JADWA 29

74 4 2
                                    

Koda jadwa ta iddar da sallah ta kira Mallam Kabiru yazo ya kai ta gida. Ba tare da bata lokaci sai ga shi ya iso ta shiga mota sai gida.

Tana isa gida ta hadu da umma zaune tana waya a kofar parlour ta gaishe, bata amsa ba ta cigaba da wayan ta, ita jadwa ta mike ta wuce dakin ta. Tayi wanka ta je sitting room inta, ta duba lantana ta aje mata abinci rice and stew ne sai fish sauce gefe haka ta dauko ta fara ci da Bismillah bayan ta gama sai tunanin Dr fahad ya fado mata rai. Tana kokarin kiran aunty zainab kenan sai ga kiran shi ya shigo dauka tayi yace "Assalamu alaikum queen yakike ya gajiyan school" ta amsa wa'alaikumus salam Dr ina lafiya lau gajiya kuma Alhamdulillah ya bi jiki yace " toh Masha Allah yasu umma da Abba ya kowa da kowa? Alhamdulillah ta kara fada kai tsaye yace toh Masha Allah zuciya ta cike take da kewar ki ta tare muradin son ganin ki jin nake yi kamar na zo yanzu hmm ka koma school ne A'a nima da na gama abunda na ke yi a waje sai na wuce gida kawai.. yau ina so muyi fira sosai idan nazo ina so naji ko kin amince dani sannan zan baki labari da kyau ko kuma duk wani abunda kike so kiji nawa zan fada maki In'sha'Allah nima zaki fada mani naki koh ? tace eh In'sha'Allah Dr Allah ya kaimu nima nayi kew.... Sai ta kasa karasawa kamar tana kusa da shi yace fada mana sai ta rufe ido yace kinyi kewa na koh sai tace eh cikin murya siririya.. sai ya kyalkyace da dariya yace toh ko nazo bayan magrib ne sai nayi isha'i yi a gida tunda naga akwai masallaci kofar gida ? Eh sai kazo Allah ya kai mu yace toh Masha Allah In'sha'Allah zan zo tace toh Alright sai dai anjima zanyi wani aiki yanzu yace ok bye sai ta ka kashe waya.

Kiran aunty zainab tayi a waya ta fada mata duk abunda da umma tace akan kar ta fara ta amince da Dr fahad ita aunty zainab tace ba dai kinyi istihara ba toh idan kinji kina son dr Fahad yau idan ya zo ki amince mashi ba abinda da isa tayi idan taga baki aure shi dama can ba mijin ki bane sannan ki bari ni da kaina zan kira sistern mommyn na fada masu wannan ai abun arziki ne.. jadwa taji dadi yadda aunty zainab ta kara mata karin gwiwa sosai kuma tace ita zata amince dashi ne don a wannan karon ta cire tsoron umma a ran ta.

Ana gama magrib sai ga afra ta zo wai ita tazo jin ko jadwa ta amince jadwa ce mata tayi sai tayi istihara tukun zuwa yanzu jadwa ta fara gane manufar afra saboda ta fahimci duk wani abun da take fada mata tana kwashe ta fada masu A'isha, ita koh afra taso tayi fira sosai da jadwa don ta samu labarin soyayyar na su amma sam bata bata fuska ka haka afra ta tashi suku suku ta bar gidan.

Ta iddar da sallah magrib ta sake yin wanka sosai feshe jikin da turare mai dadi ta kara da humra tasa abaya baki tayi rolling da gyalen abayan ta zauna kusa da mirror tana kallon kanta tana murmushi tace FatabarakAllahu ahsanul haliqeen.. lallai Allah yayi halitta ina da kyau Alhamdulillah Nagode Allah ka dawo mun da mommy mu cigaba da rayuwa da ita nayi kewar ta sai hawaye ya biyo fuskar ta sai ta goge da tafukar hannun ta.
Wayen ta na wajen charging taji Yana kara Dr fahad ne ya kira dauka tayi sai tayi sallama kamar kullum sai  ya amsa yace "my queen my babylast gani nan zuwa fa zan iya zuwa"? Murmushi tayi tace duk ni ka ɗai wa'innan sunayen yace eh akwai wasu ma da zan fara kiran ki dasu nan gaba tace Nagode zaka iya zuwa nima na shirya ke nake jira yace Masha Allah abun yayi daidai kenan, nima gani nan zuwa yanzu tace toh a iso lafiya yace toh yayi.

***
7:30pm dot ya iso kofar gidan, mai gadi ya bude mashi su ka gaisa ya shiga ciki, parking space yaje ya aje mota, bai fito ba sai ya kira jadwa a waya tace ba matsala yazo guest room zata shigo yanzu. Kiran Abba tayi a waya ta fada mashi cewa zata je guest room dr Fahad yazo yau, yace ba matsa shima zai dawo gida yanzu tace toh Abba adawo lafiya yace In'sha'Allah jadwa.

Babu bata lokaci ta wuce kai tsaye guest room tayi sallama amsawa yayi cikin murya mai dadin ji sai tayi murmushi ta shiga tana gani shi sai ta tsaya tsaye chak! Bakaken shadda yasa da kulla kube baki sajen da ke kan fuskan shi yana kwanta luf Masha Allah kawai take fada shi ma yabo kyaunta yayi sosai daga halittar da Allah yayi mata na surur jikin ta har na fuska kamar ita tayi ma kanta yace Tsaki ya tabbatar ga Ubangiji wannan halittar duk a tunanin a zuciya ya fada ashe a fili ne. Ameen ta fada tace Dr kayi kyau sai ta rufe fuska yace ai kin fini tace ko tana ta tafiya har ta iso kusa da shi ta zauna. Yace eh mana dariya suka yi duka sannan shima ya zauna kiran lantana tayi a waya tace tazo guest room da snacks da lemon juice tayi bako, tana gama wayan yace ki sake kiran ta kice bakon ya gode sai ta tsaya tana kallon shi ido cikin ido tabe baki tayi kamar ƙaramar yarinya, idon ta k
ƙasa ƙasa tace meyasa ? kallon ta yake yi shi shagwaɓar ce ya bashi dariya daurewa yayi yace haba kar kiyi kuka my baby plss toh tazo zan sha idan hakan zai faranta maki rai sai tayi murmushi nan taƙe tace eh zanji dadi gaskiya idan ka sha kuma ka ci snacks in yace toh shikenan angama ran ki ya dade sai tayi murmushi mai sauti tana kallon shi..

JADWA (Completed)Nơi câu chuyện tồn tại. Hãy khám phá bây giờ