JADWA 49

51 5 0
                                    

Koda Ahmad ya dawo dare yayi amma bai wuce kai tsaye dakin da aka bashi ba sai da yaje suka gana da mahaifin shi.

Maganar da yaji daga bakin mahaifin na shi akan yana mai sha'awar auren A'isha, a wannan karan bai musa ba yace amma yana son yaga A'ishan su gana kuma gaskiya sai sun fahimci juna sannan bai ce komai ba saboda yasan miskilin yaro ne kuma ga taurin rai.

Alhaji Abubakar bai musa ba yace ba matsala Allah ya kai mu gobe da safe, yace Ameen ya wuce ma sauƙin shi yana tunanin toh ita wannan wata irin yarinya ya ce da ya amince kai tsaye duk dade yace yana son ganin ta amma zuciyar shi ya amince da ita tun kafin ma ya ganta.

Da safe Abba ya tashi ya shiga part in su mommy su jadwa da sauran yan uwa duk sun tashi, amare ma na dakin, sai A'isha da ke gefe daya, yace ta biyo shi sama ta same shi toh tace toh to bi bayan shi.

Da safe dama Alhaji Abubakar ya kira Abba ya fada mashi yadda su kayi da shi dan shi wato Ahmad kenan amma baya tunanin ko ya amince zai yadda a daura auren shi yau, Abba yace ba matsala ya dai amince in.

Ko da Abba ya ce ma A'isha ya mata miji ba musu ta ce Abba duk abunda kayi nasan baza ka cutar da mu ba na amince da zabin ka. Sosai cikin rai Abba yaji dadi yasa mata albarka yace anjima bayan daurin aure za taje su gana da Ahmad in tace toh Abba. Yace yawwa za ki iya tafiya Allah ya maki albarka tace Ameen Abba. Ta mike kai tsaye ta wuce ta sauka kasa.

Da kallo kowa ke binta da ta sauko amma yadda suka ga fuskar ta da alamar farin ciki yasa suke tunanin toh me Abba ya fada mata haka.

Ita aran ta ji take yi lallai Abba ya mata gata sosai don tasan Abba bazai taba zaba mata miji wanda ba nagari ba dama tana cikin damuwa yan uwan ta zasu wuce gidan aure su barta sai gashi Allah ya yi nashi ikon.

Kallon su yake yi kamar yadda suke kallon ta mommy ne kawai ta son komai ko jadwa bata sani ba ballantana sauran. Kuma babu wanda ya tambaya ita ma haka bata ce masu komai ba.

Karfe 11 am za'a daura aure goma na yi A'isha ta shirya tasa jilbab inta sky blue ya mata kyau sosai kasancewar ta doguwar mace ce mai diri Masha Allah tayi kyau sosai ta light makeup da ke face inta.

Kai tsaye ta wuce masaukin Ahmad tayi sallama amma gaban ta na faduwa kuma babu wanda ta fada ma wa, hmm kawai take fada a ranta.

Toh shi wannan Ahmad in ko zai so ta ? Take tambayar kanta minti uku tayi ta kara sallama hade da knocking.

Wannan time in yazo ya bude yace ya amsa sallamar, ganin ta yasa ya yayi mutuwar tsaye wanda ita ma shi tayi, sai dai yayi minti uku sannan yace shigo mana sai ta shigo ta zauna parlour shima ya zauna jallabiya ke cikin jikin sa fari.

Dashi da ita babu wanda yake ce ma wani kala, amma yarinyar ta burge shi sosai da shigar ta da yanayin surar ta da kyawun ta, kuma yasan indai a wannan gidan nan ne ba'a a taba bashi macce da bata da tarbiyya ba.

Ahmad abubakar matashi ne mai shekaru 37 kamar yadda na fada a baya ya auri matar shi ta fari yana da shekara 34 Allah ya mata rasuwa da ita da abunda ta haifa, yana da kyau da tarbiyya sai da yana da miskilan ci da taurin rai amma yana da biyayya sosai ga iyayen shi asalin su yan kano ne aiki ne amma shi yana aiki a part Harcourt ne marine officer ne.

Shiru yayi yawa babu wanda yake ce ma kowa kala ya juyo yace ya sanar malam ne, kanta a kasa tace A'isha yace Masha Allah sannu A'isha suna mai kai kyau kamar yadda mai ita ke da kyau sai ta ɗago fuska ta kalle shi tayi murmushi shima murmushi yayi a takaice sai ya gyara murya ya fada mata labarin shi harda auren yayi ya rasa matar shi kuma ya sheda mata yana son ta don bayan mutuwar matan shi an ta kawo mashi mata amma babu wanda ya taba jin shi a ran shi kamar ita da ya gani yanzu kuma yana so su fahimci juna kadan sai ayi maganar auren su tace toh Allah ya jikan su
Yace Ameen.

Kowa yayi shi sai yace kai ma ki bani labarin ki mana gashi kuma kamar ban maki ba sai tayi saurin ɗago wa tace kayi mana ai ba macce da za ta same ka tace baka mata ba sai tace Abba ne mahaifin ta amma ba shine ya haifa ta ba amma ya mata gata sosai wanda Allah ne kawai zai biya shi, ya dai auri mahaifiyar ta ne ta da bashi labari a takaice kuma ya gansu.

Agogo ya duba yace bari yayi saur ya shirya ya wuce wajen daurin aure sai suka yi exchanging contacts, dadi fal a ran A'isha kamar an mata kyautar Makkah.

An daura auren Fatima da hussain sai radiya da Adam Alhamdulillah. Abba ya shirya walima a gidan shi, yan uwan ango da nashi kanshi Abban harda wasu dangin mama sun zo daga ningi..

Jadwa tayi kyau sosai shigar da tayi amma a ranar zazzaɓi ya taso mata kamar me, har tace baza ta fita walima ba radiya ta nuna rashin jin dadin ta haka ta lallaɓa ta fita, angama walima anci an sha an fara pictures Adam na kallon jadwa sai ya tuna da ranar da ya ganta a airport ita da Abba duk abun na dawo mashi a rai yace Allah sarki ashe zai sake ganin wannan baiwar Allah ya dade yana tunanin ta kuma yana mafarkin ta. Yace ko ba komai ya auri yar uwan ta amma ya so jadwa a ran shi yayi saukar neman ta Allah sarki ya fada a ran shi.

Mommy bata samu fitowa ba saboda jikin mai ciki yau ciwo gobe lafiya.

Abba da Alhaji Abubakar sun ji dadin yadda Ahmad da A'isha suka amince da junan su gashi zasu kara zumunci.

Taro ya watsi an kai amare gidan su A'isha a lokacin ne da taje gidan radiya take bata labarin komai, ba karamin dadi radiya taji ba kuma tayi murna da sanye Alkhairi. Ita ma Fatima da taji labarin tayi farin ciki sosai.

Bama kamar mama da labari yazo wajen ta sai sa albarka take yi.

Jadwa kan jiki ba kwari har Dr fahad yace zai zo ya dauke ta shima aiki ya rike shi ranar da Abba ya dauke ta ya kai ta hospital da kanshi aka sheda masu da tana da ciki ba karamin murna yayi ba.

Ita kan mommy da aka fada mata tayi murna amma ta komai don dama tasan da kyar hakan bai biyo ba.

Cikin jin dadi jadwa take yi ma Dr fahad albishiri da dare yayi, har sai da zabura yace Masha Allah ai dole gobe nazo bauchi na daki matata nayi jinya..

Sai murmushi take yi tace ita anan zata tsaya sai ta haihu Dr fahad yace ai Abba ba zai yarda ba ma. Sai suka yi wasa da dariya ya kashe waya bayan sunyi sallama.

Ma'assalama🦋🦋

Unedited chapter pls ignore mistakes

Next chapter coming soon In'sha'Allah

And it's the last chapter..

Pls vote and share...

Yours khads🦋🦋❣️

JADWA (Completed)Where stories live. Discover now