JADWA 11

69 3 0
                                    

Umma na shiga harabar Company ta hango Abba zaune da masu mutane suna magana da sauri sauri ta kara shiga ta je daidai wajen. Zuwan ta yayi daidai da lokacin da mutanen suka ta shi wuce suna ma Abba sai anjima, nan takai ta fara zuba ma Alhaji Yusuf gaisuwa (Abba) kamar wata zabaya, dai amsawa yake yi shi dai. Dagana yace ta zauna shima ya zauna tana zaune kam mat shi kuma yana saman chair, sai ta fara kirki mashi bayani na karya da gaskiya wai ita don yaji tausayin ta da kyau da kyau ya bata kudi masu yawa hmm.

**Wallahi Alhaji da farko dai ni yar ningi ce yana da yara hudu mata duka baza su wuce shekara goma sha biyu zuwa uku ba, mijina ya gudu ya barmu, tunda muka taso bai san cin su da shan su ba ni ce ke wahala ga kudin makarantar su gashi Ni ina son yara da karatu amma shi sai yace ai yara mata ba amfanin karatun su Alhaji haushi na ma yake ji saboda duka mata na haifa daga karshe dai guduwa yayi ya barmu dama shagon kayan provision yake dashi kasuwa amma bashi da kowa sai wani dan uwan shi guda daya, shine da yasa aka bashi aure na saboda shi ya daidai garin an san shi amma duka ba yan gari bane yan kasar chadi ne. Iyaye na basu so bashi ni ba amma Ni ganin na daidai gida banyi aure nace sai shi haka suka yi hakuri suka bashi ni, a haka akayi aure su kuma basu da wani karfi. Tun ina sana'ar kulle kulle na gida har ya kai ba mu da komai saboda ciyarwa hmm yanzu haka dai har kayan daki na komai na sai da surutu duka daga karshe dai saboda ba mu da komai sai na zaɓi sana'ar bara da shi muke ci muke sha kuma makarantar yara ya tsaya shine nace bari nazo ko Allah zai sa ka taimaka mani kamar yadda ya taimake ka yasa kake jin tausayin bayin sa nima ka taimaka mani ko sa'ana fara saboda ko kudin haya da kyar nake biya don bashi da gida kuma wannan karshe watan mai gida yace idan bamu biya ba sai ya mana korar kare saboda na shekara daya da rabi yake bin mu ga wani shekara ya kusa karewa. Sai kuka umma kamar an bude faffo.. 😭

***Abba yace "yi shiru baiwar Allah duk naji labarin ki babu dadi gaskiya kuma na tausaya maki matuka, shiyasa nake shirin bude ma matata wani babban organization wanda za'a rika taimaka ma mata masu ire-iren wannan matsalan ana basu jari kuma ana taimaka masu da shawarwari". In'sha'Allah wannan matsalan naki ta zo karshe kinji, shi kuma Allah yasa duk inda yake yana lafiya. Yanzu zan baki dubu dari biyar ki samu kije ku saya kayan abinci ku rage ma mai gidan hayan ku kudin sa kuma ki maida yara makaranta dan Allah, daga nan sai kiyi tunanin wani sana'a zaki zan baki jari sai ki fara juyawa amma yanzu ko dawo nan da sati biyu saboda zamu tafi umra Ni da iyalai na sai bayan sati biyu zamu dawo In'sha'Allah.

**Umma sai godiya har da kuka kamar wata karamar yarinya, yace mata ai wannan ba abun kuka bane karki damu Allah da ya taimake mu duka. tace "Ameen ameen Nagode Alhaji" umma ta gudu ta bar Company har ji na rawa taji ta ajike 😂 sai hanzari take yi yaje ta tare mota tayi ningi..
Da isar umma ningi ai sai ta shiga gidan tabawa ta fara mata labari taba abokiyar cin mushen ta kawar umma ce wacce duk kusan matsalan su daya na rashi amma ita bata bara kuma mijin ta na nan sai dai akwai talauci, ita ma tana da yan mata uku amma duka sunyi aure sai kulla masu mugun hali take yi a gidan mazajen su saboda tana da mugun son abin duniya duk malaman da ke ciki gari da na daji tasani. Haka umma ta fara bama tabawa labari yanda suka yi da Alhaji har da bata labari tayi na aikin da yace matar shi zata fara na taimakon mata da kudin da ya bata da kuma sana'ar da yace mata taje tayi nazari zasu je umma da matar shi sai sun dawo ta dawo, ita dai tabawa ta baza kunne sai ji take yi, hmm daga nan sai taba tace aike wannan aikin sai ke ki fara shi badai wata ba kuma da wannan kudin zamu je wajen boka naira baza ki ci ba dashi za'ayi maki aiki ki mallake Alhaji sannan ko zama matar shi, dani da kai duka duk mu fita cikin taulaci. Sai dariya suka hada baki suna yi kyalkyalkyal!! Kake ji umma tace "dadi na dake tabawa baki da kyau" tabawa tace "lallai ai yanzu duniya ya wuce wasa, shi bada ya ga mata yana rawar jikin taimaka masu ba toh yayi ai da kudin shi za'ayi mashi aiki" a haka suka gama tattaunawa yanda zasu yi su samu kan Alhaji da wajen bokan da zasu je hmm, daga baya umma tayi ma tabawa sallama ta wuce gida ta bar mata kudin..

*** Da isar umma gida yan matan ta suka fara murna amma sai da sheda masu cewa ita bata samu Alhaji ba ba waya nan tana zuwa ace yanzu suka fita, A'isha ta bude baki tace kash! Umma kodai kin taushe hannu ne, tace A'a amma ance in dawo bayan sati biyu zasu je umma, Radiya tace toh umma Allah ya kai mu.

** Yau ne tabawa tace ma umma za'a shirya ake wajen boka, da sauri ta shirya tace ma yaran ta zasu je biki ita da tabawa a wani kauye kusa dasu, haka suka mata sai ta dawo da Allah ya tsare. Tace "Ameen"
Tana isa gidan tabawa ta tarar da ita ta shirya tana jiran ta, haka suka kama hanya suka je suka hau mashin su biyu sai cikin wani kauye, ga nisa ga shi daji ko da mai mashin ya sauke su a garin haka suka ta shiga cikin daji sai nisa har umma ta fara gajiya tana ma taba magiya, can tabawa tace ai ba'a samun abu mai kyau cikin sauki haka zaki yi hakuri. cigaba da tafi suka yi jim kadan sai kashi su fara hango wani rumfar bukka da baki ƙyalle jikin bukkan. Sai can suka hango wani mutum da baki kaya, can tabawa ta fara cewa gara dai gara dai. Daga masu tsawa yayi sai da umma ta tashi faduwa ita taba ta saba, nan yace masu nasan bukatun ku Alhaji yasuf kuke so ku mallake wannan ta aure shi sai abinda take so zai yi, sai daga kai take yi tabawa ita ko umma sai mamaki take yi tace lallai wannan bokan karshe ne aiki zai yi kenan nan umma ta fara jin dadi.. boka yace "yanzu aiki zai yi wuya saboda yana kasa mai tsarki, sai dai idan ya dawo sannan ke ya nuna umma zaki bar sallah na wata daya, zaki samo gashin kan shi, zaki samo takalmin shi daya, zaki bama aljannun jini alade idan babu jini alade zaki kawo kudi miliyan 1 daya a saya masu.. nan umma ta zaro ido, ya kara daga masu tsawa yace ku wuce Ni bana maka biyu.. nan takai tabawa taja umma suka wuce sai sauri suke yi ba wanda yace ma wani ƙala sai da suka bar dajin nan umma tace ina zan samu miliyan daya tabawa, tace ni barin sallah ba ya dame ni bane tunda dama ba wani sallah ma nake yi ba amma ina zan samu dubu dari biyar in hada kai miliyan daya na Bama boko, sai tabawa tayi tsaki tace wajen shi mana bari dai ya dawo ai sai kije kice kin gama nazari zaki sana'ar shinkafa zaki rika dauko buhuhunan shinkafa kina sayar wa wanda kinga zai baki jari, kice shi kawar ke yi kuma akwai alkhairi sosai idan ya baki sai mu dawo nan. Tace haka ko za ayi. Da wannan tunanin suka iso inda zasu hau mashin haka suka hau mashi suka koma ningi koda suka isa dare yayi kowa yayi gida. Umma na shiga yara suka fara murna daga nan suka dauki mata abincin da ta bari ayi ta fara ci, haka ta cinye tace su karo can Fatima tace umma kamar ba wanda taje biki ba nan tace ina ruwan ki shegiya nan suka fara dariya.. tana gamawa ta hau kan gado ta ce su sa mata ruwan wanka ba zance sallah tunda tabawa tace ai doka zai fara aiki ba zan cen yin sallah har wata daya kamar yadda boka ya fada. Haka ko ta dauko, sai tunani take yi yanzu zata zama matar Alhaji Yusuf ita da yaran ta zasu shiga daula.. hmm Amma kamar da wuya toh idan ta shiga ya zatayi da matar shi ita kam baza ta iya zama da kowa ba daga Alhaji ai sai yaran ta amma wannan ba wani matsala bane matsalan dai ta shiga. Da wannan nazarin ta tashi taje ta fara shirin shiga bayi..

Not edited chapter
Kindly ignore mistakes pls
Vote and comment plss ♥️♥️
Khass xo.

JADWA (Completed)Where stories live. Discover now