JADWA 38

65 6 0
                                    

Tana kama duk abunda take yi sai ta zauna tana tunani mama ce take mata magana amma san bata ji abunda take fadi ba saboda dogon tunanin da take yi..

Bubbuga ta tayi tace ke radiya lafiyar ki kalau kuwa ko jikin umman naki ne ? Amma naji kin ce taji sauki koh? Eh tace ta daga kai can tace mama ina son muyi wata magana wlh ina cikin damuwa.. koda aka auna jinin umma tana dauke da cutar HIV.

Da karfi mama ta tashi kamar zata kife kasa tace HI me kika ce ? Radiya ta kisa tace mama HIV toh Ina ta kwaso shi??? Kenan Alhaji yana dashi? Radiya tace umma bani da amsar tambayoyin ki suka nima amsar nake neman sani a iya zama na da umma tun koma Bauchi wlh ban san ta da tabi'ar bin maza ba marai nace kilan su suka sa mata sannan umma ko kiran wayan ce ta shigo tohi idan ba ku bane nan toh Abba ne yana son wani abu.

Hmmm toh yanzu meye abun yi mama ta tambayi radiya, sai radiya tace mama kawai a kira Abba a sanar dashi shima yaje yayi gwaji idan kuma yana da msaniya duk mun tunda wannan abun ba abun boyo bane, mama tace tabbas radiya haka za'a yi.  Yanzu ke zaki kira shi koh sai radiya tace bari na kira.

Rigingi daya biyu Abba ya dauko da sallama suka gaisa bayan sun gaisa ya tambayi mai jiki radiya tace da sauki yace yanzu yake cewa zai sa mata kudi account su kara cikin magani sai radiya tace Abba ina da kudi enough wlh ka barshi kawai yace ba ruwan ki kyauta nayi ai tace toh mun gode Allah ya saka da alkhairi. Nan ta ke fada mashi mama nason suyi magana yace ba matsala a ta bata wayan, sun gaisa kuma ta kara mashi godiya da dawainiyar dasu duk da irin abun da aka masu sai yace kada ta damu ai komai ya wuce ta bar tuna baya tace toh nan ta fara kwaro baya ne Abba yana zaune sai da ya tashi da yaji mama tace akan umma na dauke da cutar HIV sai da gumi ya karyo mashi.  Yana fadar innalillahi wa'inna ilaihi raju'un yace umma ina ta kwaso mana wannan cutar innalillahi wa'inna ilaihi raju'un kawai ya ke fada mama tace kasan umma da wani hali na bin maza ne ? Yace shi ko alama babu shi a zaman su da umma bai taba jin ko waya tayi da wani ba wlh.

Abun dai akwai abun mamaki sosai aciki mama ta fada ta kama ma Abba nisiha ganin yadda ya rude daganan ta bashi shawara tace ya ce yayi gwaji yace In'sha'Allah ko da ya kashe waya hankalin shi a tashe dama yana Company wayan da suka yi ba shiri ya ta shiga mota ya wuce sai hospital bai je hospital inshi saboda gudun magana koda ya kasance positive Amma ba ya fata ko kadan.

Da haka ya kama tuki yana tunina kamar me kuma yana fargaban abunda zai je ya dawo

Karamin wani clinic ya tsaya ya shiga yayi sallama wata nurse ta amsa ya mata bayanin komai sai tace ya biyo tace ya biyo ta lab, koda suka kaje ta dibi jinin shi, 3hrs result ya fito.. Alhamdulillah babu abunda Abba yake dauke dashi.. Abba dadi wajen shi kamar be sai hamdallah nan take ya kira mama ya fada mata sakamako mama taji dadi sosai tace Allah ya kiyaye gaba yace Ameen...

Ya kama hanya gida yana tunani, koda ya isa ida da hidaya ya ci karo zata fita parlourn nan ta fara mashi sannu da zuwa ganin yanayin mijin na ta yasa jikin ta yaya sanyi sosai sai ta fara tambayan shi ko lafiya? Ce mata yayi lafiyar shi kalau sau da dai... Nan ya fara bata labarin komai tun suna tsaya har suka zauna abun ya bata mamaki sosai sai hamdallah take ma Allah da ya taimake su yasa Abba bai dauki cutar ba..

Hidaya tace lallai umma ita ce jarabawar rayuwar mu Allah mun gode ma da kare mu da ka sharrin ta duk da mun wahala Alhamdulillah tunda outcome in yazo da sauki ta fada tana ta gumi nan ya cigaba da rarrashin matar shi don yaga itama yanayin ya chanza ya masu nasiha duka yace shi zai wuce yayi wanka.

A haka radiya da mahaifiyar umma suka ci gaba da jinyar umma ana ciwo HIv ne ya kwantar da haukan na ta amma ba don ya fita ba, ita ko radiya a kullum bata da wani tunani sai idan umma ta kwaso cutar ga kuma yan uwanta su A'isha har yanzu shiru basu dawo gida ko ta kira su ba kullum take samun su a waya ba kuma idan ma taci Sa'a ta same su toh sai dai suce zasu dawo duk da halin da umma take ciki da ta fada masu bai sa koda wasa sun leko ba.

Sauran kwana biyu bikin jadwa, jadwa tayi waye da radiya tace zata zo ko kwana ɗaya ne tayi ana shirye-shirye da yake ba wani even za'ayi walima kawai za'ayi ko shi sai an kai amarya sai Abba sa yace zai gabatar da waliman da manyan friends inshi yan kasuwa bayan anyi daura aure immediately. Ita ko nasu jadwa sai bayan an kai ta Abuja anan Dr fahad zai yi waliman shi da friends da yan uwan shi na Abuja amma mommyn shi na adawama da Aunty sunce sai ya kawo jadwa tayi kodadai daya ne bayan biki domin ta saba dasu tunda ba Adamawa zata zauna ba idan ya wuce da ita Abuja ai baza su saba ba. Ya amince da hakan amma ita jadwa koda ya fada mata bata tuna damuwa sai da aranta kamar wata babban exams zata je yi don duk second daya idan ta tuna sai naji gaban ya fadi duk da suna waye da ita kuma tana jin dadin yadda ta suke kula da ita suke son ta kuma tana da yaƙinin ko a fili ma sai hakan yafi amma tension in na ranta. Dr fahad ya lura da haka duk da yadda tayi dun ta boye amma sai da ya fito fuskan ta, kuma ya mata bayani yace tabbas yasaan she will feel somehow about idan taje Adamawa yadda su mommy da aunty zasu kula da ita da su sultana wlh sai taji kamar ka ma ta bishi Abuja don suna don duk abunda yake so kuma shi yasan su waye family inshi da wannan maganganu ya sanyaya mata zuciya taji dadi sosai.

Ya thursday kowa yan uwa an hadu dana hidaya yan tanzania duk an cika gida hatta da mahaifiyar hidaya sai da tazo dama tana raye amma sai dai ta tsufa yaƙi bari a bata la bari tace zata tazo bikin jikarta, gidan Abba mutane sun cika kuma duka yan uwa da abokan arziki ita ko radiya tana hanya zuwa bauchi domin gobe friday kuwa za'a daura auren jadwa Yusuf da Fahad Ibrahim Rashid.

Ahaka shirye shirye ya cigaba da wakana ana ta dafe dafe akaci aka sha hidaya kuma ta kira yar ta taja ta gefe ta fara mata nasiha akan rayuwar aure, sosai maganganun hidaya ya ratsa jikin jadwa harda kuka sai da tayi ta ta kawo mata misalai da kissosin matan Sahabbai da suka ta ma mazajen su biyayya da ladabi akan rayuwar auren su sannan ta kawo mata misalai da yadda ƙaddaran rayuwa ya ta dawainiyar dasu a gidan da irin biyayya da take ma Abba da duk tayi koyi dasu ta nuna mata cewa rayuwar aure Akwai jarabawa aciki idan Allah bai jarabce ka ta miji ba sai ya jarabce ka ta uwan miji ko surukai ko makwabtaka ko abokiyar zama daya daga ciki Allah yana iya jarabta ka koma fiye da haka toh dole sai kinyi hakuri sosai kin jajirce domin samun aljannan ki ta kuma bat labarin abunda ya samu umma da kuma yadda Allah ya kare shi bayan ita babu wanda hidaya ta fada ma wa ita kuma tace yana bakin ta tayi shiru ta fada mata ne saboda ita yar.. duk inda hankalin jadwa yake sai da ya tashi babu abunda take yi sai zubar da hawaye lallai Allah yana jarabta Alhamdulillah da komai yake zuwa masu da sauki kuma ta kara jinjina ma mahaifiyar ta hakika mahaifiyar macce ta gari acikin zamanin nan basu da yawa masu hali irin na mommyn ta tabbas zata yi koyi da ita kuma duk ta dauki nasihar ta sai dai zata yi kewar ta sosai a lokacin da take buƙatar Kara shakuwa da mahaifiyar ta gashi aure ya shiga tsakaninsu..

Kukan da jadwa ke yi Ni yasa hidaya tazo tana bata hakuri, tana rarrashin ta sai ga Aunty zainab ta shigo dakin ita ma ta fara bata hakuri da haka ta tashi ta wuce dakin ta Aunty zainab raka ta, tana isa dakin ta sai ta ka radiya ba ƙaramin dadi taji ba har ihu tace wlh naji dadin zuwan ki Alhamdulillah kin zo lafiya ya jikin umma? Tace da sauki Alhamdulillah tace zuwa kenan fa na tambaya aka ce kina ce keda mommy kuna magana shiyasa na tsaya nan nasan daga kin fito toh sai nan zaki dawo ai. Tace haka ne kam toh kije ki dai da mommy tace toh aunty amarya sai jadwa tayi dariya tace naji dadin zuwan ki gashi bani da friends ko daya da na amince ma ko afra na ki bari nasan komai ga labarin bikin don na gane ita wacece shiyasa na damu ki zo ba ke kadai kin ishe Ni bana son harka da kawaye da gaba baya su zasu zo suyi betraying inka. Radiya tace wlh kuma Ni shiyasa I don't keep friends.. gwara haka Ni kade nasani tunda ba wani event za'ayi ba Ni kaina naso nazo tunda wuri toh jikin umma ne kuma kinsan ita ma mama ta tsufa ba komai zata iya ba..  sai jadwa tace har yanzu su A'isha shiru dai ? Wlh kuwa har yanzu sun ki zuwa kuma ba kullum nake nake samun su a waya ba sun ma ki fada mun inda suke kuma sun ki su zo gashi Ni kadai ke ta fama jadwa tace In'sha'Allah zasu dawo nasan ma idan aka gama hidimar bikin nan Abba zai yi wani abu duk inda suke zasu dawo da yarda Allah ke kuma ki cigaba da abinda kike yi Allah zai baki lada. Radiya tace toh shikenan In'sha'Allah Aunty amarayan mu sai tayi dariya ta mike zata wuce wajen mommy ita kuma amarya ta shige toilet..

Ma'assalama 🦋❤️
Not edited
Let's meet in next chapter In'sha'Allah
Don't forget to vote and comment
Your khadss ❤️🦋

JADWA (Completed)Where stories live. Discover now