JADWA 33

56 5 3
                                    

Daren ranar da umma ta wuce ningi, Abba ya gane bata gida sai yayi waya da zainab dama washe gari ne zasu zo bauchi nan yake fada mata komai anan ta kara bashi labarin duk abun da yayi harda irin wulaqanci da ya mata yace karta kara shigo mashi gida, tabbas yayi mamaki yace tayaya da ranshi da lafiyar shi zai aikata wannan danyen aikin.. nan zainab ta ke fada mashi cewar suma su hidaya komai jirgin su zai sauka kuma taji sauki sosai amma tace bata so ka sani surprise zatayi maku, nan hankalin Abba ya tashi yace ko dai bata so ta ganshi ne ? Innalillahi wa'inna ilaihi raju'un yake ta fada zainab ta cigaba da ba ma yayan hakuri tana nuna mashi cewa ita fa ba hakane nufin ta ya kwanta da hankalin shi ai hidaya zata fahimci komai kuma yasan da ranka da lafiyar ka baza ka taba aikata wannan aikin ba ita dai wannan azzalumar da shigo cikin rayuwarmu ne tayi duk wannan abun kuma In'sha'Allah amana zai kama ta Allah bazai barta a haka ba kuma zaku cigaba da rayuwar ku kai da hidaya ta kwantar mashi da hankali sosai kuma yaji dadin maganganu ta. Yayi mata godiya sosai yayi fatar Allah ya kawo su lafiya.

Yaso ya fada ma jadwa yace sai kuma yayi tunanin bari ya barshi a matsayin surprise in don zai so ganin reaction in ta..

***
Ita ko jadwa yar tana faduwa da gudu ta sheko ta buge umma ta rungume mahaifiyar ta fadi mommyyyyyyyyyy wani hawaye ne ma zaifi ya fito mata ita ma hidayar rungume ta tayi suna kuka na ban tausayi tana tsaye jadwa sai da duka kuka harda majina idon ta da yake fari lokaci daya ya koma ja, hmm Abba kallon hidaya yake yi yana jin wani sabon soyayyar ta na kara shiga ran shi... Ta rame amma ba sosai ba sai manyan idon ta da ya kara fitowa shi tayi kyau ba laifi jilbab milk colour ta sa sai yayi daidai da jikin ta.. kowa wurin na kallon su cikin tausayi zainab sai da tayi kuka akan kukan da hidaya da jadwa suke yi babu wanda ya hana su ko ya rarrashe su don su san wannan ranar ranar da Allah ya karbi addu'ar su ne kuma ranar farin cikin su ne...

Ita ko umma juyawa suka yi suka tana kokarin cire kayar ta sai ihu take tana fadan ni ce nayi asiri na farko da gashin kan Alhaji tun kafin na aure naje wajen mi aski na samo gashin shi shi nake ma boka, yana bani kudin sadaka tashi nayi amfanin na kai ma boka har ya amince zai aure ni, da ya aure ni nayi ma hidaya asiri na farko aka hada ta da bakaken aljannun da ma tana sallah ne abun yazo dasauki na biyu kuma ni ce nayi haka ta ta fadi maganganun abinda ya faru.  Ta nayi ta na yawo cikin dakin tana ihu tana cire kayan ta babu wanda yake kusa da ita Abba kuka yake yi, kowa wajen sai da yayi kuka saboda tausayi....

Haka Abba yasa aka kira masu aiki don lokacin an kara samu wasu masu aiki aka kamata aka daure ta yace duk a kwaso kayan ta, ana asa a mota haka yace a wuce da ita ningi kuma a fada masu abunda tayi yace ya sake ta.. hidaya da sauran yan uwan ta da suka zo tare, haka suka zauna da su Abba da jadwa kowa na fadi albarkacin bakin shi, Abba yace ya dauki wannan abun a matsayin jarabta kuma ya gode ma Allah da wannan karshen lamarin tunda har Allah yasa suna da rabon kara haduwa da hidaya, haka ya duka ya bata hakuri yana kuka sosai ita ma hidayar tausayin shi tayi tace ita bai mata komai ba wlh umma ce ta mata kuma Allah ya fara saka mata tun a duniya ta gode ma Allah da aka gane gaskiya wannan lamarin tun anan duniya, sosai suka bama mutanen wajen tausayi..

Haka dai suka cigaba da magana ita ko umma an kwashe ta an wuce da ita ningi.
Sai da hankalin ya kwanta bayan kwana biyu Abba ya kira kowa acikin parlourn yace yana so ya mayar da hidaya dakin nan suka kama kallon juna cikin so da kauna. Kuma ya basu lamarin auren jadwa akan an kawo kudin auren ta amma yace bazai sa rana ba sai da izinin su, sun ji dadi yadda abba yayi, a haka suka ce a sa rana ko da zuwa karshen wata ne..

Nan zainab tace babban walima za muyi kam tunda auren biyu ne ? Sai Abba yace da nawa da nawa tace ka naku ka na jadwa sai kowa yayi dariya ya sai Abba ya bar parlourn yace zai fita yana mai farin ciki jin yake yi rayuwar shi ta dawo sabuwa da.

Ita ko jadwa ta ba ma Dr fahad labarin duk abunda ya faru saboda korafin bata bashi kulawa yayi yawa sai ta bashi labarin abun da ke faruwa gidan su hakika ya jinjina al'amarin yace abunda umma tayi ne ya koma ta yace Alhamdulillah tunda gaskiya ya bayyana kuma yaji dadi yadda Abba da mommy suka ce sun barta da Allah yanzu ga yana Allah ya daukar masu mataki tun a duniya umma ta haukace yanzu abunda da shuka zata girɓa..

Da haka suka ta fira nan ya tambaye ya ce ya maganar sa ranar su ? Nan ta fada mashi yadda aka yi tace anyi shawara ance a barshi karshen wata da farin ciki yace da gaske baby? Tace wlh yace kaii Alhamdulillah i Can't wait to be your groom... Tace sooon In'sha'Allah yace amma Ni dai ko dazu munyi waya da daddy bai ce mun komai ba tace zai ce ai In'sha'Allah maybe Abba bai riga ya fada mashi ba tace toh shikenan.

Zan zo bauchi cikin satin nan In'sha'Allah Ni da kai zamu hade laifi duk abunda kike so shi zan saya maki kinji tace ok love sai yayi murmushi yaji dadin yadda ta kira ok love yin don murya sai ya kara zaki daidai lokacin. Da haka suka yi sallama ya kashe waya. Yana gama waya daddyn shi ya kira yana mashi albashi da surukan shi sun tsayar da rana. Da murna yake amsa maganar don yaji dadi sosai yace Alhamdulillah sai daddy yace sai ka shigo Adamawa a fara shiri biki ko nan Aunty na kusa da Abba tace toh dan gidan Aunty angon gobe Finally Allah yayi yanzu sai kazo mu fara hada lefe koh da sauran shirye shirye sai Dr fahad yace dama munyi maganar da ita akan bauchi zamu hada duk abunda tace tana so shi zan saya mata sai Aunty tace hakan ma yayi amma dai karka dade ko kaje can saboda nan ma akwai shirye-shiryen da za muyi yace In'sha'Allah da ta gama waya da shi sai ta ba ma mommyn shi shima haka suka gaisa tana taya shi murnar daganan suka yi sallama..

Koda ma aikatar Abba suka isa da umma bauchi da kyar suka iya fitar da ita duk ta jin ma kanta acikin mota saboda kokarin fitar da take son yi..
Mama na ganin su ta fara salatin tana fada ma Allah tace yau bai zan gani ni a'a innalillahi wa'inna ilaihi raju'un kawai take fada 🥺 Anan suka fara bata lamarin komai take nan heat attack ya buge mama ta fadi.. jikin su na rawa suka kira Abba yace a kai ta hospital ita kuma su daure ta nan gidan da driver shi da yake namiji aka kira wasu maza su biyu aka daure umma nan magana ya fara kaɗe gani sai gashi ana zuwa gani umma ita kuma mama tana a gadon hospital Abba yace kar su fito zai turo da kudi a kula da mama sosai... Sai da washe gari yayi mama ta farfaɗo cikin tashin hankalin abunda umma tayi..

Anan tace masu aiki su kira mata Abba don sun ce shine yace a Kaita hospital Kuma karsu dawo sai ta farka, koda taji abunda yayi tace wannan bawan Allah dan Aljanna ne duk irin mugun abunda umma tayi masu ace yace a cigaba da kula da ita hmm tace Allah sherin da ya saka da alheri ba zai wuce a bazan ba. Ko da Abba ya dauki wayar haka ta rika bashi hakuri harda kuka Abba byace don Allah ta daina kuka ai ba ita ta mashi ba umma ne tace amma ai Ni ce na haife ta, yace ya sani amma da still tayi hakuri don Allah... Shi duk abunda yayi yayi ne saboda Allah, taji dadin maganganu shi tace Allah ya jikan iyayen shi ya saka mashi da alkhairi. Nan ta ke tambayar su A'ishah, yace "wlh bai gansu ba ance sun dade basu gida kuma basu zuwa makaranta amma bai san ko ita umma nada masaniya da inda suke ba gashi kuma gashi yanzu tana cikin lalura". Mama sai kuka yace "Ta kwantar da hankalin ta In'sha'Allah daga yau zai sa a fara bincike akan su amma ita radiya tana Kano tana cikin yan haddan karatun Alqur'ani bata ma san abinda ke faruwa. Kuma nayi Alƙawari ko ta dawo zan cika ba da rika ta amma su A'isha bazan iya ba sai dai su dawo na wurin ku mama don halin su ba daya da na radiya ba wlh suna biye ma umma labarin da nake ji nasu baya mun dadi ko kadan, zan cigaba da biya masu kudin karatu har su gama In'sha'Allah kuma ina fatar idan sun dawo sun ji abunda mahaifiyar su tayi ya zama izina a gare su".

Mama tace "Allah sarki baiwar Allah Radiya" kayi kokari Alhaji kuma kai dan halaq ne, Allah yasa su dawo cikin koshin lafiya Allah ya taimaka yasa maka a gaskiya umma ba uwa bace Allah ya shirya yasu baki daya.. Ameen In'sha'Allah zan yi kokari da yarɗan Allah mama..

Ma'assalama 🦋❤️
Unedited, ignore mistakes pls
Comment and vote plss


JADWA (Completed)Where stories live. Discover now