JADWA 5

162 10 0
                                    

~~ NIGERIA~~

Saukan su gida Nigeria kenam su Hajiya hidaya da Alhaji Yusuf suka Isa haraban mallam, mutane masu tarin yawa ana zaune ana zaman makokin yan uwa da abokanana arziki kowa na jimamin rashin mallam....
Nan aka tarbi mutanen Saudi sannan aka masu ban gajiya da Kuma hakurin rashin mallam shi dai Yusuf shiru yayi Yana kallon mutane kamar bai San su ba, haka aka kai su daki suka huta aka kawo masu abinci Amma Yusuf bai iya cin abin ci ba sai da ya ga Hajiya babba sannan yayi magana da ita yace mata meyasa suka ki fada mashi abinda yake faruwa sai da ya Kira baba mai gadi ya fada mashi sannan zai sani. Nan Hajiya ta mashi bayani na kance wa yayi hakuri sun ga cewa ma ibada suke yi kar su fada masu su tayar da hankalin su su kasa karasa ibadar ta su.. Amma yanzu mallam addu'a mu ya ke bukata ba wannan maganan ba, nan yusuf ya saduda ya manta da hudubar banzar da shedan yake mashi dangane da yan uwan sa..

****
Yau ne kwana bakwai da rasuwar mallam har yanzu su Yusuf da matar shi su bauchi ba su koma Lagos ba... A ranar ne yan Tanzania suka zo gaisuwa amma sai dai mai ? Hidaya ta tashi tmda zazzabi mai zafi da ciwon Kai haka aka kai ta asibiti yan uwanta ta na ta mata sannu, anan doctor ya fito da result in tests in da aka mata bayan ansa mata drip yace masu Yana taya su murna hidaya na da juna biyu na tsawon kwana goma sha hudu watau sati biyu kenam kowa yayi murna da yan uwan ta da na yusuf, Amma shi gogan naku kan marna ai bana ma iya misalta mu ku wallahi 😁 baki har kunne

****
A kwana a tashi ba wuya hidaya ta ji sauki sosai suka dawo gida yan uwanta Kuma sun koma gida tuntuni, shi Kuma yusuf sai rainon cikin shi yake yi Amma ko suna so su koma lagos musa yace a bari yazo sai an raba gadon mallam sannan zai wuce haka ko aka yi. Duka yaran mallam ne sun taru cikin gida har da su zainab, mallamai da ka Kira sun yi nasiha sosai har jikin kowa ya mutu.. haka da aka raba ma kowa gadon shi. Sun samu alkhairai sosai domin ko mallam mai arziki ne... Shi dai Yusuf rabon shagogin mallam na kasuwa duk ya samu har uku Kuma manya ne.. ko wa dai da abunda ya samu. Anan musa yace Yana da abun fadi yace mallam ne ya bashi wannan wasiyar kuma yace Kar ya bude sai ranar rabon gado shi mallam ma shi yaso ya raba gadon shi da kanshi, Amma Ina alokacin jikin shi yayi zafi sosai ita ko hajiya babba mamakin musa take yi irin wannan zurfin cikin na shi, toh kilan Kuma mallam ne bai bashi daman fada mata ba..
Maganan da mallamin yayi ne ya dawo da ita da ga duniyar tunanin ta.. amsa takarda yayi ya bude ya ga rubuta ne Amma da Arabic Kuma tabbas hannun mallam ne toh yace kawai ya girgiza Kai sannan ya karanta Kuma ya fassara bawai dun basu San mai yace kawai ya dai fassara ne domin ya san yaran mallam su gwado shi sosai..

****
Takardar na baya Ni ne akan yanda musa da Yusuf ke aiki a wani gari shi Kuma mallam gashi baya duniya yanzu duk da komi nasu zai zama mallakin su Yana so ace sun dawo gida sun bar aikin su sun ci gaba da kula da dukiyoyin su da na kannin su mata matukar haka bazai takura masu ba, idan da yuyuwar ci gaban aikin a bauchi su karasa shi anan Amma yana so su dawo gida.
Tirkashii!!! Hajiya ta fada a ranta ta San Yusuf bai da matsala zai iya yin komai idan a kace mallam ne amma zai yi wuya musa yayi....
Anan mallam yace to shi zai wuce gida sannan Yana basu shawara su Yi abunda mallam yace amma shi ma yace idan har bazai ta kura masu ba..

****
Nan kowa ya shiga duniyar tunanin akan abunda mallam ya fada sai can Yusuf yayi kokarin sallamar mallam da abun alkhairi sannan mallam yayi godia ya wuce nan Yusuf ya shaida ma yan uwan shi cewa shi zai yi yanda mallam yace duk da cewa Yana matukar son aikin shi amma zai bi umurnin mallam shi ko musa nan take yace bazai iya barin aikin shi ba aiko shi mallam ya fada yace idan zai ta kura mana mu barshi...

Wannan kenan!!!

Small chappie y'all

Non edited chapter, ignore mistakes please

Khadija Harris
Love you all 😘

JADWA (Completed)Where stories live. Discover now