JADWA 43

87 6 0
                                    

Cikin motar radiya sai gaban ta fadu ake yi addu'a kawai take yi Allah yasa lafiya, duk tunanin umma ta ke yi da yan uwan ta A'isha da Fatima sai kuka take wanda hawaye kawai ke duba..

Yanzu haka zasu cigaba da zama inda ba'a san inda suke ba, innalillahi wa'inna ilaihi raju'un kawai take fada a cikin ran ta shiyasa ramin mugunta aka ce ka gina ta karami kar ka gina da fadi watarana ka fada ciki kai ma, yanzu ji yadda rayuwa ta juya masu yadda umma ta so ba haka rayuwa ta mata ba, ta cutar da mommyn jadwa, ta cutar Abba da ita kanta jadwa, Mutanen da suka rike mu tsakani da Allah wa'inda duk duniya ba mu da kamar su, su A'isha da Fatima da taso su zama kamar jadwa suyi aure gidan masu kudi kuma su auri dan boko mai ilimi yau gashi jadwa ce da hakan basu ba yanzu su babu wanda yasan inda suke makarantar ma sun dai, bata anka ba kawai sai taji Mallam Kabiru na cewa malama radiya mun iso fah ai da ya kara magana sannan ta dawo daka hayyacin ta.

***
Alhamdulillah Allah na ko dai maka da muka iso lafiya sannu da kokari mallam Kabiru yace yawwa.  Fita tayi daga mota tace bari ta kawo mashi ruwa gida yace A'a bashi da ƙishin ruwa sai ta gaidar mashi da mama tare da umman tace In'sha'Allah zanyi hakan.

Tana shiga gidan da sallama sai mama ta hango bakin kofar dakin ta zaune tayi tagumi kara sallama tayi ta tafiya zuwa inda mama ke zaune, mama ta tashi dasauri tace lale lale maraba maraba yan biki ma shaya gara.. Barka da zuwa Barka da zuwa, ya hanya tace Alhamdulillah tace ya amarya kuma da iyayen tace lafiya lau mama tace an watse taro lafiya tace Alhamdulillah tace ya Adamawa kuma ? Tace can ma lafiya, sai tace mama ya umma na da ji ki duk da dai ina tambayan ki a waya tace da sauki sai dai yanzu kam sai a hankali zan ce addu'a kawai za mu cigaaba da yi amma umma na shan jiki tace dazu na je asibiti ma, malamar asibiti da ke kula da ita sai ga tabawa an garo ta da keke guragu yanzu tabawa ba kafa ciwon barin jiki da ya kamata yayi sanadiyar mutuwar kafar.  Innalillahi wa'inna ilaihi raju'un kawai radiya ke fadi, sai mama tace ke tsaya ma ke ji mummunar abunda naji tabawa ke fada ma umman ki ashe ba ƙaramin ta'asa suke yi da umma da tabawa ba gashi yanzu Allah ya nuna masu abun su tun kafin barin su duniya yayi..

Zauna ki zauna ki sha ruwa kuma bari na kawo maki dan wake ki ci, radiya tace mama a koshe nike sai ta shiga daki ta dauka tabarma suka baza gefen dakin sai suka zauna, ita ko radiya duk hankalin ta a tashe yake da ji labarin mama kuma tasan karkaran labarin bazai yi kyau ba.

Mama tace jin nayi suna labarin akan asirin da suka ma mommyn jadwa ta yi rashin lafiya hauka da kuma yadda ta ke ma Abba asiri ba ya jin maganar ko wa sai ita sai inda tabawa take cewa taji labarin bokan da suke zuwa wajen shi ya haukace kuma yana da cutar HIV yanzu haka ma an daina ganin shi inda yake shawagi ana tunanin kilan yaje wani wuri can ya hadu da ajalin sa..

A lokacin ne umma ke ce tabbas wannan cutar boka ne yasa ma don akwai wani maganin da taje karba wajen shi yace sai yayi zina da ita daga karshen maganin bai yi sai gashi ta kuma da wannan cutar, suna kuka suna nadamar abun da suka aikata suna neman hafiyar juna hmm..

Radiya babu abun da take yi sai kuka daga nan mama ta jawo ta ta rungume ta tace sai kinje asibiti kinga umman ki, tabbas rayuwar nan dole mu bi ta a hankali idan ma ba mubi ta a hankali zata koya mana hankali..

Tace Ni yanzu abunda ke damuna yan uwan ki da babu wanda yasan inda suke ya kamata suzo suga yadda umman ku ta koma ko suma sunyi karatun ta natsu... Nan radiya  ba ma mama labarin yadda Abba yace zai sa ayi tracking in number su dun location in da suke zai nuna in har aka yi waya dasu daganan jami'ar tsaro zasu shiga su fita su gano inda suke yace daga nan za'aje a dauko su.. su dawo gida.

Mama tace gaskiya wannan ba Allah bamu da abunda zamu saka mashi dashi a duniya sai addu'a da fatar dace a rayuwar shi ta duniya da na lahira ya kika ya kai mutum wlh. Ba kowa bane zai iya yin yadda yake ma duk da irin cutar da umma tayi mashi amma har yanzu yana kula da mu gaskiya ya cika dan halal..

Ana radiya tace ma mama zata shirya ta je wajen umman ta mama tace toh ki gaishe ta haka ta shirya ta sa hijab ta fita ta mike sai asibitin tana cikin ta fiya sai ga kiran wayan mommyn jadwa ta dauka suka gaisa take tambayar yadda ta iso tace lafiya lau ta tambaye ta mama tace ai tana hanyan zuwa asibiti ne wajen umma amma mama na lafiya lau tace toh ta gaida me jiki da kuma mama tace In'sha'Allah suka yi sallama ta kashe waya sai tunanin irin kirki wa'innan bayin Allah take yi, tana kusa da asibitin sai ga wani random number da ta gani kamar baza ta dauka ba sai da ya kusa yanke wa ta dauko jin muryan ta gana wannan abachen nan ne mai damunta da kira tayi kamar ta kashe sai ta tuna da shawarar jadwa sai ta dauko suka yi magana lafiya lau yaji dadin Yadda ta mashi kuma ya shaida mata cewa wajen karatun Alqur'ani ne da suka yi ta burge shi sosai shine ya nemo numbern kuma idan zata bashi dama gaskiya shi bada wasa yake yi yana so yazo ya gabatar da kanshi wajen ta kuma idan sun fahimci juna ya sa manya a al'amari murmushi tayi tace kafe gwagawa gaskiya yanzu dai ina wani uzuri ne idan na rage zan kira ka yace toh ai ko da nayi murna sosai amma ki sani inda baki kira ba zan kira tace karka damu In'sha'Allah ni da kai na zan kira kamar yadda yace yawwa Allah ya nuna mana tace Ameen.

Saurin kashe wayan tayi amma sai taji ta samu natsuwa da suna wayan murmushi tayi tace Allah ka shiga al'amari na..

Sai ta kara sa asibitin mike wa tayi kai tsaye dakin da umma take ganin babu kowa kuma umma naso ta yi fitsari babu me taimaka mata gashi bata ita tashi yasa ta mike tsaye ta fara yin shi sai da radiya tazo ta taimaka mata ta kai ta toilet suka je can ta kai ta tayi fitsarin kuka radiya ke yi irin ganin yadda umman ta ta koma.

Bayan sun dawo ta zauna umma ta dafa ta tace hakika radiya kin cika 'ya nayi nadamar abun da na aika a gare ki don Allah ki yafe Mani, da na nuna maki tsana da hantara saboda Ina son yan uwan ki kuma saboda Suna son abunda nike kuma ba abunda nike so bashi da kyau amma nasani nike tura su ke ko kin kasan ce mai son gaskiya.. yanzu gashi su da nike so sun guje ni kuma sun fada mugun rayuwar da ba kowa ke son ace nashi na ciki ba sannan sai gashi ke ce mahaddaciyar al'qurni..

Yau zan gaya maki maganar da ko su A'isha basu san da shi ba, wlh Abba bai taba so na tun farko da asiri na kama shi, nan ta bata labarin duk irin makircin da suka shirya da tabawa tun farkon haduwan su da Abba suka mashi asiri, babu abunda radiya take yi sai kuka tana ce ma umma tayi hakuri komai zai wuce, tace zai wuce nima zan wuce amma ina so ki kira mani Abba zan bashi hakuri shi da hidaya har jadwa don na cutar dasu su yafe mani, nan take radiya ta kira Abba ya dauka yana mata Barka da hanya nan take bashi labarin nadamar umman ta cikin kuka ta mika mashi waya ita ma kuka take yi sosai nan Abba yace kar ta damu zasu zo har ningi In'sha'Allah ba komai a ransu..

Umma ta ce ma radiya don Allah ko bayan bata da rai kar ta fada ma kowa maganar nan siri ne tsakanin su ko yan uwan ta bata so su ji sannan idan ta samu miji tayi aure kar ta tsaya ruwan idon ta mata nasiha sosai mai ratsa jiki wai yau su umma ne ke nasiha lallai duniya budurwan wawa.

Taso ma ta bada Labarin Adaam wanda yake kiran ta amma sai taga basu cikin natsu daga ita har umma..

Haka radiya tace zata je ta saya abinci restaurant ta kawo ma umma kuma ta kwantar mata da hankali tace kar ta damu In'sha'Allah su A'isha zasu dawo ta bata labarin da ta ba mama na wanda Abba yace idan angama bikin jadwa zai sa ayi tracking in number su a gano inda suke a nemo su, su dawo gida.

Da haka hankali umma ya ɗan kwanta ita ko radiya ta kwashi cooler ta fice tana tafiya tana magana ita kade tana mamakin da ganin karfin halin irin na umman ta da tabawa muguwar Aminiya tace lallai Allah ka kare mu da fadawa cikin bala'i tace Allah na gode maka da umma zata roki yafiyar wa'innan mutanen kafin ta koma gare ka Allah ka yafe mata kurakuran ta ya Allah da mu baki daya...

Tana kuka tana magana ita kade tana tafiya ta isa restaurant ta gama sayan abinci sai ga jadwa ta kira ta sun gaisa sosai ta mata godiya akan hidimar da ta mata tace haba aunty jadwa har sai kin gode mun tace ya ai dole ya jikin umma tace da sauki kawai tace ki gaishe ta tace zata ji kina shan amarcin ki tace eh wlh 🙈😂 tace yayi Allah ya kara hada kan ku tace Ameen suka yi sallama ta ta kwashe cooler inta ta mika kudi ta kama hanya zata koma asibiti..

Ma'assalama! ❤️🦋
Unedited chapter pls ignore mistakes
Don't forget to vote, comment and share pls
Next chapter coming soon In'sha'Allah
Stay tuned!!!

Enjoy!!❣️

Love you XOXOXO

Khadsss 💗

JADWA (Completed)Where stories live. Discover now