JADWA 23

58 6 0
                                    

Ku dakata haka kullum kuna kona mu yau mun gaji wlh zamu fita zamu fita ya isaaaaaaaa mukace.. isuka yi wani ihu mai kara wanda kowa da yake wajen nan sai da ya razana yaja da baya, mallam ne kawai ya kara zuwa kusa da Ita wani murya mommyn jadwa ke yi wanda duk wanda yaji yasan ba ita bace.. Nan Mallam yace sai yau zakuyi magana ko bazan daina karanta ayoyin Alqur'ani akan ku ba har sai kun fadi wanda ya turo.. nan suka sake yin wani irin murya suna kuka wai alqawari suka dauka su baza su iya fadin wanda ya turo su sai dai yau zasu fita kuma basu sake dawowa ba, idan sun dawo ma kone wa zasuyi saboda ko tun can jikin matar nan akwai zafi kuma gashin Al'qur'ni da ake karanta masu kullum sai ya kona su kawai hakuri suke yi.. nan Mallam ya cigaba da karatu suka je wlh zasu fita yace suyi alqawari basu illata ta ba sannan basu dawo ba kamar yadda suka fada suka ce ai sun yadda nan suka ce zasu fita ta kafa nan Mallam yace sai dai su fita ta baki haka suka fita suna kuka mai kara sai dai kawai a kaga umma ta bude baki wa. Hmm nan suka wuce kowa yayi hamdallah sistern hidaya harda sujood tayi tana gode ma Allah ita ma jadwa godiya take ma Allah a bayyane harda hawaye nan tausayin su ya kama kowa musamman Abba shima yayi farin ciki sosai.. nan Mallam ya bada magani su habbatus sauda da man saitin yace a rika shafa ma mommyn jadwa sannan kullum a bata dabino kuda Bakwai kafin ta karya ta sha ya bada wani magani da ya haɗa da ruwan zam zam yace shima tana sha, ya dauko wani gayen yace shima ta rika wanka dashi In'sha'Allah zata ji sauki. Yanzu da ta tashi daga baccin nan nasan komai zai dawo mata sabo kai zainab ki tsaya kusa da ita idan ta tashi ki rika bata magana kadan kadan kuma kiyi wannan aikin ke da yar uwan ta In'sha'Allah kuma ku rika cikin dabino kuda Bakwai kafin ku karya, sannan ku rike karatun Alqur'ani sosai da azkar In'sha'Allah ba dai mugu. Nan suka ce sun gode Abba yayi ma mallam godiya yadauke shi suka bar gidan bayan yayi masu sallama yace idan ta farka a fada mashi zai zo.
Akan hanya suna fira da Abba da Mallam nan Abba je kara ma mallam godiya kuma yace ya duba yasa mashi kudi account inshi Mallam yayi godiya sosai, anan Abba wato badun doctor Kabir ba da yake shi mai basira ne Allah yayi shi ya kawo shawarar a kira ka da yanzu sai da muka ma daba daban mu rasa ciwo mu rasa magani yace tabbas haka ne ai Alhaji irin barin su doctor Kabir hospital ba Karin muhimmanci yakeda shi ma gaskiya don yana da basira da hikimaa sosai Allah yasa mu dace sannan Alhaji tsarin nan da kake nema ka haɗa da iyalen ka saboda idan kayi maka wani abu idan bai sameka ba yana iya samun iyalen ka toh sun Allah a kiyaye sosai yace In'sha'Allah zamu ci gaba da kiyaye wa nagode sosai.. da haka yakai Mallam gida ya sauke shi. Ya juya ya koma gida, koda ya isa ya ga umma kwance a dauki ta mashi Barka da zuwa ya amsa da yaso ya fada mata abunda ya faru sai kuma ya gama ai ita ma ya kamata ta tambaye shi ya jikin hidaya tunda tasan duk ya fita sai yaje dubata, da ya ga bata tambaya ba shima ya kyale ta ya hau sama.

Duk abinda ya faru bata sani ba, Ita kuwa a bangaren hidaya ta farka amma sai komai ya dawo mata sabo tana kokarin tuna da ranar da taci abincin da kuma zamar da sukayi da umma nan ta tambayi zainab ina umma ina jadwa ina Abba nan zainab tace a kira mako sune sai tace ai amma banda umma aiko sistern taji dadi tayi murna nan hidaya ke tambayen ta yaushe tazo tace yau, sai tace toh me suke yi a gidan zainab sai sun kawo mata ziyara ne ko da zainab ta je daukin jadwa ta kira ta ta fada mata mommyn ta ta farko tana tambayen ta da gudu ta sheko har tana faduwa zainab nace Jadwa kiyi a hankali mana, nan yaje wajen mommyn ta tace mommy ya jiki mommy Ashe zaki farka Alhamdulillah ya Allah na gode maka da kanuna mun wannan ranar sai hidaya tace dama Ni nasan akwai abunda ya sameni su zainab na boye mun ne jadwa fada mun me ya faru dani na manta na kasa tuna wa akwai na farka na ganin gidan zainab sai jadwa tayi shiru, kowa wajen shiru yayi sai kallon jadwa da hidaya suke yi.. nan jadwa tace mommy ba komai wlh kawai da... Tama rasa mai zata fadi sai kuka ita ma hidayar kuka take yi nan sistern ta ta jawo su tana lallashin su ita zainab da gudu taje ta kira Abban marwan tana fada mashi abunda ke faruwa da Abba taso ta kira sai kuma tayi tunanin bari dai ta fara kiran mijinta nan yace gashin nan zai dawo.. aiko ko yana kashe waya ya kira Abba ya fada mashi kuma yace su hadu gida shima Abba ya shiga damuwa yace su hade can toh..
Abban marwan baya riga Abba isa gidan nan yake shiga yaga hidaya da jadwa na kuka nan ya fara lallashin su ya ke ce mata ai ta bari yanzu Abba zai zo zai fada masu abunda ya faru, aiko nan aka ji sallaman Abba suka amsa kallon da take ma mijin yasa wani Sabuwar soyayya ya kara darsuwa acikin zukatar su shima ji yake yi wani soyayyar ta ya dawo sabuwa dar, hmm nan dai Abba kowa ha lura da halin da Abba da mommyn jadwa suke ciki nan Abban marwa ya katse shirin yayi magana yace, dama mommyn jadwa kun yi tafiya ne zaku je wani kano keda Abba shine kuka yi accident toh babu wanda yaji ciwo kuma dama daga ke sai Abba acikin mota ke ne kawai kikayi lossing memory inki sai aka dawo ana ta maki magani shine kika farfaɗo nan Abba yace eh hakane fah. Shiru suka yi da jin yadda Abban marwan ya tsara magana hmm nan mommy jadwa tace toh ni abun zan iya tuna shine munci abinci da umma wanda ni banso cin abincin ba ta dakura daga nan sai na gama jin jiki babu dadi kuma nayi mafarkin mutane biyu na mina mata wanda banga face insu ba amma tunda na farko bansan kuma me ya sake faruwa dani ba. Nan kowa ya sake baki yana kallon hidaya hmm da jin maganganun ta kuma abun ya ba ma kowa mamaki sai dai bata fadi wani maganar da yanu cewa umma ne tayi mata wani abu ba sai dai kawai zainab ce da take zargin ta kuma ita tabbas tana tunanin akwai sa hannun ta acikin al'amarin hidaya shi kuma Abba abun mamaki ya bashi toh tunane yake yi waye wannan mutanen biyu amma bai kawo komai ba ga maganar da hidaya tayi na cewar sun ci abinci da umma daganan jikin ta ya chanza..

*****
Nan dai Abba yace kowa ya samu wuri ya zauna, sai ya fara masu nasiha mai ratsa jiki ya nuna masu cewa duk abunda kama wani na mugunta wata rana zai dawo gare ka kuma idan ma bai dawo gare ka ba ta zaku tsayi wajen Allah SWT zai fitar maka kowa da hakkin sa dagana ya kwashe labarin komai ya fada ma hidaya duk abunda ya faru yace babu amfani boye mata komai gwara ya fada mata duk yasan cewa badun yawan ibadar ta da take yi ba da babu yadda abunda zai hana wannan abun tsakani ba sannan yace karta zargi kowa a ranta kawai ta dage da ibada kamar yadda take yi duk wani sadaqa da take yi ta cigaba domin yana kariya kuma yadda take kullum zuciyar ta is pure ta cigaba a haka kar ta bari shaidan yayi tasiri acikin zuciyar kuma duk wani abunda aka bata idan bata yarda dashi ba toh karta ci ko karta sa shi. Haka hidaya ta kama kuka da jin wannan labarin toh ita mai tayi ma mutane da zasuyi mata haka kuka take yi mai tsuma rai na tambayar su, ana Abba yace mommyn jadwa ina so ke gane shi da mutum basai ka mashi wani abu a duniya zai illar taka ba ke wani ko baki da komai ganin ki da yake yi a duniya toh shine babban tashin hankali shi sannan ku ke kisan yadda nake gwagwarmaya da mutane abokan kasuwanci na ko su nasan akwai wa'inda basu so na toh dole zasu iya mun irin wannan abun ku ke iyali tace ko bai sami ba yana iya fada maki ba wai ina fadan hakan bane ya faru a'a misali nake baku don haka kiyi hakuri ki godema Allah ayi nasarar gano matsalar da wuri kuma kuma ki dauka wannan kaddara ne shikenan ciki gaba da abunda ya dace sannan zan barki ana zainab zata cigaba da kula da kai Kuma duk yadda Mallam yace kiyi duk zata maki bayani idan jikin ki yayi kwari sosai zamu koma gida ke da jadwa duk ku cigaba da zama anan.. kowa yaji dadin yadda Abba yayi hikima ya fada ma hidaya komai abunda ya faru akan yadda Abban marwan yaso a boye mata da ta fadin abunda zata iya tunawa nan Abba yaga babu amfanin boye mata.

***
Bayan kwana biyu mommyn jadwa ta kwantar da hankalin ta ta cigaba da shan magani kuma tana yawan azkar da karatun Alqur'ani kuma sadaqa kullum sai tayi haka ta fara murmure wa raman da tayi duk ta fara cikowa, ita kuma jadwa an zama budurwa tunda an shiga SS1 ana zuwa school wannan kenan

***

Koda Abba ya koma gida haka umma bata tambayi hidaya ba shima kuma har yanzu bai fada mata halin da take ciki ba amma aran shi yana tunani iri iri kuma abun ya fara bashi mamaki yau dai ace idan bata tambaya shi zai mata magana. Aiko ko da ya dawo tayi mashi sannu ya zauna ya fara cin abincin ya gama nan yake nuna bacin ranshi akan rashin tambayar yar uwan zamanta da bata yi kuma tunda tace bata sake komawa ba yace ko akwai wani abu ne? Nan umma ta kwashe labarin wulaqanci da akayi masu ita da su A'isha da suka je duba ta, kuma tafi daura an zainab laifin, nan ya bata hakuri yace ai laifin ta shi fa mijin ta ita kuma zainab kaunar shi ne da ta fada mashi tuntuni abunda ya faru ya da ya bibiyi magana ya gano gaskiya kuma ya dauki mataki, bazai bari zainab ta raina ta ba kuma shima bazai bari ta raina zainab nan ta bude baki tace ai ko yanzu bai ɓaci bazai iya bibiya kuma ya dauki mataki daidai da abinda ya gano. Kallon ta yayi yace toh shikenan. Nan kuma ya kwashe duk labarin abunda ya faru daga kan inda aljannun da aka turo ma hidaya har yadda suka yi magana da kuma labari da hidaya ta fara bayar wa bayan ta farfaɗo da shi kuma nasihar da ya mata.. tunda ya fara bada labarin kuma ke gumi Ac ne acikin parlour Amma sai tsiyaya take yi, hmm nan tace lallai ba toh ita hidaya mai take nufi da take tun sanda muka ci abinci tare, nan Abba ya kara bata bayani yace ita fa ka yadda mijin zainab yaso ya boye mata ne kuma ya kirkiri labari shine ta fadi iya abunda zata iya tunawa amma bawai tace kinyi mata wani abu bane kina fahimtar magana na, nan tace eh Amma akwai matsala wlh sai yace matsalar mai ita a tunanin ta a zuciya ta fadi maganar ashe yafito fili sai ta rasa mai zata ce kuma sai ya ga tana gumi yace a'a ya kina gumi wai lafiya kuwa ?

Ma'asallam 🦋🦋
Not edited, ignore mistakes
Let's meet in next chapter In'sha'Allah
Don't forget comment and vote pls

JADWA (Completed)Where stories live. Discover now