JADWA 9

71 4 0
                                    

Da isar hidaya lokacin anje kai shi gidan shi na gaskiya bayan dawo wan su hankalin kuma ya koma wajen salamatu sai cikin yara Hajiya babba wasu suka wuce asibiti wasu kuma suka tsaya amsar gaisuwa ita dai hidaya ta bisu ita da yusuf don ganin halin da take ciki.. anan suka je asibiti kowa ya tausaya mata anan doctor yace yana so yayi magana da Yusuf da shigan su office ya sheda mashi cewa salamatu da samu injury na spinal cord class 4 🥺🥺🥺🥺 innalillahi wa'inna ilaihi raju'un kawai kake jin Yusuf na fada hmm rayuwa kenan za'a fita da ita waje za'a yi mata aiki kudi dai masu yawa. Haka dai Yusuf yana fada ma yan uwa hankalin kowa ya tashi a daidai lokacin ne yan uwan ta suka iso suma suka kaji hankalin su ya tashi dama basu da hali duk cikin su ita ce ke taimaka masu idan basu da abu haka dai aka fara shawara Yusuf yace zai bada nashi suma cikin yan uwan Musa yaran Hajiya babba kenan suka ce zasu yi gudumma wa dai a har haɗa haka dai aka samu da kyar kuma aka nemi tallafi a wani organization akayi masu funds raising toh anan aka samu kudi ya kai aka fita da ita waje ita da wata sistern ta don ta don a samu wanda zasu tafi tare wannan kenan.

****
Bayan anyi kwana uku da faruwa haka, haka akayi family meeting da yaran Hajiya Babba da su Yusuf da zainab sistern Yusuf ana so aje kaga ƙaddarorin Musa ko don yaron shi abbee da aka karba daga hannu mai aiki aka sallame ta aka ba ma Hajiya babba jikan ta ta rike shi, ana Yusuf ya fada masu kudin da ya taba ara ma musa amma shi ya yafe toh da yake duk kansu suna da hankali ba wanda yayi wani negative tunani akan abinda Yusuf ya fada kowa ya yarda amma suna mamakin toh meyasa basu taɓa ganin ya fara business in ba sai kuma suka yi tunanin ai yace bai dade ba da faruwa abun shikenan yace amma shi ya yafe har ga Allah ko wani ne wanda bai sani ba zai yafe mashi barai kuma musa yayan shi kuma dan uwan shi na jini hmmm. A haka dai aka gama meeting in aka je ayi bincike kam ƙaddarorin Musa ana suka tarar da abunda bazu yi zato ba barai kuma tsammani babu komai na Musa ya sayar hmm suka suka ce bazu yarda ba ta yaya dan uwan su zai yi wannan danyen aikin..?

****Amma sai takardun da suke gani na shaguna da gonaki da ya sayar duk suna ganin sa hannun shi da ma matar shi toh idan haka ne kenan matar shi tana da masani kenan. Sai Yusuf yace yanzu duk wani binciken zamu yi mu bari idan Allah ya dawo da su salamatu lafiya ta samu sauki sai tayi mana bayanin abinda ya faru mugi ko zamu gamsu da wannan ne aka rufe tauro kowa ya tafi gida..

*** One month da faruwar haka alokacin salamatu sun kusa dawowa haka kowa mutanen gida suna waya da ita gefi gefi sun jin muryan juna amma Yusuf ya hana a mata magana yace a bari sai ta dawo..

***
Acan ko idan salamatu ta kai kuka tana kukan nadama musamman yadda naji Yusuf ne ya taimaka da yan uwan musa su kawo ta nan tana tunanin mijin ta da irin makircin da suka yi ma Yusuf amma shine kuma ya zama mai taimakon su a rayuwa gashi boka ya cuce su magani bai yi aiki ma Musa ya mutu ita kuma ta zama gurguwa yanzu ko ta koma Nigeria sai dai da wheel chair zata rika yawo gashi dan su karbi komai basu ajiye mashi sai idan da suke ciki hardashi ma musa yaso ya sayar Allah ya taimake ta yasa ta bashi shawara da yanzu sun rasa komai. Kaichoni salamatu ta fada tana wani kuka mai cin rai sistern naji haka tace na lura da ke salamatu tun sanda kika ji labarin gida kike kuka nayi ki fada mun kinyi wannan kukan da kike yi nasani akwai ciwo irin halin da kika tsinci kan ki na rashin miji da kuma disability Amma ya zaki kiyi imani da Allah mana idan kuma akwai wani labarin da bansani ya kamata ki fada mun a matsayi na na yar uwan ki.. anan ta fara kuka ma tsanani tana fada mata labarin komai da irin asirin da suka yi ma Yusuf da ƙaddara da ta zuga musa ya sayar nashi don su biya boka ta fada mata komai da komai. Lallai sistern salamatu ta shiga tashin hankali da jin irin abun da yar uwar ta ta aikata amma sai lokaci daya kuma ta ji tausayin yar uwar ta ta. Da ita salamatu ta yanke shawarar idan ta koma ta san dole za'a tambaye yanda Musa ya sayar da ƙaddarorin sa idan kuma tayi karya toh tabbas ita zasu yi suspecting, gwara kawai ta fadi gaskiya daga nan ta nemi yafiyar su. Sistern ta bata koyan bayan haka tace gwara kaji kunyar duniya da gaji na lahira kawai idan sun koma ta fada.. Da wannan hirar salamatu ta fara samun sassauci amma kullum tana nadama da abunda suka aikata da ita da mijin ta amma kuma idan ta tuna aiki boka bai ci ba sai taci dadi ashe ma musa gajeren lokaci yake dashi a duniya har suka je yin wannan abun kai da nasani bai yi ba hmm..

***Yau ne salamatu zasu sauko Nigeria ta Abuja suka sauka Yusuf ya aika da mota yace aje a a dauko su kuma ya sanar ma yan uwa haka aka taru koda driver ka kawo su gida lokacin kowa ya hadu sakar salamatu daga cikin mota a ka saya cikin wheel chair sistern na tura ta sai da abun yaba ma kowa tausayi.. Haka aka ta mata sannu da gaisuwa tana amsawa tana nadama kuma tana tausayin kan ta koda aka kawo nata abbee bai gane ta dama can bai saba da ita ba yafi saba wa da mai aiki hmm da kyar ya yarda ya zauna saman jikin ta ga baya kuma can ya tashi da gudu yaje wurin Hajiya babba sai dariya ake mashi ita ko yaki ciwon abun ace dan ka na cikin ka bai gane ka ba.. Yusuf yace kar wanda ya mata magana sai ta huta amma ita ta matsu ta ma fara masu bayanin abun da ya faru kafin ma a kai ga tambayan yadda akayi dukiyar Musa ya sayar bata tare da sanin yan uwa ba kuma ka signing inta a cikin duka ta kardu da suka bincika....

**Ana ta labarin duniya can yan uwan salamatu suka suna so zasu tafi gida kuma suna so zasu tafi da salamatu.. can sai aka fara jin kukan salamatu tana cewa akwai maganar da take so ta fada amma don Allah a yafe mata kowa yayi mamaki sai waje yayi shiru ana sauraren.. Nan ta fara kallon Yusuf ido cikin ido sai kuka kowa sai mamaki yake yi Hajiya babba take salama ki fadi maganan ki mana muna jin ki...

Non edited, ignore mistakes pls
Kindly vote and comment!
❤️❤️


JADWA (Completed)Where stories live. Discover now