JADWA 48

52 3 2
                                    

Yadda su A'isha suka natsu suka kwantar da hankali su suna karatu abun na burge Abba

Malamin da ke koya masu karatu ya nuna yana son Fatima, bai sha wahala ba ta amince mashi don ita ma tana so tayi aure.

Kuma yana da kyau ga kirki uwa uba ga karatun Alqur'ani.

Koda ya je ma Abba da maganar ba karamin dadi yaji ba yace ai kam ya turo manya shi a hada su tare da kaunar ta radiya shi kam yaji dadin hakan.

Zaro ido yayi yana tunanin shi yanzu ai ko ya turo manyan shi bai abun aure fa sai dai zuwa gaba sai dai yace a masu baiko duk wanda zai neman ta yasan tana da tsayayye.

Abba ya lura da doguwar tunanin da ya keyi yace mallam hussain ya dai naji kayi shiru ? Yace a'a abba ba komai zan turo manya na In'sha'Allah.

Mallam hussain ya koma gida ya sanar ma kawun shi yaji dadi yace zasu shirya suje amma ya fada masu shi fa sai dai ayi masu baiko don aure ba yanzu ba tukun.

A ranar da suka ce haka suka shaida ma Abba, Abba yace babu komai ya bada sadaki kawai ya isa haka.

Abba yasa mallam hussain basu da karfi sosai shiyasa a ran shi yace zai bashi harda wajen zama saboda duk wanda yace yana son naka ya gama maka komai.

Wani abu da Abba ke yi bai taba yin abu kai tsaye sai ya nemi hidaya shawara. Ita kuma mata ce ta gari bata taɓa hana shi yin aikin alkhairi ba, sai dai ma ta kara mashi ƙwarin gwiwa.

Bayan yayi shawara da hidaya tayi murna sosai da jin abunda ya fada tana ta zuba mashi godiya da sa Albarka.

Ya kira kawun Mallam hussain ya fada mashi ya ba ma hussain kyautar gida kuma sadaki kawai zasu karba. Kawun mallam hussain sai zuba godiya yake yi. Yana murna, koda suka yi sallama Abba ya kashe waya da sauri ya kira Mallam hussain yace yaro ka samun surukin arziki da can kowa ya san shi da kyautata ma al'umma.

Mallam hussain sai murmushi yake yi yace kawu mai ya faru? Yace wlh ya baka gida kuma sadaki kawai zaka biya. Ba karamin murna Mallam hussain ya yi yace kawu bari na kira na mashi godiya. Kawu yace wannan ya wuce godiya ai anjima da magance za mu je da kai da sauran kawun nan naka muje kudi kam..

Yace toh kawu Allah ya saka da alkhairi kuma yace amin alaramma. Sai yayi murmushi.

Aran shi yace hakika yayi dacen mata da surukai na gari. Alhamdulillah duk ya yaba da Fatima da na tsuwar ta.

Koda radiya taji labarin auren Fatima da mallam hussain ba karamin dadi taji ba don mallam hussain mutumin kirki ne kuma malami ga addini taji dadin da Allah ya bata shi a matsayin miji gashi har za'a hada auren su addu'a take ma aisha Allah ya kawo mata nata ita ma.

Jadwa ta cigaba da karatun ta duk da bata zama a Bauchi sun koma Abuja, Dr fahad ya cigaba da aikin shi a hospital inshi kuma tare da harkokin business inshi da yake yi na kasashen waje, amma duk da haka kulan da Aunty ke mata da mommy da sauran yan uwan dr fahad ba gaskiya ba ne kullum sai sun kira ta don jin lafiyar ta.

Sun saba sosai da matan Sultan ummeeta, sosai suke shawara tare kuma nasu yazo daya sai dai ba area su daya amma kusan kullum suna tare ga ayyan ma tare suke zuwa schl da jadwa amma idan Sultan yake zama. Shi zai zo da mota ya dauke ta su wuce watarana kuma mai gida da kanshi ya kai ta. Ga Aunty Zainab Kuma ita tana zuwa gidan ranar weekend tana taya ta fira kasan cewa ma tana dauke da tsohon ciki shiyasa take zuwa tana rage mata wasu aiki.

Koda taji an tsayar da ranar auren radiya ba karamin dadi taji ko don ta koma ta kara ganin mommyn ta.

A kwana a tashi ba wuya yau saura kwana biyu bikin Fatima da radiya. Angama shirin komai baki na ta zuwa, mama dai jikin tsohuwa sai godiya Allah da ta tuna da 'yata umma sai da tayi kuka, yau gashi za'a bikin biyu daga ciki babu ita.

Jadwa ta shirya sir fahad zai kawo ta ita dai Aunty zainab baza ta zo ba saboda month in haihuwar har ya wuce. Abba yace ta tsaya kawai tunda daga daurin aure sai walima za'ayi.

Mommy cikin ta ya tsufa ita ma amma dai 7months ne bai kai 9months ba but cikin ya fito sosai.

Baki sun cika gida harda su jadwa ta iso, ganin mommyn ta da ciki yasa take ta murna ita ko hidaya duk ta kasa sake wa, A'isha ko su suku suku take don ita ma Allah yasa ni tana son auren nan gashi kannin ta zasuyi aure su barta gida ita kade sai da hawaye ya zujo mata a fuska tayi saurin sharewa.

Abba ya gayyaci mutane yan uwa da abokan arziki ciki harda wani babban abokin shi da suka yi zama a Lagos, lokacin da aka yi bikin jadwa baya kasa amma yace idan wani hidima ya kara tashi nashi idan yana gari ya fada shi zai zo.

Ai ko Abba ya fada mashi da ya tashi zuwa harda babban dan shi yazo, sun iso Abba ya masu ma sauki, nan yake ba amma labari, don Abba ya tambaye shi ɗan nashi yayi aure ne yace ai yayi shekara biyu da suka wuce sai dai Allah yayi ma matar shi rasuwa ita da yaron da ta haifa wajen haihuwa, Allah sarki Abba ya fada yayi jimamin abun.

Sannan yake cewa gashi har yanzu yaki mai da hankali yayi aure, Abba ya tambayi yaron yace hakane ? Yayi murmushi Abba ya mashi nasiha mai shiga jiki kuma yaji dadin nasihar.

Ana gobe za'a daura aure abba yake tunanin koda ya hada ahmad yaron abokin shi da A'isha ? Shi kade ke wannan tunanin sai yaje ya samu mommyn jadwa da maganar tace toh shi Ahmad in zai amince kuwa ita A'isha na kula tana cikin damu kuma nasan dun yan uwan nan nata ne da taga zasu yi aure su barta wata kila ta amince amma shi Ahmad in zai amince? Abba yace toh zan yi shawara da mahaifin shi idan zai amince shima sai a nemi shawarar shi in har an dace kinga shikenan.

Tace toh Allah yasa a dace. Ameen ya fada yace maman baby sai tayi murmushi.

Da karfe goma na dare Abba suna zaune da wasu abokan da suka karbi gayyatar shi suna fira bayan sun gama cin abinci biyu sun tashi sun bar parlourn suka ce zasu shiga gari su zagaya. Daga abokin Abba Alhaji Abubakar sai Abba shi kanshi Ahmad yana cikin gari dama yana da friends a bauchi.

Abba yazo mashi da shawarar yana son hada ahmad da A'isha sosai Alhaji Abubakar ya ji dadin wannan zancen, amma sai dai yake tunanin ko zai amince shi kuma gashi abba ya nuna yana so a hada su gobe sai abba yace toh ko dai ba a hada su tare ba idan ya amince yace toh bari idan ya dawo gida zai kwanta zai kira shi ya shigo sai suyi magana yace toh yayi kyau ya gode.

Ma'assalama ❤️
Unedited chapter, ignore mistake pls..

Next chapter coming soon In'sha'Allah and the novel is about to end pls comments and vote..

Yours khads 🦋🦋



JADWA (Completed)Where stories live. Discover now