JADWA 45

54 5 0
                                    

Karfe 10 na dare jami'an saro na fararen kaya watau dss suka shigo da su A'isha garin bauchi, basu tsaya ko ina ba sai gidan Abba mai gadi ya bude masu gate, koda suka isa suka kira Abba yace su shigo kai tsaye guest room suka tsaya harda su aisha.

Abba ya kalli hidaya tana bacci kuma baya so ya tashe ta tunda ya ga ta fama da zazzabin kuma yace su je hospital ta ki dama gobe yace babu abunda zai hana su zuwa hospital In'sha'Allah.

Sallama yayi suka amsa koda ya gaka su A'isha babu abunda yake furtawa sai salati duk sun rame sunyi baki kuka suke yi sosai suna fadin Abba ka yafe mana yace ni ba ku mani komai ba ku zauna dai tukun, mai ya faru nan suka bashi labarin yadda Alhaji ya yaudare su yace zai fita dasu waje ya samar masu makarantar da aiki kum zai auri aisha haka dai ya wuce dasu akwa ibom ya bautar dasu kuma ya kafe su, suna bada labarin suna kuka harda na zina da yake yi dasu basu boye ma abba komai ba innalillahi wa'inna ilaihi raju'un kawai abba yake fada yace ya isa hakanan yanzu shi ina azzalumin yake ? Ya jiya yana kallon officers in, suka ce unfortunately we wouldn't meet him.. kashh!! Abba ya furta yace ai wannan mugun irin ya kamata a nemo shi a hukunta shi zan baku sake baku kudi this time around ma flight zaku bi ku je Abuja daganan ku wuce akwa ibom dole sai an koma shi ok sir suka fada ya shiga ya fita ya basu wasu kudin yace zan nemai ku nan A'isha tace Abba dan Allah ina jadwa? Ko tayi auren ? Ina radiya? Ina momyn jadwa? Fatima tace Abba dan Allah bamu waya mu kira umman mu wlh kwanan nan sai tunanin ta muke yi tana ran mu sosai..

Jin hakan sai da idon Abba ya kada kamar zai yi hawaye shi tausayi ma yaran ke bashi, nan yayi karfin halin ce masu ku bari gobe In'sha'Allah zaku gan su kunji yanzu ku je kuyi wanka ku je dakin mai aiki ta baku wasu sutura ku chanza kuje kitchen ku debi abinci kuci ku kwanta ku huta har gobe kunji? Toh suka ce don sun ji dadin yadda ya nuna kula sosai a wajen su basu da wanda ya fi shi a duniya..

***
Washe gari da asuba hidaya na sallah ya shi kuma Abba ya dawo daga masallaci da ke kofar gidan shi, tsaya yayi na minti biyar hidaya ta juyo gare shi ta gaishe shi a lokacin ta idar tasbi na hannu ta, ya amsa nan ya bata labari yace mata da su A'isha sun ta dawo da karfi ta mike tace dan Allah ? Yace tabbas suna dakin su, labarin da ya bata wanda yaran suka bashi sai da hawaye ya zubo a fuskar ta, jawo ta yayi yasa kanta kan cinyar shi yana bubbuga bayan ta kamar karamar yarinya, yace ai mu gode ma Allah sun dawo sai basu taradda da umman su raye ba kuma ko a yanzu naga nadama sosai a ransu kuma ina kyautata zaton In'sha'Allah idan sun ji labarin mutuwar umman su zasu shiryu In'sha'Allah ita kuma umma ta gode ta roke mu yafiya kuma mun yafe mata yanzu abunda ya saura mata ita da Ubangijin ta ne, amma tsakanin mu Alhamdulillah komai ya wuce umma tace hakane kam Allah ya kare mu ta mummunar kaddara  yace amin..

Kamar zai yi magana sai kuma yayi shiru ya taba jikin ta yace har yanzu jikin ki da zafi fa tace eh wlh kaina ke ciwo kuma ga jiri da ke diba na idan na tashi tsaye, yace In'sha'Allah anjima Ni da kaina zan kai ki hospital zata yi magana sai tayi shiru tace Allah ya kai mu yace Ameen.

Karfe 10 hidaya taje dakin don ta duba su amma suna baccin nan ta kira radiya ta fada mata ba ƙaramin murna radiya tayi ba tace don Allah mommy ki basu waya mu gaisa kin fada masu umma ta rasu ne ? Sai muryan ta ya chanza ya fara rawa alamun zatayi kuka. Mommyn da ta fahimci abinda ke nan tace radiya kiyi hakuri suna bacci amma yanzu zan tashe su karya kinji za kuyi waya anjima tace toh..

Kai tsaye mommyn jadwa ta bude dakin ta shiga haka ta gansu kamar gawa alamun sun gaji, amma kamanin su duk ya chanza kamar basu ba tausayin yaran ya shige ta sosai kamar zata tashe su sai kuma tace bari ta kyale su idan 12 yayi basu tashi ba sai ta tashe su lokacin ..

Ta koma daki sai ga wayan jadwa, sun gaisa take ce mata gobe zasu dawo nigeria don daga makka sai da suka je dubai tace mata Allah ya dawo dasu lafiya nan take fada mata cewa su aisha sun dawo ta bata labarin abinda ya faru dasu sosai jadwa taji abun a ranta tace In'sha'Allah zasu zo bacci dama Dr fahad yace mata zasu zo su gaishe su, sai jadwa tace ke zan kira shi nace ya barku ku huta sai zuwa gaba auren ku ko 2months bai yi ba kuce kun fara zuwa gida ziyara.. shagwabar da jadwa take yi shi tayi mata tana rokon ta da tayi hakuri. Toh tace kawai don bata san damuwa.

Karfe 12 Abba ya shigo gida don dama ya fita, a lokacin su A'isha suka fito suka shiga dakin mommyn jadwa duk nan aka hade tare.. da ganin mommyn jadwa sai kuka suka je suka rungume ta suna cewa ta haife masu, tace ta yafe masu, kuka sosai suke yi dukkan su, nan Abba ya fara rarrashin su, da kyar suka yi shiru..

Yana jin yadda zai fara fada masu abunda ya faru, ita ko Fatima sai tambayen jadwa ta ke yi tace ita ma mun cutar da ita ina take mu roketa yafiya mommy?

Ma'assalama ❤️
Plsss vote!!!

Short chapter bcos you're not commenting lol


Byee, see you next maybe tonight In'sha'Allah 

JADWA (Completed)Where stories live. Discover now