JADWA 30

75 8 9
                                    

Sai ta kwashe duka labarin abunda yake faru ta fada mashi. a da kuwa da yazo yake cewa yasan me ke tafe da ita, duk bata lura da hakan ba sai zuba ta ke tana mashi surutu.

Yace toh ta dakata ai laifin ta ne da bata waiwayen shi kullum sai dai aike aike.. yace yanzu zai fada mata abunda za'ayi yace sai na sadu dake kafin aikin da na baki ya dawo saba sannan zaki aje ma aljannun kudi 1 millon. Zaro ido tayi ita ba kudin bane ya dame ta a'a cewar da yayi wai sai ta sadu dashi ta gama yadda ya koma duk ya wani rame yayi baki sai baki mashi kamar kacha hmm yace ko baki bukata ne ? Tace ina nazari ne yace idan sai kin yi nazari ai sai a bar abun tunda babu dole, haka tayi shiru tana kallon shi can ta ce toh ya za tayi tunda tana son wannan abun ya dawo sabo don tana hankalin ya tashi da Abba sosai yadda yake mata ga shi kuma jadwa zata auri dan mai kudi ta bar yaran ta duk cikin yaran babu mai kamun kai sai radiya..

Na amince ta fada kai tsaye ya washe da dari yace toh muje... Tace ina za'ayi yace can kasa zamu je mana karma ta tambayi bukkan shi sai kuma ta fasa.. ta fara bin shi suna ta tafiya yana zuwa bakin wani sai ya zagaya ta bayan wani icce ya dauko shimfida yace da cire kaya ita dai mamaki abun ke bata zai kara magana kenan sai ta zauna ta cire gyalen da ke jikin ta ta fara zuge zip in rigar ta yana tsaye yana kallon sai da ta kama tayi zindir sai ta fara kame jikin ta, shiko bako sai hadiyar yawu yake yi yana zaro ido haka ya zauna tana matsawa zai yi magana kuma sai ya jawo ta ya fara shafar jikin ta daga hakan dai sai da ya cimma burin shi yayi lalata da umma ya gama ya tashi yace ta aje kudin tace ba ta zo dasu ba amma zata dawo mashi dasu.. yana kama dariya yace gaskiya mijin yayi dace da don ba karamin dadi kike dashi ba.. shiru tayi bata ce mashi komai ba yace zai mata aiki da yafi na da zata sha mamaki.. toh tace ta sa kayar ta ta fara shirin barin dajin don ita yanzu babban burin ta tayi wanka da kazantar shi take gani ma. Ko da ta juya ta kuce ta koma wajen taba jiki dai yaki haka ta bata kyautar 5k tabawa cikin murya mai ban tausayi da zafin ciwo tace wai ni umma kike na ma 5k ? Sai umma tace haba tabawa kiyi hakuri kinsan komai yayi kasa, yanzu haka ma boka million 1 yake nema amma idan zan dawo da kudi zan zo maki da kudi kinji toh tace mata tayi mata sallama ta kama hanya ta bar garin ningi ko mahaifiyar ta bata je ta duba ba bata ma san ta shigo ita abunda tazo yi shi tayi..

Tana koma wa gida yamma yayi sai ta kuce kai tsaye part inta Abba ta gani zaune ya hade rai, ina kika fito ya tambaye kai tsaye, sai tayi karye tace magani taje karbo ma radiya na ciwon mara da ke yawon damunta wajen Al'ada hmm yace ya kalle ta yace zanyi maganin ki.. kallon shi take yi ta kasan magana ita fa yanzu abun ya kara daga mata hankali irin abunda yake mata cewa tayi gobe zata sayar da wani karamin filin da ta sake ta saci jiki ta koma ningi ta ke ma boka kudi don wallahi abubuwan da Abba ya bijiro mata dashi baza ta iya hakuri ba, fita tayi ya barta nan tana wasu wasi...

Jadwa da Dr fahad soyayyar yayi karfi kullum waya, amma ko taje school basu hadu bai taba cewa su hadu a school ba. Ita ma bata damu don hakan ya bata saboda bata son sa ido, afra sai bibiyar take yi ko zata samu wani labari ta fada masu basma su kwashe su fada ma A'isha ma sam bata fada mata komai ba kuma ko ta tambaya sai dai ta tuna mata addu'a suke yi har yanzu..

Kamar yadda Abba yace ma Dr fahad yasa manya cikin maganar su haka da washen garin da yayi ma jadwa alqawarin zai kira daddyn shi haka ko ya kira. Daddy ya yi murna da wannan albishir da ya mashi yace burin shi zai cika ba shiri daddyn yasa aka fara abin cike akan Abba. Kasancewar babban dan kasuwa ne kuma ya shara wajen kasuwancin sa babu bata lokaci aka hada duk wasu bayanai da daddy ke so aka kai mashi, sai nan ma daddy yace ina jin labarin companies inshi. Abba yasu shaidar da akeso, sosai mutane sun ya bashi Alhamdulillah ita kanta jadwa an ya beta ba laifi. Ai ko daddy yayi murna ya hada kan mutane yace weekend za aje neman aure, daga nan bada kudin aure ayi komai cikin lokaci.. ba karamin dadi Dr fahad yaji ba da daddy ya fada mashi kiran jadwa yayi ya mata albishir ita tayi murna sosai, yace mata zai kira Abba da kanshi ya sanar mashi tace toh shikenan ta fada tana dariya haka suka waya suna labarin yadda zasu gina rayuwar auren su abun sha'awara

Sistern mommyn ta kira don bata ji komai wajen Aunty zainab ba tunda tace zata kira su akan maganar amma shiru.. tana kira ta dauka sun gaisa bata ce mata komai ba sai ta ba ma mommyn ta yadda suka yi fira da mommyn ta jadwa sai da tayi ma Allah sujood don fira suka yi sosai harda tambayen ta Abban ta ? Tace yana lafiya lau tana fada tana mamaki da kara gode ma Allah ko da ta ba ma sistern na ta waya tace kinyi mamaki ko Allah ne ya karbi addu'a mu duka kuma shi kashi Abban muna nan zuwa gare shi sai mun ba shi mamaki kuma naji abun arziki wajen zainab In'sha'Allah a wannan lokacin dole mu zo ma ko don saboda wannan kuma mommyn ki taji sauki sosai Alhamdulillah abunda ya rage cikin lalurar ta bai da yawa kadan ne.. kuma shima da yardar Allah zai tafi. Tace mommy naji dadi nayi ma Allah godiya Allah ya kara mata lafiya tana fadi tana farin ciki suka yi sallama ta kira Aunty zainab na murya tana fadan Aunty zainab mommy taji sauki mommy taji sauki Alhamdulillah Allah mun gode ma Alhamdulillah.. Aunty zainab tace tsaya jadwa muyi magana murna ya isa haka kar ki shanye zaƙin tace wlh Aunty zainab sai dai na shanye kinsan abun farin ciki ne tace tabbas nasani jadwa nima ina ta so na kira don wanna lokacin zasu zo nigeria kuma harda mommyn ki ya kika nima nasan taji sauki tunda wayan a har da ni muka gaisa kuma ta amsani alhamdulillah naji dadi sosai sai dai muce Allah ta kara mata lafiya.. Ameen tace suka yi sallama.

Dr fahad ta kira tana fada mashi, yayi murna sosai yace hakika addu'a bai bar komai ba kuma duk wanda ya rike addu'a da ibada gama daya ta yana tare da nasara hakika ibadar ki ce da addu'ar mu Allah ya karba. Allah ya kawo su lafiya Ameen.

Kema idan Abba ya dawo zai fada maki ranar da za azo neman auren ki ya fada yana dariya... Shiru tayi can tace Alhamdulillah i cant wait yace soon In'sha'Allah amarya na.. rufe ido tayi kamar suna tare. Jin shiru yayi yawa yace kunya koh? Zaki daina ai sai tayi dariya haka suka cigaba da firar soyayyar suna kara ba ma juna labarin kansu cikin nishadi da kaunar juna har lokacin bacci yayi sukayi sallama suka kwanta.

Koda ya dawo bai je ya duba umma ba kuma sam bai damu da ita ba ma dakin shi, shi tafi ranshi kwanta kwanta

Da safe bayan taje kai da Abba ya mata albishir kuma yace yau zai tarbi manya baki don haka ba zai je ko ina ba, tayi murna sosai amma ba ta bari ya gane ba saboda kunya..

Haka ko jadwa ta su lantana suka yi abinci kala kala na alfarma, duk abun da ake umma bata sani don Abba bai kula ta ba, radiya kawai jadwa ta fada ma wa tayi murna sosai kuma ta shiga kitchen taya su girkin amma san bata fada ma umma tunda tasan halin ta kuma tasan basu kaunar abun. Su A'isha ana can ajen yawo wannan karon yawan su har Lagos ya kai su da su basma. An hada su da wani Alhaji yana shirin yi masu visa za'aje dubai duk. Koda umma tayi waye dasu karya suka mata kuma bata damu tace Allah ya dawo dasu lafiya ita yanzu ta kanta take yi..

Mamaki take da ta fito ta ga duka motocin Abba a gida bai leko ta ba har gari ya waye rana ya fito, koda ta je kitchen taga ana ta jera abinci za fita dasu aje guest room. Kallon abun ne da gaji dashi sai ta tambaya wai me ke faruwa ne gidan mu? Rabi ta bata amsa tace Abba ne ke da baki kuma bakin na jadwa ne tace kan uba! Jadwa fa?? Shine ake wannan abin da snacks ikon Allah.. fita tayi a hankalin ta atashe ko ba a fada mata ba tasan manya ne zasu shigo don maganar auren jadwa toh me yake faru da ita, har yanzu ace magani bai fara aiki ba. Kara sauri tayi ta shiga dakin Abba ba salam tace haba wai me nayi maka ne ko ni ba matar ka bane tun da ita zaune gidan ka ai ka so sanin halin da nake ciki ko bare ni hakkin ka ce ya kama kasan yadda na kwana da kuma yadda na tashi, banza ya mata kamar bai san me take fada ba.. kara magana tayi cikin daga murya, nan juyo ya ɗaga mata hannu yace fita... Fita nace ki fita ki bar nan.. tsawar da ya mata ne yasa ta fita ba shiri don ta san ko murya bai taɓa daga mata ba in ba yanzu ba..

Ko data fita tana waige waige cikin gida kawai sai taga mai gadi na bude kofa.  Tsayawa tayi cak! Manyan motacin da suka hada convey suna shigowa gidan ya sa ta mamaki tsayawa tayi ta kama ƙugu tana kallon su harda su police ciki abun mamaki ya kara bata...

Ma'assalama! ❤️❤️
Sorry for this little chapter
Kinda busy these days
Comment and vote pls
Ignore mistakes

From now on I will only be updating a chapter during weekends In'sha'Allah because your girl kinda really occupied now..

Enjoy! ❤️🦋


JADWA (Completed)Where stories live. Discover now