JADWA 16

55 6 0
                                    

Bayan kwana biyu da Alhaji Yusuf ya fita batun umma ranar yana bacci sai yaji kamar an tashe shi koda ya tashi da tunanin abun ya dawo mashi sabuwa ya dauko waya misalin ƙarfe 3 na dare ya dare kiran numbern umma switch off aranar bai samu bacci ba ita dai hidaya tana kusa dashi sai sharan baccin ta take yi amma shiko sai juya juye ya rasa mai ke masa dadi shi dai burin shi yaji muryan umma ko zai ji sauki ita ko wayan ta akashe haka ya kwana raye, ya matsu gari ya waye yaje ningi aiko tunda asuba da gama sallah asuba ya gama hanya sai ningi wannan karan babu wanda ya fada ma wa, koda hidaya ta farko tayi sallah asuba ta ta jiran shi ya dawo ta gaishe shi kamar yadda ta saba amma shiru har gari ya waye nan hankalin ta ya fara tashi ai ko ba shiri ta dauki wayan ta kira shi kira daya biyu ya dauka yace tayi hakuri kiran gaggawa ne ya taso wlh, zasu yi taro da manyan yan kasuwa da kuma wasu turawa da suka sauka daren jiya, nan hidaya tace Allah ya tsare ya bada sa'a tayi mashi addu'a sosai.. tace har hankali ta ya tashi amma yanzu taji sauki yace ba komai ta mashi addu'a. Tace tanayi sai dai ta kara hmmm abunda Alhaji Yusuf bai taba yi ba kenan ya ya fara boko nace ai ba banza ba..

***

Koda ya isa ningi har kofar gida ya tsaya da mota, nan aisha fito dubawa ta ga ko wanene yazo masu kofar gida da safe, ai tana lekawa ta koma gida ta fada ma umma lokacin umma na bacci ba shiri umma ta tashi ta shirya ta wanke fuska ta, sallama ya tsaya yana yi kofar gida umma ta amsa tace ya shigo, koda ya iso sa tace tayi mamakin ganin shi, nan ya bata hakuri yace shi haka kawai yaji kamar ya fasa lamarin sai jiya yaji ya kasa sukuri wlh shi yau bazai wuce ba sai yaga ma su mama da baba watau iyayen ta kenan sannan koda zai koma bauchi sai turo ai nema masu auren ta ayi komai a gama, nan umma ta fara murmushi lallai boka yayi aiki a ranta, tace ai bata yi wasa da boka ba dole ko auren akayi ta samu da rika kai mashi wani abu yana magani akai akai saboda tsaro. Cikin wannan tunanin tace Alhaji ko dai makiya kwai su shiga tsakanin mu yace ko dai sune Allah ya fisu yanzu kam na dawo da yardan Allah.
Nan tace bari ta sayo koko a dama mashi yace a'a ta dai tambaya mashi ko zai iya zuwa yaga su mama. Nan ta tura aisha, ai ko da A'ishah taje mama tace yau wai ina aka taba yin aure saman wani aure ni fadima? Duk da dai auren nan ba'a san inda mahaifinsu yake ba ai kamata yayi ace taje kotu an raba aure ko da watarana ya dawo ashe mashi kotu ta raba aure kuma ita tayi wani aure, mahaifin umma ta fito wa daga bayi yace tabbas haka ne, yanzu ita mai umma tace wai mai neman ta ne yazo yana so yazo ya gaishe mu kuma da maganar aure yazo, yace toh madallah yazo ai ba matsala Ni nasan mai zan fada mashi..

**
Shiko Alhaji Yusuf koma yayi cikin mota yana tunani toh shi gashi ya wutau a gaggauce ko wani kudin kirki bai wutau da shi ba infact ma ba kudi ya jiki shi kuma kudin da ya duba cikin mota kadan ne baza su wuce 70k hmm haka yace ma umma ko da ta fito yana fada mata yace yana so ya ba ma su mama da baba ko nacin gora ne amma gashi yayi fitowar gaggawa kudin dake cikin motar shi baza su wuce 70k, hmm umma tace ai ba matsala kar ya damu yace toh shikenan zai basu wannan hakan nan in tace toh yayi..
Suna cikin magana sai ga A'isha ta dawo haka ta fada ma umma sakon su mama, nan koh umma tace oya ta shiga mota ta kai shi gidan haka koh ya shiga, so lokacin ne Alhaji Yusuf ya kalli kayan da ke jikin shi fara jallabiya ce sai kulla irin ta Saudiya, hmm kawai yace amma yaso yace yasa manyan kaya irin da malam bahaushe.

***
Da isar su yace ma A'isha ta je ta nemi izinin ko zai iya shigowa nan ko taje ta fada sai mama ta shimfida ta barma tace ace ya shigo, da sallama ya shigo ya zube kasa yana gaida mama da baba, nan suka fara hausawa sai ya fara gabatar mashi da kanshi, ko shi wane ne, tabbas bana yayi mamaki don yana jin labarin Alhaji Yusuf sosai a labarain gidan radio ashe zai ganshi har yazo neman hada zuri'a dashi Ni Wannan yar umma inata hadu da mutumin kirki haka ? Duk wannan maganar da yayi tunanin shi a azuciya yayi nan ko a fili yayi. Alhaji Yusuf yace wannan ai ba komai bane Alhaji tabbas nine kuma kasan haka Allah ke lamarin sa. Ina yar ka kuma da aure kuma nayi alqawarin zan rike mata yaran ta mata zasu yi karatu kamar yayana. Baba yaji dadi sosai sannan ya mashi bayanin auren da tayi na farko, yace yana so taje kotu a raba auren tukkun kafin ace za'ayi wannan. Alhaji Yusuf yace ba matsa kuma yayi alƙawarin zai ba ta kudin da za'ayi komai a gama, dagana bana yace ai babu wanda zai ki haɗa zuri'a da kai wlh.. nan Alhaji Yusuf ya kama murna irin yabon da baba ke mashi. Nan ya fito duka kudin 70k ya basu yace aci gora ayi hakuri ba haka naso ba, bana yace bazai karba ba yayi yawa Alhaji Yusuf yace mashi babu komai wannan kadan ne ma yayi hakuri da shi da kyar da baba ya karba, duk wannan abun da akayi agaban mama ne da A'isha...
Haka suka yi sallama suka wuce shi kuma baba yaji dadi sosai da yadda yar shi ta samu miji nagari kuma inda zata huta, ya kuma jinjina irin kudin da ya bashi.

JADWA (Completed)Where stories live. Discover now