JADWA 21

64 5 0
                                    

Assalamu alaikum warahamatullah wabarakatuhu y'all
Going through this book 'jadwa' I've seen lots of mistakes which are typing errors 🥺 please bear with me In'sha'Allah if I'm done typing the book I'll kindly go back and edit it.. so let's go like that okay??

Please you guys should vote and comment after reading it could really means lots ☺️

***
Nan hankalin ta ya tashi jini ko sai zuba yake yi kamar su ruwa koma wa tayi ta bude kofar toilet ta fito bedroom zuwa tayi ta dauki wayan duk a lokacin jini bai dai na zuba ba, ta ma rasa mai zata yi, aiko ta na daukan waya lokacin sai numbern zainab ta kira, kira daya biyu sai ga shi ta dauko aiko nan ta fara magana a lokacin ma har ta fadi kasa,muryan ta ma baya fitowa amma zainab naji Maganar ta ciki ciki, nan tace mommyn jadwa kiyi magana lafiya kuwa lafiya sai wayan ya yanke.. kaii! Ina ba lafiya Nan zainab taje da gudu dakin mijinta ta na fada mashi abunda ke faruwa ta bashi labarin komai kuma tace mashi ba lafiya don Allah ya dauke su, ita da jadwa aje a duba mommyn ta ko lafiya yace ba matsala su shirya..
Ita ko hidaya a lokacin ta suma, da isar su haka suka garzaya part in hidaya kasancewa dare ba wanda suka gani ko masu aiki kowa ya nastu da gudu har zainab na gudu mijin ta nace mata tayi a hankali ita ko jadwa sai kuka tayi suna isar suka wuce bedroom straight yana yin da mijin zainab ya ga hidaya sai yasa ya fita yana salati, zainab da jadwa sai kuka suke yi sun rasa abun yi, jadwa na kusa da kanta sai kuka ta ke tana fadin dan Allah mommy ki tashi mommy ki tashi.
Koda mijin zainab ya fita da ya rasa abun yi shi sai ya kira Abba yana fada mashi abunda kenan.. nan hankalin Abba ya tashi yace toh me ake jira da ba'a kai ta hospital ba? Ko kuna so ta mutu ne? Nan yace dan Allah su maza su kai ta hospital, dama gobe jirgin su zai tashi.
Ai ko haka ya koma ya kira zainab yace taje side in masu aiki su zo da ita su taimaka mata su gyara jikin ta, sai su kai ta hospital ya kira Abban jadwa shi ya bada umurnin haka, ita kuma jadwa ya ja ta suka je parlour yana lallashin ta..
Da gudu zainab ta wuce part in masu aikin gidan tafa knocking nan suka bude take fada masu abunda ke faruwa, suma cikin tashin hankali suka rufe kofa suka ce suje.

**
Duk wannan abun da ake yi umma da yaranta basu sani ba, suna can suna sharan bacci, don wannan abun misali karfe 11:11 ne.
Suna isa dakin suka dauke ta su da zainab duka gyara mata jiki suka chanza mata kaya amma kamar gawa, duk inda hankali zainab yake yayi mugun tashi don ita a tunanin kilan mommyn jadwa tayi barin ciki ne amma ganin da tayi sun dauke ta su wanke mata jiki sun chanza mata kaya ko motsi bata yi yasa suka fara tunanin ko dai babu rai a jikin ta ne, lantana kuka ta fara yi dauko sauran idon su ya cika da hawaye.. koda zainab ta fito taso ta fada ma mijin halin da suka ga hidaya acikin amma sai tayi shiru ganin jadwa kusa da shi.
Nan ta fada mashi sun gama gyara mata jikin, nan ya tashi ya barta da jadwa yace ta koma su fita da ita su wuce hospital bari yaje ya dauko mata kusa da dole, don saboda tashin hankali mai gadi da ya bude mai gida suna shiga ya tsayar da motor duka suka fita cikin tashin hankali ko da zainab ta koma ciki haka suka fito da hidaya, suka wuce da ita suka sata a motor, nan jadwa ta rika kuka mai sa zuciyar mutane cikin tashin hankalin.

****
Nan lantana ta jawo ta tana bata baki da tayi hakuri mommyn zata ji sauki kuma zata farfaɗo, nan suka shige motor dukkan su, suka wuce hospital.
Da isar su hospital aka wuce da ita emergency room aka fara aiki a kanta..

Karfe daya sannan doctor aka samu kan mommyn jadwa lokacin da farfaɗo, nan nurse ta fito ta ke fadi Alhamdulillah ta farfaɗo sai duka suka hada baki suka ce za mu iya shiga cikin su ganta? Nan tace eh kai tsaya ta wuce war ta, koda suka shiga haka suka ganta sai motsi take yi suna mata sannu amma sai kallonta su take yi kamar bata taɓa ganin su ba. Hmm zainab tace ma mijinta ya je ya tambayi doctor meke faruwa ne meyasa meta yace toh suje tare ita ma jadwa tayi farin cikin ganin mommyn ta ta farka, amma yadda ta gani tana yi ne sai hankali ta ya tashi da zata bi zainab amma suka ce sun zuwa.
Ko da suka isa office in doctor lokacin zai hada kaya ya wuce gida. Nan ya basu wuri ya su shiga, sun zauna ya fara masu bayani kenan a lokacin Abba ya kira doctor in don yata kiran numbern su bai samu duka da na zainab da mijinta ita na jadwa ya kira har ya gaji ba'a dauka ba don ita jadwan barin wayan ma tayi gidan zainab ta manta da wani waya, ko da ya kira umma yaji ko tasan meke faruwa shiru Baga dauka ba kasancewar dare ne shiyasa yayi tunanin tana bacci kilan bata ma san abinda yake faruwa ba nan ya yanke shawara bari ya kira daya daga cikin doctors in hospital inshi yasan dole tabbas nan zasuje yana ko kira sai doctor ya dauka a lokacin su zainab na ciki nan ya fara tambayan shi, yace Alhaji ya ta farfaɗo kuma Alhamdulillah sauki ya fara samu, nan yake tambayen shi meke damun, yace yanzu ya kira su zainab ya masu bayani sai yace ok suna kusa da kai kenan sai yace eh yace basu waya nan ya mika ma mijin zainab da waya,ya kai a kunni, nan yake ce masu duka numbern baya shiga suka ce cikin rudani suka fito shiyasa wayan su duka suna mota, nan yace toh yanzu dai ance doctor zai maku bayani koh? Sukace eh yace toh kusa handsfree Ina so naji. Toh suka ce zainab ta karba tasa. Nan ya fara bayani..

JADWA (Completed)Where stories live. Discover now