JADWA 15

77 5 0
                                    

Da isar ta ningi sai gidan tabawa, tabawa ta tare ta da zumudin son taji labari amma tunda taga yar gidan nata na fara'a tasan andace... Akwai nan ta bata labarin komai abunda ya faru harda kudin da ya kara bata.. akwai tabawa sai buda tace haƙan mu ya kusa cin ma ruwa kenan Lallai wannan labarin yayi mun dadi.. ana cikin haka ta raba kudin biyu tabawa tabawa dubu ɗari biyu da hamsin, tabawa tace anya ayi haka kuwa? Tace ai amma yi ke dai karbi ai kin gama mun komai wlh.. tace toh ta gode.
Nan umma ta wuce gida tana mai nishadi tana jin dadi..

***
Haka ta samu yan manta ta ta masu karya da ta saba kuma tace suke su sawo tsire da lemu yau aci asha, Sudan suna mamakin yadda take kashe masu kudi kwanakin nan amma suka yi shiru basu tambaya ba. Haka ko suka yi suka ci suka sha.

***A bangaren Alhaji Yusuf kuwa rigima suka yi da hidaya sosai akan cewa ita fa bata yarda da umma ba abun nata ya fara wuce gona da iri da daina zuwa mata gida shi dai ya lallabai ta yace yaji amma a zuciyar shi ya rasa mai yake ji game da umma sai tunanin ta yake yi yana Alla Alla ya fita ya kira umma a waya yaji ya ta koma, aiko ya a fita haka yayi, yaje ya kira a waya da sallama umma ta amsa kamar wata na kwarai hmm, nan ya fara mata bangajiya akwai nan kuma ta sake jiki sai kalame take mashi masu dadi cikin kwanciyar hankali shiko ya shagala har bai son daina waya da ita, hmm. Ana cikin hakan can ya kira ashe sun share awa minti 30 suna waya nan ya mata sallama ya koma gida. Ita dai hidaya koda ya shigo gida bata yarda dashi ba amma ta kyale ta addu'a Allah ya kare mata mijin ta don bata son wata ta shiga tsakanin su yadda take jin labarin mata akan kishiya baza ta so yazo kan ta ba kuma ita koda wasa bata taɓa ganin wacce Alhaji Yusuf ya sake ma fuska haka ba kamar umma tana tsoron kar alaqar su ta wuce gona da iri..

***
Ita ko kuma kasa kwance kasa zaune tayi ai nan take ta kira tabawa tana bata labari, tabawa sai kara jingina mata tayi tana kara mata kissa iya magana yadda zata kara samo kan Alhaji da kyau da kyau su basu san bata lokaci nan da kwana kadan ayi biki akai amarya 😁 jama'a ku kuji fa, wannan wani irin karfin hali ne ?

Haka umma taji dadi sosai tace aiko zata yi iya bakin kokarin ta.. da haka suka yi sallama.. nan ta fara fada ma yaran ta wai zatayi aure ba, nan A'isha ta zato ido tace umma aure ba fa? Shi baban mu fa? Tace idan kika sake mun wani magana baban sai naci mutum cin ki, wani baban ku wanda ya wuce ya bar mu cikin halin taulaci, wa ma yasani ko yana raye? Lallai ma, nan Fatima tace toh umma wa zaki aura tace Alhaji Yusuf wanda nake baku labarin shi, nan suka zaro ido sukace da gaske umma tace kwarai kuwa, tace shine yace yana son ki? Tace toh wannan ya ba damuwar ku bane kudai kira addu'a idan ya aure ni rayuwar mu dani da ku zai chanza gaba daya kuma zaku zama yaran manya..
Nan suka ji dadi sosai wlh amma banda radiya da tayi rau rau da ido tana tunanin irin hali na umman ta don ita karama ce sai wayau sannan ta fara yi observing abubuwan da suke kullawa da tabawa duk da baza ce tasan komai duka ba amma lallai wannan auren da umman su tace zata yi yana da alaqa da abubuwan da suke shiryawa dasu tabawa...

***
Kwana a tashi, haka suka rayuwa ya cigaba da tafiya tabawa da umma sun koma wajen boka ya kara masu magani harda na binne binne, shi kuma Alhaji Yusuf kullum abun sai gaba yake yi a kullum sai jin umma yake yi aran shi yana jin soyayyar ta sosai kuma kullum sai sunyi waya har sau uku, zuwa yanzu yana so yaje har ningi ya ga inda umma take, Ita kuwa hidaya tasan komai don tun yana waya da umma a boye har ta fara kama shi kuma ya gaya mata gaskiya. Tabbas ta shiga tashin hankali, taje wajen zainab watau qanar Alhaji Yusuf kenan, haka tasame ta tana mata bayani tana kuka lallai zainab taji tausayin ta sosai, haka tace zata sake yayan ta suyi magana na fahimta. In'sha'Allah komai zai zo da sauki zainab ta kwantar da hankalin sosai kuma taji dadin zuwa wajen ta. Da haka ta koma gida.

***Yau Alhaji Yusuf ya nufi hanyar ningi shi da wani yaron shi wanda suke kusa sosai, shi dai yace mashi ya raka shi ningi haka suka shirya suka wuce, ya fada ma hidaya zai je ningi nan a hankalin ta kara tashi don basai ta tambaya ba tabbas tasan wajen umma zai je don tasan labarin ta, nan ta ma zainab waya ta fada mata tana kuka nan zainab tace ta kashe wayan zata kira ta, sai ta kira yayan ta bayan sun gaisa tace tana so yazo wajen shi kuma zasuyi magana mai mahimmanci nan dai, yace mata tayi hakuri zai je kauye amma idan ya dawo gobe sai tazo, nan tace mashi toh shikenan yaya na gode. Ai zainab ba shiri taje gida tana ba ma hidaya hakuri tana kara kwantar mata da hankali. Daga nan tace bayan nan gobe ma zata dawo dole saboda suyi maganar. Nan dai hidaya taji sanyi sanyi a ranta.

JADWA (Completed)Where stories live. Discover now