JADWA 37

69 6 2
                                    

Labarin duk abunda ya faru ya bata babu daɗi babu kari. Abubuwa abunda radiya take sai kuka hawaye ke zuba a fuskar ya bata labarin kuma su A'isha ya ce su koma can amma zai cigaba da biya masu kudin makaranta, ita ma zai nema mata admission In'sha'Allah Amma ita yana so zai cigaba da zama da ita anan sa dai idan tace baza ta zauna ba.

Nan ta fara magana cikin shaƙekken murya tace Abba hakika irin ku a duniya kadan ne In'sha'Allah Abba tun ana raye mutane ta maka zaton shiga aljanna kuma ko abunda umma na tayi maka ka kyale kuma kace zaka cigaba da kula damu wlh In'sha'Allah kana da sakamako mai kyau wajen Ubangiji domin Allah yana son masu yafiya. Zan cigaba da zama da ku In'sha'Allah amma ina so kuyi mun wata alfarma ku barni naje ningi naga umma. Abba yace ba matsala gobe idan kin rage gajiya kije kiyi zan sa driver ya kai ki In'sha'Allah.

Abba ya tashi abar parlourn saboda kukan radiya yana raunana mashi zuciya. Jadwa ce ta tashi taje tana rarrashin ta, mommy ma barin parlourn tayi. Da kyar radiya tayi shiru tace zata koma daki ta kwanta toh jadwa tace mata ta wuce nata takin ita ma.

Radiya ta isa daki ta fada kam bed sai kuka tana tunanin irin ɗayen aikin da umma tayi tana kara ba ma zuciyar ta hakuri tana jin yadda zata cigaba da zama dasu duk da tasan ba halin su bane wai su kalle ta da abunda umma tayi amma ita ranta dole ta kama jin wani iri anan ta fara rokon Allah ya kawo mata miji tayi aure tare da yan uwanta da suka sa ma rayuwa gaba ita umman ta Allah yasa taji sauki ta tuna ta nemi yafiyar mutanen da ta zalunta kafin lokacin mutuwar ta..

Tana cikin wannan tunanin sai ka kira numbern da ya dame ta tun tana cikin mota lokacin da zata dawo Bauchi koda ta dauko wayan kashe wa tayi gaba daya ta wuce toilet tayi alwala ta je ta dauko dadduma ta fara sallah tana fada ma Allah damuwan ta, koda ta idar taji sauki sosai a ranta bayan ta gama kai ma Allah karar damuwan ta ta dauko Alqur'ani ta fara karatu bayan ta gama taji sauki sosai aranta ta kwanta tayi bacci.

Washe gari da karfe 8 ta tashi ta fara shiri taje ta gaida mommy tace ta shiga gaida Abba anan ta hadu da jadwa suna fira da Abba ta gaishe shi, shi da kanshi yake tuna mata maganar zuwa ningi tace eh ai gashi tana ta shiri yace toh idan taje ta gaishe su duka tace In'sha'Allah

Tanan ta bashi tare da jadwa ta koma tayi wanka tayi breakfast sannan ta kunna waya sai ka kiran numbern nan da ke kiran ta ya kara shigowa bata dauka ba ta bari sai da ya gama ringing sai ga na malamin su yana mata maganar zava kawo mata matar ta da aka bata kyauta wajen musabaqa godiya tayi tace Allah ya kawo su lafiya. Dama tunda ta dawo ta mika ma abba key in aka bata kuma ta fada mashi kudin da ta samu sosai yaji dadi yace ta barsu a account inta tukun..

Taga shiri tsaf taje ta sallame su mommy kamar yadda mommy ta saba ba ma umma tsara idan zata je ningi takai ma mama wannan karan ma bata manta haka ta ba ma radiya tace ta kai ma mama.

Driver ya dauke ta ya fara tafiya a hanya mai numbern ya ci gaba da kira kamar zata dauka sai ta fasa ta kashe wayan ta kar ya karar mata da charge in waya..

Suna isa km ingu gaban ta ya fara faduwa koda ya keta kofar gida a sanyaye ta fito mota da sallama ta shiga ta mama ta amsa tana zaune kan tabarma.. koda ta ga radiya tace auta Barka da zuwa Barka Barka tace yawwa sannu mama juyawa ta fara yi koda ta ga umman ta daure da mari da gudu taje wajen tana kuka tana umma kece nan innalillahi wa'inna ilaihi raju'un ummma tana salati tana fada ma Allah hankali ya tashi sosai umma tayi baki ta rame wasu kuraje manya sun fara fito mata a jiki SubhanAllah babu kyaun gani..

Juyawa tayi tana kuka tana tambayen mama su A'isha mama tace tun bayan da suka dawo da kwana biyu suka gama kuke kuke su suka ce mun zasu wuce ma school har yau ko kira babu radiya tace mama school ana hutu fa sun dai je nasu radiya tace gaskiya su A'isha basu kyauta ba..

Da haka ta wuce taje ta samu dan sahu ta da maza aka kwance umma aka sata a sahu aka wuce da ita hospital an fara gwaje gwaje aka gano tana tabin hankali kuma tana da cutar HIV ko da result ya fito radiya ta kusa summa da ta gani ta so ta kira Abba sai tayi tunanin irin abunda umma tayi ma su Abba bai ka mata ma ace ya dauki nauyin ta ba tunda tana da kudin ta bari ta mata kawai a matsayin ta na mahaifiyar ta.. duk ta san Abba idan ta fada mashi halin da umman ta take ciki tasan zai yi amma bari ta kyale kawai da wannan tunanin ta je office in doctor.. sunyi lissafin Kudi da magungunan da zata fara sha  kusan 400k a haka ko radiya ta fitar tunda samu kudi sosai ta baya aka fara ba ma umma treatment..

Haka ta cigaba da kiran layin su A'isha domin ta fada masu halin da umma take ciki, amma basu dauka sai wani yammacin ta samu Fatima ta dauka ta fada masu ta nuna hankali ta ya tashi tace zasu dawo gobe da haka suka yi ta kuma radiya har yanzu tana tunanin toh ina umma taje ta kwaso HIV ita dai rokon ta kullum Allah yasa bata sa ma Abba ba.

Koda ta fada masu halin da umma ke ciki ta kasa basu labarin HIV abba ya mata fada sosai kuma yace meyasa bata fada mashi ya turo da kudin hakuri ta bashi tace saboda ta ga tana tashi ne shiyasa tace zata yi mata da kudin ta. Haka dai abba ya hakuri.

Ta kwashe sati ukku tana jinya umma hospital amma har yanzu su A'isha shiru babu labarin su.. ba laifi umma jikin ta ya fara warware wa da taimakon maganin da take sha da abinci da kulawa  sosai sai ta fara jin sauki.

Ana gobe za'a kai lefe jadwa ta kira ta ta fada mata tayi mata murna sosai kuma tace In'sha'Allah zata dawo ayi biki da ita..

A ranan radiya tace zata daga wayan wannan anacen, da yamma ya kira ta kusan so hudu na biyar ta dauka tana dauko yayi sallama ya ce mata lalla shiyasa yau akayi masu ruwa yau radiya ce ke dauki waya ta Alhamdulillah Alhamdulillah ya kama fada yana hamdallah ita shiru tayi tana sauraron shi can tace tashi kayi maganar ka, ya fara tsara maganganu tace dan Allah ya fada mata magana kai tsaye ita bata son kwana.

Nana ya fara mata baya Ni ce yana cikin malaman wasu makaranta anan kano komai nata yayi mashi shiyasa ya kirbi numbern ta kuma yana ta kira ba'a dauka shi kuma ya dage yana kira yana addu'a Allah ya karba mashi addu'an shi. Tace toh naji yanzu me kake yace yana so su fahimci juna idan Allah yayi akwai rabo tsakanin su sai ayi aure tace toh

Kawai ta fadi kai tsayhe  da ya gama zuban shi yace tayi Saving in numbern sunan Muhsin tace zatayi Allah ya bata iko yace Ameen..

A ranshi yaji dadi ba ko kadan ba yau yadda ya dace har ta dauki wayan  shi kuma suka yi magana duk da dai magana bata yi tsawo ba shikan alhamdulillah yake ta fada.

Ita duk matsin umma yana kan ta ita tunanin ya za'ayi su san umma tana da HIV abun Yana tayar mata da hankali ta rasa da wa zata yi magana don ko mama bata sani ba ga yan uwan basu jin magana suna can suna yawa da sunan makaranta..

Koda ta koma gida tayi wanka tayi abinci sai mama tambaye jikin umma tace da sauki a yau ne tayi alkawarin zata fada ma mama cutar da umma ta ke dashi, domin ta samu shawara a wajen ta domin ita kadai baza ta iya ba.

Ma'assalama
Yours khadss ❤️
Not edited pls ignore mistakes
Vote and share alsoo
Let's meet in the next chapter In'sha'Allah

JADWA (Completed)Where stories live. Discover now