wuce sai gidan gonar Abba domin halartar waliman

Ma'assalama 🦋❤️
Unedited..
Let's meet in next chapter In'sha'Allah
Yours khads ❤️🦋

JADWA (Completed)Onde histórias criam vida. Descubra agora