JADWA 2

393 15 3
                                    

A bangaren sir fahad kuwa, tun sanda ya karbi address in jadwa bai yi tunanin zuwa gidan su sai yau da yakama lahadi, ba makaranta, yake so yaje area su. Amma kafin haka sai da sukayi labarin jadwa wa da wani friend inshi da kenan a cikin makarantar su. Ya nuna mashi cewa shi dai bai taba ganin fuskar jadwa Amma gaskiya yarinyar zata kasan ce mai kyau da kuma natsuwa. Kuma yayi mamakin yanda fahad ya kamu da matsananciyar soyayyar jadwa haka.

Kafin abban ya dawo sai da umma ta tabbatar Aisha ta iso da wuri. Dun kar asamu matsala.

Karfe 3 na lahadin jadwa ta shirya tsaf domin zuwa dauko abban ta daga airport saboda ita ce dama ke dauko shi bayason driver, hakan baya ma umma dadi, Amma toh ya ta iya ? Abinda yafi karfin ta ai sai ido, wani lokacin ba komai boka ko mallam ke iyawa ba musamman idan mutum ya kasan ce shi mai yawan karatun al'qur'an ne da kuma zikr tare da sallolin akai akai, ita kuwa jadwa ta gaji haka.

Bayan ta gama ta fito parlour anan ta tarar dasu umma dukan su tare harda afrah ta zo gidan.

Sallama tama umma cewar zata tafi zuwa dauko abban ta, galla mata harara umma tayi sanna tace mtwss toh ( aranta kuwa cewa tayi munafuka sai kace ita kadai ke da abba. Wai abban ta) Ni ko nace abban ta ne mana ita kadai tunda she's the only daughter of her Dad and mum.

Wuce wa jadwa tayi zuwa parking space don dama bata damu da amsar umma ba ta dai fada mata ne kawai.

Yauma kamar kullum Ashe hijab har kasa tasa amma yau fuskar nan ba niqab. Bata makeup dama she always prefer natural look Kuma she like pink lipstick yauma shi kawai ta shafa a siririn lips inta, tayi kyau sosai.

Shiga motar tayi ta kama hanyar barin gidan, kafin kace mai, mai gadi ya wangale gate ta fita bayan sun gaisa. Da ganin ta ba niqab suka yi tunanin zata tafi dauka abban ta kenam don gaskiya baza kata ba ganin ta ta fita ba niqab ba. Ita fa rayuwan ta ya banbanta da na sauran matan zamani.

Dun gaskia ko biki bata faya zuwa ba idan ba walima za'ayi ba, Kuma daman waye ma zai gayyace ta biki? Lokaci lokaci course mates inta idan za suyi aure suna gayyatar ta amma sai idan za'ay walima take zuwa, Kuma tana sayan anko sai dai ta dinka tasa kuma tare da zubudaidan hijab inta. Hakan yasa wasu suke ce mata gaskia su basu iya wannan life inta ba ai ko Allah yace enjoy life in a halal way. Sai dai tayi dariya tace haka Kuma take enjoying life inta. Su har gani suke yanda abban yake da kudi gata da kyau zubin larabawa bai dace ta ita wannan life inba

Su Aisha da Fatima kuwa tsana suke nuna mata kirikiri. A cewar su dun mommy ta ba ba hausa bace shiyasa ita bata damu da al'adar mallam bahaushe ba.. radiya kawai ke nuna mata so a fili Kuma suna jin haushin haka

Da isan ta airport ba jimawa ba jirgin su yayi landing. A tsaye take tana kalle kalle sai ga abban ta ta hango, murmushi gaske tayi da ya bayyana kyawawar hakoran ta. Chan abban na ta kalle kalle ai kafin ya ganta da gudu ta je gurin shi. Ta gaishe ya amsawa sannan ta karbi trolley in shi suka nufi motor

Wani Adam da ya fito cikin jirgin kamar yanda naji ankira shi haka ya tsaya yana kalan su, su dai sun burgeshi da ga gani 'ya da uba ne. Duk da jadwa na kama da mommyn ta hudaya kamar bai hanata kama da abban ta ba ta wani gafen domin shima fulanin asalin ne.

Haka Adam ya gama kallan su har jadwa ta ja motar su. Suka bar airport in. Can naji Adam nace wa DAMA ACE. da baya sauri da ya bi bayan motar su ko don yaga gidan su ya kulla wata akala da jadwa domin tayi matukar burgeshi. Amma ina yin hakan zai ja mashi ya iya rasa aikin shi da yayi shekara da shekaru ya na nema, domin kara minti daya da ga lokutar da manager campany in su yayi timing daga Egypt zuwa naija to tabbas zaiyi sanadiyar rasa aikin shi gaba daya. Amma idan har da rabon kara haduwa a tsakanin su toh komin daren da dai wa sai sun ga juna

Da wannan tunanin Adam yayi ya samu relief sannan yayi gaggawar shiga motar company, daman motor ta dadai tana jiran shi.

Bayan isan  gida kowa yayi murna daga masu drivers, masu gadi har da masu aikin abincin.

Ita ko hajiya umma ta darge da ita da masu aiki don dafa ma maigidan ta abincin da haifi so, ta dafa mashi tuwan shinkafa da miyan taushe, sanna nan pepper soup in kaza, ga kalolin cocktails da tayi. Yan matan ta ko na daki suna chat da dauke dauke pics.

Haka Abba ya yayi wanka ya huta ya samu natsuwa ya ga kowa na gidan Amma banda su Aisha da fatima. Ita ko radiya da murna ta tari Abba ta ji dadin dawowan shhi sosai. Ya fara cin abince  kenam sai suna firan Egypt jefi jefi sai can yace Wai ina su Fatima da Aisha ne ? Har da ma'aikantar gidan nan sun mu barka da isowa, su fa ? Shiru umma sai da ta gama tsara karyan da zata yi sannan tace wallahi Alhaji kasan yaran nan da bacci yanzu haka sun yi bacci amma su da  suke ta dokin dawowar ka yanzu bari in  je duba su. Abban yace A'a hajiya ki kyalesu idan kin ga sun yi bacci amma bacci rana ai na raggaye ne don sun ga yau lahadi ba school, yanzu ne ma na tuna da radiya tazo mun gaisa shiyasa na tambaye su don su bangansu ba. Tou Alhaji bari dai yanzu inje in duba su. Toh kawai yace, ita ko ta kama hanya zuwa dakin su Aisha.

Tana Isa ta shiga bako sallama ta ga suna ta pics radiya Kuma tana karatu harara ta buga masu tace yanzu ko meye haka ? Shiyasa wance munafukar kanwar ku radiya sai ta fi cin riba abba wata rana,taje ta gaishe shi ku kuma kuntsaya kuna pics in bazan tunda kullum yin pics baya kare maku. Nan suka kama hararan radiya suna fada mata kananun maganganu ita kuwa bazan ta masu nan umma ta daka masu tsawa ai kuwa nan suka arce da gudu suka nufi parlour suka gaida abban ya tambaye su mai suke yi  harsu ka dadai basu zo su mashi barka da iso wa ba ? Su karyan suka lafta mashi Wai karatu suke yi saboda suna da da test. That's very good cewar abban ya kuma ce Allah ya basu sa'a yace idan na huta kowa nashi tsaraba na nan.

Ihu su sa ya kaman yara suna godia.
Su ka koma daki.

Ita kuwa a bangaren jadwa tun bayan da suka ga gaisa da abban a parlour tace mashi zata je ta sha magani tayi sallah ta kwanta kanta na ciwo. Yayi mata sannu!

***
Bayan fahad ya shirya tsaf cikin farin shadda da yasha aiki baki. Ya saka hullan shi baki kuma takkalmin shi baki. Ya feshe jikin da turaruka masu kamshi dadi sai kamshi kake ji, Sajen fuskar shi ya kwanta luf luf zan shawa'awa sai wanda ya gani yayi nufin zuwa area su jadwa, daman sai da yayi sallah magrib sannan ya shirya ya fito ya ja mota sai GRA.

Yana zuwa gidan bai bashi wahalar gane wa ba saboda yabi address in da afrah ta bashi.
House no 6 ya tsaya sai ya ga mai gadi suka gaisa Kuma ya tamabaye shi nan ne gidan su jadwa Yusuf ?

Anan mai gadi ya ce mashi eh, yayi murna Kuma yace yana bukatar son ganin maihaifin ta? Daman Abban idan yayi sallahn magrib zai zauna yata zikr sai an Kira isha'i zai koma gida. Kuma da ma masallacin gida suke saboda abban ya gina masllaci agidan shi. Kuma mallam kabiru driver shine liman in

Yace tou yana cikin masallacin bara na mashi magana. Yace toh ya gode. Yana zuwa ya sanar da abba, Abba mai saukin kai ne sosai kuma yace ace ya shiga ciki akai shi guest room gashinan zuwa. Haka ko mai gadi yayi, fahad ya shiga Kuma an kaishi guest room, ba jimawa abba ya zo, sun gaisa sosai kuma sir fahad ya mashi cikakken bayani akan daga inda ya iso da dalilin sa.

Abban da farko da ni lecturer in su jadwa ne, Kuma ni ba permanent lecturer ba ne nazo nayi taking over ne ma prof. Adeyosun wale dake bauchi states University wato makarantar su jadwa kenam. Mu yan adamawa ne baba ne senitor ibrahim Rashid, nikuma ina aiki a Abuja I'm a medical doctor kuma i own my pravite hospital Amma ko students basu san aikin naba susan dai I'm not a permanent lecturer.
Nazo ina koyar da medical chemistry ne zanyi 3months ne bayan nayi 3monts zan koma Abuja naci gaba da aiki na. Yanzu nayi 2months
Na Kamu da son jadwa Kuma ban taba ganin fuskar ta ba kasance ce wa ita ma abociyar mai sa niqab ce. Amma wallahi Abba ahaka nake son jadwa, domin kowa na yaba ta acikin school tana da natsuwa sosai da tarbiya ga kuma illimin addini da na zamani

Kuma nayi kokarin samun dama muyi magana da ita,amma bata bani dama da taimakon kawar ta afrah na samu number ta da address inta sai ban Kira ta ba nace bara inzo gida in nemi izini tukun. (Duk wannan maganan a kunne umma da yake tazo wuce sai taji ana magana sai ta  tsaya tayi labe tana ji harda cewa kan uba! Medical doctor Kuma a Abuja ga ubanshi senitor, haba wlh wannan sai dai ya auri Aisha ko Fatima ba dai jadwa ba, duk acikin ranta take wannan maganan)

Abba yace good!!! Gaskia kayi abunda ya dace kuma abunda addini yace ayi Amma.....

Look forward for the next chapter

Khadija loves you❤️❤️

Please comment n vote, if possible share I'll appreciate!

KhadijaHarris
Khadssss❣️

JADWA (Completed)Where stories live. Discover now