JADWA 18

59 3 0
                                    

Da isar Alhaji Yusuf gida haka ya kira ma'aikacin shi aka yi maganar makarantar islamiyar su A'isha da Fatima da radiya duka kuma anan jadwa take yi ita ma.. yazo angama komai ya saya masu uniform yasa a Kai su ayi masu register, anyi komai angama gobe zasu fara zuwa Ita kuwa radiya sai murna take yi amma su o'o sai haushi ake ji su basa son zuwa ko ina sai dai aci a kwanta ansamu abunda ake so ba aikin fari bare na baki.

Washe gari Umma ta roki Alhaji kudi wai tana so ta taimaka ba tabawa ne ginin gidan ta ya zube nan ko karya take yi so take yi ta bama tabawa kudin da tace tana so akai ma boka taya murna, dayake Alhaji ya san tabawa kuma yasan Aminiyar umma ce haka ya tausaya mata ya bata dubu dari biyar yace ta bata ta kara, umma tayi godiya sosai tace zata ba ma tabawa yace ai ba komai an zama daya.

Bayan ya fita yace masallacin kofar gidan shi, umma ta samu damar kiran tabawa a waya ta fada mata yadda aka yi ta samu kudi, tabawa ta kama dariya tace naji dadin karyan da kika yi gobe zan zo nayi mashi godiya sai ki bani kudin ina kai ma boka tace mata toh Allah ya kai mu. Tace zata ma kara mata dubu ɗari biyu, ta kara ita don tana kokari kuma wannan dubu dari biyu in da ta bata cikin kudaden da aka wankin Alhaji na biki ne.

Kamar yadda tabawa tace zata zo haka ko tazo ta samu Alhaji suna fira da umma sun gaisa sai zuba godiya take yi yace don Allah ta daina ya an zama daya.. haka tace toh ina yara aka ce mata yara suna makarantar tace aiko hakan yayi kyau.. su kuma su A'isha a islamiyar basa fahimtar komai sai dai radiya tana mai da hankali sosai.
Haka tabawa ta karbi kudi ta koma ningi.

***
A kwana a tashi ba wuya yau umma sun yi sati da aure da Alhaji Yusuf shi kuma yau ya koma Company ya fara aiki... Yayi maganar makarantar bokon su A'isha kuma makarantar ne mai kyau mai tsada wanda ake ji dashi cikin gari bauchi yaran manya ke ciki harta da jadwa nan take yi shi dai da yake Alhaji Yusuf baya tuna bambancin kamar yadda ya dauki alqawari duk kulawar da zai ba ma yaran umma haka zai ba ma jadwa zai rike su amana. Haka ake kai su aka yi masu registration ace zasu fara zuwa sati mai zuwa duk kan su an kai su aijin da yayi daidai dasu.. sai murna suke yi su A'isha an saka su makaranta masu kudi shikenan sun zama yaran manya su ma..

***
Labarin mommyn jadwa.. alhamdulillah sun isa tanzania lafiya lau yan uwa da abokanan arziki anyi murnan ganin su, da taso ta zauna a gidan da Abban jadwa ya saya masu sai dai taga tafi bukatar zama kusa da yan uwan ta tunda daga ita sai jadwa suka zo.. sun yi waya da shi kuma kullum suna waya ta she da mashi cewa ita kan baza zauna gidan su sai zauna family house insu, yace mata ba komai tayi yadda take so. Jadwa kuma dama ake makarantar islamiyar da take zuwa a Tanzania lesson Kuma akwai uncle ta da yake yi mata lesson kanin hidaya ne..

***
Boka yayi murna sosai kuma da ganin kudin da tabawa ta kawo mashi haka ya ba ma yadda wani turare da garin magani yace take ma umma ta rika shafa turaren a jiki kullum sannan idan zai ci abinci ta rika barbada mashi maganin mallaka ne.. tabawa tayi murna sosai kuma tayi godiya ba iyaka.

Tayi ma umma waya ta fada mata yadda suka yi da boka murna wajen kuma kamar me. Tabawa tace ma umma idan har ta samu lokaci zata zo ta aiko mata da shi.. tace toh sai ta ganta..

***
A kwana a tashi ba wuya a wajen Allah ya sunyi wata daya da sati daya kullum sai zuba soyayyar yake yi da umma ita kuma bata wasa wajen zuba mashi maganin da boka ya bata, mommyn jadwa dai yana kokari kiran ta sau biyu a rana amma ya koma yin sau daya watarana na baya kira idan ta zo ta kira shi sai yace mata aiki ne aiki ne nan ko babu wani aiki akwai maganin boka ne yake aiki don umma sai abunda da tace ma Alhaji Yusuf har jikin shi rawa yake yi yayi mata abu ita da yaran ta.. hidaya tana damu sosai kuma suna waya da zainab tana bata shawarwarin da ya dace yan uwan ta ma sun san halin da take ciki suma suna ɗebe mata kewa kuma suna Bara shawarwari kamar yadda zainab ke bata..

Haka rayuwa taci gama da tafiya umma ta matsu kullum hidaya ta dawo ta fara aiki a kanta dun yadda ta saba da Alhaji kuma tana kwasan kudi ita da yaran ta da tabawa tabbas baza taso tayi tarayya da ko wata mata ba.. amma fa tana yi na munafurci kullum sai ta tambaye Alhaji Yusuf yasu hidaya da jadwa kai rannan har karban numbern ta tayi ta kira gaban Alhaji suka gaisa. Ranar da ta cika wata biyu tace ma Alhaji tana so idan weekend yayi zasu shiga ningi ita da yara su gaida iyaye da mutanen arziki.. Alhaji Yusuf yaji dadin hakan kuma yace dashi zasu je sai ya basu cen su sai su kwana washe gari su dawo.. anje kasuwa ranar umma an kashe tsaraba iri iri kamar hauka wanda za'a ba ma mutane da su mama.. tace harda masu jin haushi sai ta basu su san cewa ita kam yanzu an wuce wurin sai dai kallon..

JADWA (Completed)Where stories live. Discover now