JADWA 22

68 3 2
                                    

Sun hadu hospital lokaci guda ko da isa malamin tare suka shiga room in da hidaya ke ciki lokacin zainab na waya da family da hidaya kenan suka nemi da a ba ma Abba suyi magana. Hankalin su ya tashi sosai jin ance yar uwan su bata ko iya magana. Nan dai Abba ya kwanta masu da hankali kuma yace masu In'sha'Allah ta kusa samun sauki.
Malam yana gaife yana kallon jikin mommyn jadwa don yau kwana biyu kenan ba magana sai juyi sai kallon mutane su drip in da ake sa mata su kansu doctors sun kasa gane ko menene. Lokacin da malamin ya nemi da abasu wuri daga shi sai Abba sai zainab ko jadwa sai da yace su wuce waje taje can ta tsaya da su lantana.
Yana matsa wa kusa da ita mommyn jadwa ta fara zare ido tana kallon shi ta yunkura da karfi zata tashi zaune sai ta kasa sai kuka nan malam ya fara gano matsalan amma baiyi bayani ba..
Sai yace zainab ta samo ruwa a kofi da kawo da sauri zainab tabi umurnin shi tana dawowa da kofi a hannu ta mika masa zama yayi ya yi addu'a yi a ciki ya fara watsa mata wani kuka da mommyn jadwa ta kama yi tana fisge fisge toh kai daga ji kasan ma ba muryan ta bane nan ya fara cewa wa kayi magana ko ka fadi ya akayi kazo jikin wannan baiwar Allah sai kuka dai ba cewa komai ya ko nan ya fara karanto ayoyin Alqur'ani, amma shiru ba magana sai kuka da fisge fisge saura kadan mommyn jadwa t fada kan don hanta da drip inda ke hannun ta ta cire shi ka fisge fisge. Malam yace ta kyaleta karta matsa kusa da ita, haka ko ta fada sai wani kuka tayi mai kara wanda bako su lantana ba harda da doctors sai da suka shigo room in don gani me ke faruwa nan yayi masu alamu da su wuce haka suka wuce shima doctor kabir jansu yayi suka wuce jadwa sai kuka haka doctor kabir ya wuce da ita office Yana lallashin ta, shi ko Abba ya shiga wani hali mai wuyan fassara wa shi tunanin shi wai meke faruwa ne? Me yake gani haka? Kuma babu wanda zai bashi amma sai mallam. Aiko malam ya gama karatun shi ban kuka babu abunda hidaya ke yi. Can ya ja Alhaji yace su wuce office in doctor kabir, suna zuwa aka kira zainab tazo ta tafi da jadwa. Nurses sun dauki mommyn jadwa su maida kan gado zad tausayi duk taji ciwo ka hannu da ta fisge drip ya kumbura, ga gashin ta duk ya wargaje abun ka da masu yalwan gashi kullan ta na kai garin fisge fisge ya fadi sai da zainab tayi kokari ta nemo ta sa mata lokacin hawaye ke zuba tana kallon kowa daya bayan daya.
Nan malam ya ke tambaya doctor kabir akan hidaya cewa ko jinin da ke zuba mata ya daina, suka ce eh amma bata magana kuma bata cin abinci sai kuka kawai, nan ya tambayi Abba ko ta taɓa lalura haka ko makamancin haka? Abba yace ko da wasu bata taɓa ba wlh shi yau ne ya fara ganin wannan al'amarin ma. Sai yace toh magana ta gaskiya matar kan aljannu ne akan ta kuma alamu sun suna na turowa ne tunda bata taɓa lalura haka kuma ba sa magana sai dai akwai abunda zamuyi wanda dole zasuyi magana kuma zanje zanyi istihara sannan za'a mayar da ita gida kuma ba gidan ka ba wannan kaunar naka ta dauke ta ake ta gidan ta ta zauna acan tukun duk abunda nagani zan fada maku sai asan mai za'ayi kuma In'sha'Allah zata ji sauki zasu fita jikin su koma inda suka fito da yardan Allah SWT hmm Abban yakai minti 5 yana kallon malam shi mamaki take yi tabbas duk wanda yayi wannan abun ya cutar da hidaya yasani cewa hidaya ba duk ma ta kasance mai ibada ba da ila abun yafi haka wama yasani ko cikin abokanan kasuwancin ne masu binshi da bita da kulli yasa suka fara tabo iyalan in da ma umma ne yasan da ya fi haka yadda bata damu da ibada ba da wannan tunanin da yake yi malam yace Alhaji kayi hakuri ka dai tunani komai zai wuce In'sha'Allah yanzu ayi abunda nace Toh shikenan haka Abba yaje ya ma zainab bayanin komai zainab sai kuka daganan sai aka ɗauki mommyn jadwa aka sa ta acikin motan Abba jadwa na kuka hakan daddyn marwan mijin zainab ke ta lallashin su har suka isa gida. Abba ya aje su ya koma gida ya tarar da umma kwance babu abunda ya dameta ya tambaye ta yara tace sun dakin su kuma ita karya take yi bata gansu ba sun dai mata karya sunce zasu je makarantar saboda yanzu har samari sun fara yi yaran manya haka suke kwasan su idan Abba baya nan, nan ta fara nuna damuwar ta tana tambayar wai ya jikin hidaya Abba kyaleta kawai yayi yace da sauki dama shi Abba ba mai irin surutun bane kawai yace mata an sallame mommyn jadwa na gidan zainab can zata tsaya kafin jiki ya warware nan umma gaban ta ya fadi tace meyasa? Yace haka kawai tace toh gobe In'sha'Allah zata je ta duba ta. Yace ba matsala ai.

***
Yana shiga dakin sa ya huta ba shiri umma ta kira tabawa tana fada mata, nan tabawa tace ai dama zata kirata ta bata labarin don taje wajen boka akan maganar da tace ayi mata aiki kan Abba ya fara mata fada ita bata gane mashi ba, sai boka yace komai step by step shi zai yi kuma yace aljannun da aka tura ma hidaya masu karfi ne sosai wani lokacin ma basu fita sai sun nakasa mutum koda anyi kokarin fitar dasu kenan ko su makantar da kai ko kuma su kurmantar da kai, don haka shi sai anga yanda yanayin aikin hidaya ya wuce sannan zai fara mata aiki kan Abba ya dama yana mata aikin ai jefi jefi tace toh ta gode da kokari sannan tabawa tace ta turo da kudi za'a tura ma boka, toh kawai tace sai suka yi sallama ta tura mata.. don yanzu tabawa ta mayar da umma bank ko boka bai ce a turo kudi da zarar ta bukatar kudi sai da ta kira umma ita kuma bata jin keshin tura mata don Abba yana ma matar shi salary 300k duk months duk da basu rasa komai ba kuma still idan kana da wani bukata zai maka shi ba ruwan shi da wai duk yana baka kudi ko wani abu.

***
A gidan zainab kuwa jiki na nan yadda yake sai dai kallon mutane da mommyn jadwa takeyi wani lokaci kuma sai kuka, yau sistern hidaya zata sauka domin jinyar yar uwan na ta don video call in da suka yi da jadwa tana nuna mata mommyn ta abun ya dauga hankalin su. Koda ta sauka driver ya je ya dauko ta ya Kaita gidan zainab ba laifi yan uwan Abba na kula da mara lafiya sosai domin kowannin na kokarin zuwa gidan zainab.. karfe biyu na rana umma taje gidan zainab dasu A'ishah gaishe da hidaya koda suka isa haka umma ta kama yi kamar munafuka. Zainab ko kallo bata ishe ta ba haka suka kama yi sumu sumu ita A'isha abun ya fara bata haushi yadda yake masu ta ja fatima suka fita itama jadwa kamar hadin baki ko kula su bata yi sosai ba. Ummaa na ta sa baki suka tayi har suka isa gida.

***
Yau malam suka hadu da abba aka je gidan zu zainab yayi addu'a sosai ya sauke Alqur'ani har yanzu shiru basu yi magana ba nan ya ce kullum za'a haka yace shi dai istihara da yayi tabbas macce kuma na kusa da ita sannan za'a sha wahala domin aljannun ture ne sai dai In'sha'Allah za ci gaba da sauke Alqur'ani kuma za'a ga sauki, kowa hankalin shi ya tashi musamman Abba da zainab toh waye wannan ita dai zainab Allah ya sani bata yadda da umma ba amma bata ce komai ba haka dai akayi sallama abba ya wuce da malam..

Akwana a tashi haka kullum malam ke zuwa yana sauke Al'qur'ni yana addu'o'i yanzu ta fara samu sauki tana tashi tana yawo haka kuma ta rage kuka amma bata magana sai ta kalli mutane idan ana mata magana.. ita ko umma tun sanda taje bata koma ba ko Abba ya tambaye sai tace bata da lafiya ne ita ma.
Sai da kwarara ma tabawa kudi take yi watarana ta kai ma boka watara ta cinye...
Sati uku kenan ana ganin chanji amma maganar ne shiru haka dai a cigaba sati sai da akayi wata biyu da kwana biyar ana sauke qur'ani da addu'a da sadaka sannan hidaya ta fara magana kuma dama tana cin abincin sosai maganar farko da ya fara fito bakin ta sunan Allah sistern taji dadin haka sosai kowa yayi murna.. aka kira Abb aka ce yau hidaya tayi magana da murna ya tashi y je ya kira malam suka kama hanya sai gidan zainab koda suka isa suka yi tayi magana tayi shiru nan malam ya fara karatun Alqur'ani yana addu'a sai ko aljannun suka fara magana...

Let's meet in the next chapter In'sha'Allah
Vote
Comment
Share
Your khdss❤️

JADWA (Completed)Where stories live. Discover now