JADWA 8

88 3 0
                                    

Bayan sun koma gida musa da matar shi suka fara hada takardun gidaje da na shagogi kai duk wani ƙaddara da Musa yake dashi sai da ya haɗa da na bauchi duka ya fara neman dillalai masu saya har yaso ya haɗa har da gidan da suke zaune amma salamatu ta bashi shawara akan kar yayi haka saboda ina zasu zauna duk wannan abun yana yi ne daga shi sai matar shi ko Hajiya babba bata san da zancen ba. Cikin kwanaki kadan ka fara sayar da komai na musa kamar yanda ya bukaci haka Amma still kudi bai kai ba don 25m ba wasa ba haka dai saura kadan kuma salamatu still itace ta bashi shawara da ya nemi aro wajen Yusuf yace yana bukatar kudi ne urgent ya ara mashi 5m dama sune suka saura cikin kudin. Haka ko Musa ya dauga waya ya kira Yusuf ya shara mashi karya yace wani kasuwan ci zai daga south Africa za'a fara shigo mashi da wasu kaya toh shi dai Musa bai tsaya bincike ba ko shisshigi haka dai yace ya bashi nan da karshe wata zai hada mashi kudin ya bashi haka ko aka yi karshen wata nayi haka Yusuf ya tura mashi da kudin nan...

*** Shi kuma Musa ya kwashi komai da komai sai wajen boko ya kai mashi kudade haka boko yata washe baki yana sa masu albarka yana kara tabbatar masu kamar Yusuf ya tsiyace ya gama yanzu zai ba ma aljanu kudin su zasu fara aiki wani sati mai zuwa su dawo haka ko suka tafi suka koma gida wani sati da yayi suka zo ya basu magani da za'a je kofar gidan Yusuf a gina rami a saka da Yusuf ya bi ta wajen ko ya tsallake rami shikenan. Haka ya karba yana ta murna cikin daren na ya bi hanya bauchi shi da salamatu (ni ko nace wannan matar akwai kokari) ko da suka isa dare yayi sosai kowa ya watse yana gida saboda dare makwancin bawa hmmm Musa sai dadi yake ji haka koh ya fito mota ya fara gina rami kofar gidan Yusuf ya sa maganin kamar yadda boko ya bada umurni haka ya gama ba wanda ya gansu don ce yayi ma salamatu ta tsaya ta dunga duba mashi kar wani ya gansu haka suka rufe suka yi nasara ba tare da kowa gansu ba suka koma suka shiga Mota suka tafi suka wuce kuma daga nan hanyan su ta koma wa babban mota ta hau kansu shikenan fa duniya labari Musa kam Allah yayi mashi rasu nan take sai dai ita salamatu bata mutu ba amma ta raunana da yawa.. da kyar aka iya samu wasu information insu bayan da aka je asibiti don salamatu ba'a ma san inda take ba. Cikin wayan musa aka cire number sai a kayi sa'a da numbern Yusuf ne an kira shi ana fada mashi lokacin yana shago don rana tayi ma sosai ya ya fito gida kuma Yusuf ya bi ta inda musa suka sa asirin nan amma bai ji komai ba da yake Yusuf ya gado Mallam sosai da sosai kuwa baya wasa da karatun Alqur'ani da azkar sai da yayi su kafin ya fita kuma haka ya saba ma iyalinshi da haka ita ma ta nayi kuma tayi ma babyn su jadwa..

****Ba abunda Yusuf yake yi banda salati yana fada ma Allah. Hankalin shi a tashe ya kasha waya yace masu zai zo yanzu duk ya rude sai da yaron shagon shi ya fara kwantar mashi da hankali yana mashi nasiha. Nan hankalin shi ya fara kwantawa ko sai suka dauki mota shi da yaron shi sai garin da su musa suka yi hatsari anyi masu kwantancen Asibitin kuma sun gane koda suka je hankalin da musa yaga matar dan uwanshi da shi gawar musa nan Yusuf ya sulale ya suma dama koda aka fada mashi bai iya fada ma kowa ba hankalin shi a tashe suka wuto daga yaran shi sai shi suka kasani kadai shima da yazo tashin hankalin yasa ya sume...

***Allah sarki abbee (yaron su musa da salamatu mai sunan malam) dama basu sabo zuwa yawa dashi ba yana can yana wasa shi da mai aiki kamar yadda aka saba barin shi wajen mai aiki bai ma san abinda ke mashi ciwo ba ita ma mai aiki baya san abinda ke faruwa ba ita ma dai taji shiru shiru basu dawo ba kamar yadda su ka fada mata zasu dawo a jiya ta kira numbern salamatu a kashe ita kuma ta da numbern Musa saboda kishin salamatu yasa ta hana mata numbern mijin ta tace duk abinda zai faru a gidan ta sai dai ita ce take da hurumin kira ba mijin ta ba haka suke zama numbern salamatu take dashi bata da na mijin ta, jin wayan ta a kashe yasa ta fara addu'a Allah yasa lafiya gashi abbee sai kuka yake masu ba kamar yadda ya saba da ita kullum ayi wasa da dariya ba sai hankali ta yaci gaba da tashi sosai.

**** Yusuf an dauke shi an tafi dashi emergency nurses da doctor tsaya a kan shi, shi ko yaron shi sai hankalin shi ya tashi amma sai can yayi tunanin Bara ya kira Hajiya babba ya fada mata ce su musa da mata shi sunyi hatsari amma bazai tuna mashi cewa wai Musa ya rasu ba cewa zai yi hatsari ne kuma da sauki sai shi kuma Yusuf ya shiga tashin hankali ya suma da wannan tunanin ya gama ya iya Hajiya babba ya fara fada mata sai salati take yi tana kuka tace kata nan zuwa ita da driver ya kawo ta can asibiti.. Hajiya babba sai kuka take yi kamar idon ta zai tsiyaye haka ta kira driver ta fada mashi. A haka yazo yana mata hakuri suka shiga Mota suka kama hanya sai inda asibitin yake.. Kafin Hajiya babba ta iso Yusuf ya farka da salati haka yace ma doctor yana so a basu gawar dan uwan su zasu tafi gida a mashi sutura ita kuma salamatu aci gaba da bata treatment kamar yadda ya dace ko nawa ne zai biya ana cikin haka Hajiya babba ta iso da dubara da nasiha aka fada ma Hajiya babba labarin gaskiya abunda ya faru. Hakika ta yi imani sosai haka sai hawaye masu zafi ke zuba mata tana salati can dai ta yi karfin halin magana tace haka Allah ya shirya yanzu mu tashi muje gida a sanar ma yan uwa.. haka suka tafi sai gida suna sauka a babban gida wato gidan Marigayi Mallam kenan inda Hajiya babba take sai ka fara fada ma yan uwa mutane sunyi alhini abunda ya faru shi kuma Yusuf haka yaje ya kira hidaya a waya, yana fada mata komai ita ma sai salati take yi tana fada ma Allah. Haka tace kata nan zuwa ita ma. Lokacin jadwa na bacci haka ta shirya ta dauke ta cikin duba taje ta saka ta a mota ta saka hijab inta ta dauko keys in da dana mota ta rufe ta nufi gare sai babban gida..

Next chapter coming soon In'sha'Allah. Don't forget to vote and comment

JADWA (Completed)Where stories live. Discover now