JADWA 24

68 7 0
                                    

Nan tace Wayyo Allah cikina cikina sai ta duka kasa nan Abba ya tashi yaje kusa da ita yace lafiya lafiya ? Nan tace cikina ciwo wlh tana nishi daya daya kuma ga gumin da take fitar wa 😲 nan hankalin Abba ya tashi koda ya jawo ta jikin yana kokarin dauka ya ke ta mota suje asibiti sai suka yi ci ga su A'isha sunyi sallama sun shigo dakin ganin abunda ke faruwa ya tayar masu da hankali nan radiya ta fara kuka dama ita karanren zuciya ke gare ta.
Nan suka fara tambaye Abba meya samu umman mu nan yace cikin ta ke ciwo yanzu zamuje hospital sai ya mike tsaye ya dauke ta su kuma suka bi bayan shi, yana zuwa inda mota yake ma'aikatar na gidan suka tashi suna tambayen Alhaji lafiya? Yace ba lafiya za muje hospital ne nan ya sata a mazaunar baya A'ishah ta shiga ita da fatima radiya kuma yace ta shigo gaba lokacin lantana ta fito taso ta bisu sau yace driver ya kawo su.

Koda suka isa hospital in shiga da ita emergency room anyi gwaje gwaje kuma ba'a ga komai ba kuma ita idan an tambaye sai tace cikin tane ke ciwo yana murdawa amma yanzu yayi sauki haka aka mata allura aka bata magani.. sai da ta daki idon kowa sai tayi kamar ta sha sai ta mayar da saura tasa a breziya hmm umma kenan duk kallon su take yi ita pretending inta kawai tayi don ita babu wani ciwo da yake samun kawai ita a tunanin Alhaji zai iya saurin gano wani abu a yanayin da ya mata maganar don ita kanta bata san ta shiga wannan halin ba ita a tunanin tunda ance an kira Mallam wlh duk daukan ta ya gama tona mata asiri shiyasa ta shiga tashin hankali har tana gumi.
Basu kwana ba aka sallame ta ba tare da doctors sun gane abunda yake damunta.
Koda suka isa gida sai sannu yake mata shi kanshi Alhaji sannu yake mata ita da yaran ta..
Koda dare yayi umma ta kira tabawa ta fada ma duk abunda kenan ita ma ta nuna rashin hankalin ta amma tace yanzu duk abunda da take yi ta samu lokaci ta zo ningi suke wajen boka tace toh In'sha'Allah zata yi haka ta tambayi Alhaji sai tazo su je kam.

***
Haka rayuwa ta cigaba masu ita dai har yanzu hidaya bata dawo ba alamu yanuna bama ta so ta dawo don tana jin dadin zama da zainab nan uwa uba kuma ga sistern kusa da ita kuma suna jin labarin gida can Tanzania.
Alhaji kullum sai ya je gidan zainab don duba iyalan shi idan ya mata magana maganar gida sai ta kama kaucewa.. yau dai ko da yaje yaci nasarar ciwo kanta don ta yarda zata suma gida jibi bayan gobe ta kai sistern airport zata koma gida tasan zata ji kewa ba kadan ba. Shiko Abba sai dadi yake ji kamar wani karamin yaro.

A bangaren umma kuma tayi ta fama da Alhaji kam maganar zuwan ta ningi amma yaki kullum sai yace mata zai sa rana shi ta kanshi zai kai ta suje tare su dawo tare sam bata ji dadi ta kira tabawa tana fada mata tabawa tace lallai Alhaji ya chanza amma zamu saita shi. Koda tabawa taje wajen boka yace dole sai umma tazo da kanta kuma aikin da za'ayi sai tayi kwana biyu wajen shi nan hankalin umma ya tashi koda tabawa ta fada mata amma na ta kwantar mata da hankali tace ai baza'a rasa yadda za'ayi ba zai koma wajen boka a karbo magani wadda zata sa ma Alhaji a abinci wanda idan yaci duk maganar da tayi dole ya yarda kuma ya mata yadda take so..
Umma taji dadi sosai tayi godiya ta tura ma tabawa kudi masu yawa.

***
Yau hidaya ta dawo gida koda umma ta ganta sai da gaban ta ya fadi da yake Alhaji ya sheda mata kuma taji dadi sosai tayi murya amma aciki ita wlh barin hidaya gidan duk taji dadi sosai ta sake sai mulki take yi nan ta kara jaddada ma kanta cewa ta lallai idan ta hidaya ta bar mata gida ba karamin dadi da iko zata yi ba da Alhaji kuma da ma'aikatan gidan da wannan Tasha alwashin ko zata yi yawo zindir sai hidaya ta bar mata gida.

Taje ta tarbe ta daga bakin gate ta nuna murnar ta amma na ciki fah ita kuma hidaya bata nuna mata komai ba haka ita ma ta nuna murnan ta sai Abba ya ji dadi su Radiya ta ji dadin ganin jadwa amma sosai saboda ta ga ta kara yau ta kara zama wata babban da kadan ya rage ta kai su yaya A'isha sai murna take yi ta rungume ta, su ko su A'isha sun nuna jin dadin dawowar ta amma na ciki na ciki haushi su kaji saboda sun ga ta kara kyau kamar wata balaraba yan matan cin ta ya fara fito komai da komai

Haka suka gama gaisawa da murnan su, lantana da rabi suka kwashi kayan ta su kayi cikin part inta dama already sun gyara shi tsab sai kamshi yake yi.

***
A yau tabawa tayi sammako taje wajen boka ta fada mashi labarin komai yace ai yasani, kuma zasu yi mata babban shiri amma matar nan ba hannu sake suke ma matsalan basu wasa da ibada amma duk da haka sai sun kara nasara a kanta, kuma ya bata maganin da za'a zuba ma Abba kamar yadda tabawa ta mashi bayanin yaki amince da zuwan ta nan.

JADWA (Completed)Where stories live. Discover now