JADWA 47

56 6 0
                                    

Ko da suka iso bauchi ba karamin jin dadin ganin junan su suka yi ba, sunyi kuka har sun gode ma Allah

Radiya ta tausaya ma yan uwan ta sosai ganin yadda suka koma wai ma haka don sun yi kyau kenan.

Kwana biyu mama tayi gidan Abba ya sa da yan aiki biyu aka kai ta gidan.

Gida yayi kyau Masha Allah kamar bana tsohuwa ba ya sa mata komai na more rayuwa ko mahaifiyar shi iya abunda zai mata kenan sai da albarka take yi mashi

A ranar gidan su A'isha da radiya suka wuni. Sai dare suka koma

Mama taso ta roki Abba ya bar mata radiya ta tsaya da ita sai kuma taji nauyi don taga yana son zama da yaran kusa da shi kwai ta hakura.

Mommy yau zazzaɓi gobe sauki babu wanda ta gaya ma wa sai sistern ta da ke Tanzania ita ma ta fada ma yan gida sai murna suke ke yi suna mata Allah ya kara lafiya kullum.

Yau jadwa zasu shigo garin bauchi don sun dawo Nigeria. Ta matsa ma Dr sweet inta da ya kawo ta gida ita tayi kewar su har cewa tayi zata hada shi da Auntyn shi.

Yace bai kai chan ba zai kai ta. Ita kam alhamdulillah yadda Dr fahad yake nuna mata so kamar ya mayar da ita ciki, ga yan uwan shi na kaunar ta.. a yanzu sai take ganin kamar yafi son ta.

Yau da dai mommy ta tashi da zazzabi ma karfi sai Abba ya kira nurse tace sai an saka mata drip, sunyi waya da zainab take fada mata zainab ba ƙaramin murna tayi ba tashi suma zasu shigo.

Kamar an sun hada baki zainab da su jadwa zaka shigo garin bauchi rana daya

Gida ya cika Alhamdulillah Abba ko da ya kalle su yana kara gode ma Allah da ya haɗa mashi kan iyali gashi kuma za su sake samun karuwa.

Su A'isha ba karamin kuka suka yi ganin yadda jadwa ta zo tayi mul mul da ita sunyi nadamar abun da umman su tasa suka yi mata a baya gashi rayuwa da suka so suyi irin nata kenan su ga yadda suka kasan ce.

Sun roke ta gafara kuma tace ita kam ta yafe masu.

Ganin jikin mommyn ta yasa ta shiga damuwa sai dai Aunty zainab ta lura da bata san abunda ke damun mommyn ta ba sai ta kira ta gefe suka wuce daki, ba karamin dadi taji ba da jin abunda ya same su yanzu zata samu Kani ko kauna kenan harda tsalle, sai Aunty zainab tace wai jadwa yaushe zaki girma ne ? Dan Allah ki rage murya mana sannan irin wannan tsallen haka kema ba sai naki ya zube ba..

Sai jadwa take Aunty zainab Ni kam ai ban da komai sai ta rufe fuska tace toh shikenan Allah ya kawo ke ma sai tayi murmushi bata ce komai ba. Tana fadin haka tace amma Aunty zainab shine umma bata fada mun ba tace nauyi take ji ai nima daga baya naji tace toh.

Anyi zumunci sosai ranar kowa yaji dadin ganin kowa anci an sha kuwa mommy ma da ke kwance taji dadin yadda yan uwa suka zo aka taru akayi zumunci.

Dr fahad ya ma su mommy alkhairi sosai kuma yace shi zai wuce Abuja ne, idan tayi kwana biyu sai ta koma sai Abba yace suyi sati daya kawai ita da zainab su wuce Abuja tunda dama ita ma Abuja take.

Su A'isha sun shiryu sun koma makarantar amma dai zasuyi resitting idan sun gama saboda semester biyu da ya wuce su kuma Abba ya samar masu wani malamin islamiyya yana zuwa yana koya masu karatu sun natsu sosai

Jikin mommy yayi sauki. Jadwa da Aunty zainab sun koma Abuja jadwa ta wuce idan ta an samu mata transfer ta koma school ta shiga nile University da ke Abuja

Sun ci gaba da shan soyayya ita da Dr fahad sai Masha Allah.

Yau yan uwan adam zasu zo za'a tsayar da rana, sosai radiya suke fahimtar juna da adam kuma tana jin dadin zama dashi bashi da matsala ka saukin kai da addini shike kara burge ta da shi.

Suna da rufin asiri dede gwargwadon kuma yan uwan shi na son radiya sosai ranar da ya nemi iznin zuwa da ita gidan su kamar su lashe ta.

Sun zo Abba yasa anyi masu tarbo na musamman sun ji dadi sosai kuma an tsayar da rana wata daya da sati biyu, sun ji dadin hakan kuma suka ce In'sha'Allah next month zasu kawo lefe.

Ma'assalama ❤️
Next chapter coming soon In'sha'Allah

JADWA (Completed)حيث تعيش القصص. اكتشف الآن