JADWA 25

55 5 0
                                    

Jindadin haske wuri da ta fara gani shi ya kara mata kwarin gwiwa sai ta fara sauri amma fa akwai gajiya ba kadan ba saurin da take yi taci karo da wani katon dutse sai da kafar ta ya fashe bata sosai tana jin jina na zuba umma sai kuka nan ta tsaya dole ta fara tunanin kodai zata tsaya nan ne don wlh ta gaji ga yunwa ka ƙishin ruwa kamar me, sai hawaye masu zafi ya fara fito mata... Ta zauna wajen nan ta ke minti goma sha biyar can ta mike tana tafiya a hankali a hankali tayi tafiyar ya kai minti 30 sannan ta fara ganin alamu wani babban tafi sai ta kara sauri kadan don a lokacin kafar ta har rikewa yake yi idan tana tafiya.

Gwada ta kar kare kai wajen tafi sai ga umma ta fadi kasa ashe suma tayi jakar da ta zuba takarce da boka ya bata yace yasa cikin ruwa yana rataye a wuyan ta nan dai ta sume.
Sai da gari ya fara waye wa sanyi iskan da ake yi ni ya fara farfaɗo da umma nan ta tashi zaune tana kuka duba tayi kafar ta ya kumbura kamar me.. a hankali ta kara kusa da ruwan taje ta fara diban ruwan cikin tafin hannu ta tana sha sai da taji ta koshi sannan ta fara ganin daidai, nan cikin ta ya fara murdawa, sai hawaye ita dai tunda Allah ya halicce ta bata taɓa wahala irin na yau ba. Mutuwa kawai ya rage tayi wlh.

Bayan minti goma da haka ta tashi ta mike ta dauko duk abunda boka ya bata tayi komai da ta gama ta fara tunanin yadda zata koma wajen nan sai kuka, yunwa koh duk yadda ake jin shi ta ji shi ba ako magana nan ta tashi ta ce bari ta fara tafiya tun yanzu saboda ta kai da wuri kar dare ya kara mata, ta fara tafiya a hankali ta bin hanyar da ta fito idan ta gaji sai ta tsaya ta huta tayi kuka kamar me fuskar ta duk ya chanza kafar ta sun kumbura ji jiki ba ko kadan ba.

Koda yamma yayi umma tayi rabin tafiyar amma duk ta fita hayacin ta ana dab da magarib umma ta fara hango bukkan boka nan ta cigaba da tafiya tana ganin wurin na mata gizo kamar ba nan ba koda ta isa ta wajen sai ga tabawa ta sheko da gudu ta rungume ta tana mata sannu yanayin da taga Aminiyar ta ya tayar mata da hankali ta tausaya mata sosai, dama tabawa ta zo mata da abinci ko da ta bata bata iya ci ba ruwa kawai take fadi shi ta bata ta sha sannan ta bata abinci koda tafara cin abincin haka ta cinye shi yasa kamar wacce bata taɓa cin abincin a duniya ba sai ta ta gama tas sannan hankali umma ya fara dawowa sannan boka ya fito yace mata zaki ji dadin wahalar nan da kika yi iya abunda zan fada maki kenan. Toh kawai ta iya cewa nan tace ma tabawa ta tace ma boka ya bata wayan ta ya miko masu waya umma ta dubawa taga missed call 34 hmm sai hankalin ta ya tashi taga na Abba da yawa gana su A'isha kai harda hidaya da take ma mugun abu ta ga nata gana mama sai hankali ya tashi sosai sai ta fara tunanin toh wa zata fara kira ma idan takira me zata ce duk tunani ya dameta a ranta can sai tayi tunanin bari ta fara kiran yaran ta, numbern A'isha ta kira, tana kira ta dauka tace ummmmmaaaaaa ina kika shiga ne ? Da karfi ta fadi maganar cikin murna da jin dadi jin umman ta ta takira ta a waya nan ta fara tunanin mai zata fada mata tace sunje wani kauye ne ita da tabawa wajen me magani saboda kafar jikan tabawa ya fara rubewa sai a ka basu shawara aka ce su je kauyen saboda alamu ya nuna bana hospital bane ciwon ma'ana an sa mata hannu aci akwai wani sihiri ko siddabaru.

A'isha ta fara salati tace toh umma baiyasa baki dauki waya ba meyasa baki fada ma Abba ko su mama da kika je ningi wajen su hankali kowa ya tashi mama taje gidan su mama tabawa amma duk ba'a ganku ba kuma ba'a san wa za'a tambaya hospital ba dama yau mama tace zata je can wajen yarinyar mama tabawa taji labari dai. Abba sai kiran waya yake yi har ya fara tunanin zuwa ningi dama yana da niyya aiki ne ya rike shi sai umma tace ku kwantar da hankalin ku lafiya lau nake abunda yasa ban kira ba kafin mu tafi wayata ta dauke ne sai da muka je ƙauyen na basu su samun chaji su suka kunna mun waya kuma Ni bance su kunna ba Ni ma hankali na na wajen ku wlh. Nan A'isha yace toh yaushe zaki dawo tace gobe yanzu zan kira mama da Abba duk nayi masu bayani tace ya kamata kam nan ta tambaye su su Fatima tace sunje islamiyya suma hankali su ya tashi sosai amma idan sun dawo zasu kira ki. Toh tace kawai ta kashe waya

Sai ta fara tunanin toh mama zata kira ko Abba nan ko ta kira Abba ringing daya ya dauka sai ajiyar zuciya take yi ta fara mashi bayani, tana kuka tana bashi hakuri sosai duk bayanin da tama A'isha haka tama Abba yace gaskiya hankali ya tashi gobe shi da kan shi zai zo ningi ya dauke ta. Tace ba matsala Allah ya kai mu.. Haka ta kira mama ita ma haka ta fada mata kamar yadda ta fada masu tace yanzu zasu dawo. Mama tayi addu'a tace Allah ya dawo dasu lafiya

****
Haka boka ya tashi ya bata wasu magani yace ta yi kokarin ta zuba ma Abba a aminci kuma tayi hayaki dashi a dakin na kwana biyu amma sai ranar kwanan ta.

Haka ta karba tace idan ta koma zai ga sako dama kafin taje kwanan daji ta bashi dubu hamsin, nan suka hada kaya lokacin duhu yayi suka ta tafiya har suka fito dajin umma ba karamin jiki taji ba koda suka fito bakin hanya nan suka samu mashin inda ya kai su ningi koda suka isa kowa ya wuce gida koda mama ta ga umma sai da ta gane cewa tabbas akwai wani abu domin taga yadda jikin yar tata tayi ga kumburi ga kafar. Nan ta tambaye tace hatsari suka yi ita da tabawa amma ita babu abunda ya same ta ita ma baki wani katon rami mashin ya wurgata tashi ta kama mulmula har ya kai ga yaji wannan rauni mama ta tausaya mata harda baba da yaji wannan labarin nan yace ta kira mijin ta fada mashi haka ko tayi ta fada ma Abba ji dai dama hankali shi bai kwanta ba yace gobe dole yazo ningi da kanshi idan rai ya ke.

Nan mama ta sa mata ruwan zafi misalin ƙarfe goman dare tayi wanka ta gasa jikin ta ta kawo mata abinci taci sannan ka kira wata nurse tayi mata allura tasha magani umma sai bacci wahala koda asuba yayi bata iya tashi ba kamar gawa, sai mama ta kyaleta har Abba ya ta kiran wayan ta sai dai mama ta dauka tace mata mashi anyi mata allurai jiya kuma tasha magani bacci take yi har yanzu yace dama zai taso ne da misalin karfe 11 na safe tace ba matsala tasan kafin lokacin ta tashi yace toh suka yi sallama ya kashe waya.

Koda suka gama waya mama ta tashi taje ta dama kunu ta aiki yarinya makwabta aka sawo mata kosai ta sa ma umma ruwan zafi har tabawa ta zo duba umma sannan lokacin ne ta tashi taje tayi wanka mama ta lura da bata yi sallah sannan ta mata magana umma taje tayi sallah asuba kenan nan mama ta fara ma tabawa sannu ashe abunda da ya faru kenan, nan ta san Aminiyar ta ma mama karya kenan duk abunda mama tace tabawa tace ai hakane.
Koda umma ta idar da sallah suka karya da tabawa duka harda baba su umma anji dadin jiki da har inda kafar ta ta fashe anyi mata dressing inshi ansa bandage da cotton wool an rufe wajen.

Suna cikin cin abinci sai suka ji sallaman Abba nan aka amsa aka bashi izini ya shigo sai ga radiya da gudu ashe da ita yazo don ita tana son zuwa su A'isha ne yan gayu nan aka fara gaisuwa duka sai suka gama Abba ya tausaya ma umma ya yadda yaga face inta radiya ko harda kuka, nan umma tace ai ita taji sauki ba abunda yake damunta ta daina kuka. An zauna anyi fira Abba ya ciro kudi ya bama tabawa yace aka cikin sayen maganin mara lafiya taji dadi sosai tayi godiya shima baba ya karama ma Abba godiya sosai da hidimar da yake masu yace ai ba komai daga nan dai suka fara shirin tafiya gida sun shirya tsab umma ta kwashi kayan ta duka suka wuce waje nan suka yi sallama dasu mama da baba sai lokacin ita ma tabawa tabar gidan bayan sunyi sallama suma suka wuce sai bauchi.

Suna isa gida su A'isha da ma'aikatar gidan suka fito harda hidaya suna mata sannu dun tun a hanya Abba ya kira hidaya ya fada mata cewa umma ta suna arziki fa sosai. Nan suka ta mata sannu amma umma ko kallon hidaya bata yi sai cewa tayi a zuciyar ta zaki ci ubanki wlh.

Koda aka gama wannan umma ta tura ma tabawa wasu kudi tace takai ma boka, kuma tasa ido tana jiran taga mai zai faru sai ta tuna da boka yace sai hidaya bata da tsarki abun zai fara aiki.

Ranar da Abba yazo daki umma ranar girkin ta ya zagayo haka koh tayi hayakin kuma ta sai maganin da boka ya bata cikin abincin.

Suna zaune yana yana cin abincin suka ji wani ihuuuuuuuu daga waje mai riktar wa koda Abba ya sheka da gudu ya bude kofa ya fita ita ma umma bayan shi ta bi yayi daidai da lokacin kowa ya fito don jin wannan ihun. Hidaya ce tsaye babu kaya daga ita sai bra sai pant kanta a bude jikin ta rawa yake tana turo ido tana kallon su kamar ba ita ba.

Tashin hankalin da ba'a sa mashi rana hauka tayi ne koko me nene jadwa sai kuka tayi cikin muryan tausayi duk wanda yaji sai ya mata kuka..

Lokacin ne Abba ya juya zai bar wajen kowa ya bishi da kallo nan jadwa tabi shi tana Abba Abba Abba baka ga halin da mommy take ciki bane ??? Abba ina zaka je Abba ka fada Mani me ya samu mommy haka ? Yanzu fa muka gama fira da ita Abba Abba tana binshi yana tafiya bai juyo ba...

Ma'assalama! ❤️🦋
Unedited... Ignore mistakes
Vote and comment pls
Next chapter coming soon In'sha'Allah
Your khads ❤️❤️

JADWA (Completed)Where stories live. Discover now