JADWA 35

69 8 0
                                    

Sistern mommy ce ta fara amsa, mommy ma ta ɗaga kai ta kalle su sai ta amma cikin fara'a, Barka da zuwa ya hanya ? Mommy ne da sistern suka hada baki lokaci daya. Amsawa yayi kanshi a kasa yana basu amsar cikin na tsuwa sun yaba da shi sosai da hankalin da ladabin sha kyaun shi.

Koda suka tambaye shi yadda mahaifiyar ta kai ya amsawa yace lafiya kau sannan ya kara da cewa sun ce ma idan nazo nan na kira su zaku gaisawa yana gama fadar hakan ya ciro waya, mommy tace ba matsala ka kira su ai sai a gaisawa ta ke ya kira kuwa mommy ta dauka sai yace mata yana gidan su jadwa ne yanzu zai ba mommyn ta su gaisawa sai tace ba matsala. Mika ma umma wayar yayi yana a rusun ne, ta karba tayi sallama ita ma ta amsawa sun gaisa sosai yadda suka gaisa sun sake jiki ma junar su kaman sun dade suna magana a waya ko sun san juna da ta gama tace zata ba ma yayan ta su gaisa, ita ta karba suka yi nasu harda Aunty duk sai da suka gaisa nan Aunty ke tambaye wai ina surukar mune ? Bayan da suka mika ma Dr fahad da waya kenan, nan ya mika ma jadwa waya yace za'a gaisa da ke tace a'a taƙi karba kowa yayi yayi da ita yaƙi wai ita kunya, ita mommyn ta abun haushi ya bata, sai Dr fahad ya fadaa ma Aunty ta ƙi karba. Dariya tayi tace ai duk naji abun da kuke fada tunda baka kashe wayar, kyale ta kwana nawa ya rage ta zama namu sai yayi dariya yace toh sai anjima suka yi sallama jadwa dai bata karɓi wayan ba.

Yayi sallama yace zai wuce gidan shi inda yake sauka a bauchi ya aje masu kudi cikin envelope da bansan ko nawa bane su kansu basu lura da kudin ba sai da ya wuce sannan suka hango kudin a kasan curshion in da ya zauna.

Jadwa ta je raka shi har waje sannan yace mata ya aje ma su mommy kudi koda zasu yi tunanin ya manta ne ttoh ba manta yayi na su ne, ita jadwa mamaki abun ya bata sai ta sake baki tana kallon shi, tace Dr sweet wannan wani irin wayau ne haka ? Dariya yayi yace kema ki koya daga yau. Sai tayi murmushi yace toh shikenan take care of yourself for me okay ? Sai ya shiga motar shi ya fara reversing in motar ya juya zai bar gidan yana mata waving.

Koda ta koma parlourn a lokacin su tsaye kan envelope in suna mamaki suka ce kilan yayi mantuwa ne, ita ko sistern tace bai manta ba wani hikima ne yayi nan.  Jadwa naji tace wlh babu wani mantuwa naku ne wai ya baku kunya yake ji shiyasa ya aje. Koda suka bude 70k ke ciki, suka ce idan Abba ya dawo za'a fada mashi..

11: 23pm suke knocking in gidan kamar zasu balle gate, al'adar gidan da 10pm yayi mai gadi yake rufe gida ya shige bacci don ya san kowa na gida hatta da Abba kuwa ko, knocking in ya ta yar mashi da hankali saboda yadda yaji ana yi babu kakkautawa, dauko bindiga shi yayi ya fito yayi addu'a yace waye ?? Muryan su A'isha yaji suka ce dan Allah ka bude mana ko zaka ce baka san muryan mu bane, ka bude mu ka ce, sai ya numfasa yayi ajiyar zuciya ya bude, A'isha ta fara shigowa ita ko fadi tangadi ta ke yi kamar zata fadi suna shigowa ya rufe ya koma ciki yana maganar zuciya shi kaɗe yace su wa'innan yaran sai suka ga damar dawo wa? Toh ai uwar ta su bata nan shi tausayin su ne ma ya kama shi yadda suka lalatar da rayuwar su.

Koda suka isa part insu suka wuce, sun ga part in a kulle su kuma Bama zasu ce ga inda mukulli yake ba ilan sun yar, A'isha ta mike haryan part in umma kenan sai tayi wani tunani tace kawai mu kwana nan don bazan iya knocking ba don nasan wahalar bazan zanyi kin fi kowa sanin yadda umma ke da nauyin bacci.

Daga kai Fatima tayi ita yadda tasha tayi tatil ai bata fahimtar komai.

Haka suka shimfida kayan su suka wanka, koda gari ya waye rabi ne ta far cin karo da su, suma a dalili ne yasa ta gansu saboda tana shara ne ya biyo da ita ta part In su, koma wa tayi ta taje tana fada ma mommy, mamaki ya cika mommy tace muje, suna zuwa haka suka gansu suna bacci kama ma rasa rai ga ranar har ta fito, tace toh su wa'innan ina suka fito haka ikon Allah ta fada tana rike hannun ta.

Koma wa tayi ta shiga dakin Abba tayi sallama ta fada mashi shima mamaki yayi ya ce su je koda suka je haka ya gansu kamar yadda mommy ta barsu.. rabi yace ta samo ruwa ta watsa masu..

Da sauri taje ta samo ruwa aka wasa masu ita dai A'isha ta tashi, ita ko Fatima ta farko amma ta cigaba da surutai ba kai...  Sai ce Abba ya daga mata tsawa yace mata yanzu an tambaye ku ina kuka fito? Ke kuka ki kuma. Duka suka yi shiru hatta da Fatima sai da ta tsaya tana kallon Abba cikin ido.. kara magana yayi a karo na biyu sannan suka amama A'ishah ce ta lemo wani karya tace kawai sace su aka yi sun hau adaidai zasu je schll daganan basu sa ke ganin kansu ba sai dai suka farka suka gansu wani daki mai duhu, basu kaɗe bane, akwai yan mata irin su, a aminci ki  so daya 🤔 ita kuma Fatima yau ne ya tilasta mata sai tasha giya taki ya nuna mata bindiga shine ta sha, bayan ta sha ne shine ya suka fita suka rufe mu sai muka bulle window muka fita muna ta gudu.. Abba yaji tatsoniya su yace toh me yasa basu kira kowa na ku ba inda kidnapping ne ? Yace toh yanzu ba ma wannan ba mommyn ku ta samu lalurar hauka yadda mommyn jadwa ta taba yi kuma na sake ta tana ningi yanzu kuma za ku koma can ne yanzu drivet zai kai ku anan In'sha'Allah makarantar ku za ku cigaba amma a ningi, sake baki suka yi ita A'isha wani bacin rai taji wanda bata ba jin irin shi ba. Hmm kuka fatima ta kama yi tana kiran umma umma.. A'isha sai hawaye ke zuba fuskan ta shiga tashin hankali mara misaltuwa.

Koda Abba ya shiga daki mommy ta bishi yaje shi bai yarda da labarin su ai sai da yaje makarantar su ya tambaya kuma aka ce basu ma kasa yanzu karya suka hada mun, ƙasan suka yi bari sunje shakatawa fa.

Mommy mamaki take yi tace toh Allah ya kyauta a lokacin jadwa na tsaye sai da Abba ya wuce mommy ta mata narrating in sorry

Jadwa ita ma ta sha mamaki amma tasan karya suke yi, Abba bai yarda ba tace Alhamdulillah. Ko da ta fita ta gansu taji tausayin su sosai wlh amma ta san duk karya suke yi..

Driver tsaye yayi yana ce masu wlh idan rana tayi zafi bazai je ningi ba da suka ga kowa ya fita batun su ya kama hanya. Sa suka ga na sarki sai Allah sai suka hada kayan su suka je suka sa a boot suka sa kayan su, sun shiga, shi ko driver ya taso sai ya shiga motar ya fita gidan (cikin raina na ce toh su ba ko sallaman yan gida bana)?

Ma'assalama 🦋❤️
Your khads
Not edited, please

Net chapter coming soon In'sha'Allah..






JADWA (Completed)Where stories live. Discover now