JADWA 34

63 7 0
                                    

Mama sai godiya take tayi, a haka dai taji sauki da yamma masu aiki da driver suka mai da ita gida, suka kama hanyar bauchi..

Jadwa ne ke kuka ta na fada ma Dr fahad abunda ya faruwa a wata bayan ta gama ba ma mommyn ta labarin shi don a ranar basu bacci fira suka tayi iri iri jadwa na ba mahaifiyar ta hidaya labarin Dr fahad da kuma irin wulaqancin da azabar da ta fuskanta bayan wuce war ta tanzania wajen umma, mommy ta jingina abun kuma ta kara tausaya ma yar ta a daren sai da asuba ne Dr fahad ya kira ta a waya don tasan zai kira cikin dare amma ta kashe wayan ne don tana so tayi fira da mahaifiyar ta a daren bata so ma ya kira don ba Lokacin bane a daren.. sai da ya kira ta da asuba ne take bashi labarin abunda ya faru da kuma dawowar mahaifiyar ta..

Yayi farin ciki sosai kuma yaji dadin yadda abubuwa suka walwale a saukake nan ya fada mata ce zai shigo gobe In'sha'Allah ko don ya kawo ma su mommy gaisuwa na musamman. Tayi murna sosai tace Allah ya kawo shi lafiya..

Bayan taje gaisawa da mommy take fada mata cewa Dr fahad zai shigo gari don gaishe ta, taji dadi sosai tayi addu'ar Allah ya kawo shi lafiya..

Abba ya fada ma hidaya da yan uwanta da suka zo Nigeria yadda yasu yi da mahaifiyar  umma akan cewa zai cigaba da kulawa da hidaya kuma yau zai sa a fara bincike kan su A'isha aji inda suke idan sun dawo zai bayar dasu ningi su cigaba da kula da mahaifiyar kuma zai cigaba da biya masu kudin makarantar amma bazai zauna dasu ba, radiya ma don ba halin su daya bane, shiyasa zai barta kuma zai sa ta University tunda admission inta ya fito kuma idan ta samu miji zai mata aure In'sha'Allah.

Sun san cewa Alhaji Yusuf mutumin kirki ne, yana da kirki sosai kuma zai iya abunda ya fi haka inda akan kyautatawa ne.. sun yaba shi sosai kuma sun yi fatan alkhairi akan abun da zai yi..

Aje makarantar su ya sana aka fara binciken daga kan su afra, anan ne afra take fada masu cewa sunyi tafiya ne sunje ƙasar waje yawon shakatawa harda su basma duk friends ne..

Abba ya yayi mamaki sosai ashe duk yadda yake tunanin yaran nan sunfi haka tunda har zasu iya barin kasa. Barin makarantar yayi ya dawo gida da wannan lamari kowa yayi ya jinjina maganar daganan dai akayi masu fatan Allah ya dawo dasu lafiya..

Yau ne Dr fahad zai shigo gari ana ta shirye shiryen har da mommy a kitchen ana shirya ma suruki abinci.. 5pm dot ya sauka bauchi yana zuwa aka bude mashi gare ta shiga yaje parking space ya ja motar shi, jadwa daga sama stairs ta window ta hango motar shi, murmushi tayi sosai da ya bayyana kyakkyawar haƙoran ta. Sauri tayi taje wardrobe ta cire kaya ta sa a lokacin ne kiran shi ya shigo don ya fito yar ya shiga guest room don ya zama ɗan gida yanzu.

Dauka tayi da sallama ya amsa sun fara magana yace yana guest room, tace "wow ango nah ya zama ɗan gida" yace "dama Ni ɗan gida ne amarya" tayi tayi sosai tace zan zo yanzu In'sha'Allah yace ok!

Saukowa kasa tayi taje ta fada ma mommy, mommy tace "Alhamdulillah mun gode ma Allah bari naje ta shirya idan kun gama abunda kuke yi ku same ni parlour kinji"? Tace toh a taƙece ta wuce.

Mommy bi yar ta da kallon har sai da ta fita dakin tana murmushi tana ka gode ma Allah da ya nuna mata wannan ranar.

Koda jadwa ta isa guest room da murmushi ta shiga tana sallama, amsawa yayi suka gaisa suna wasa dariya. Yace gaskiya amarya kinyi kyau duk wannan kwalliyar ta wace ? Eh ta fada ba tare da ta ɗago kai ba tana murmushi. Yace aiko zan biya kudin kwalliyar nan.. sai ta zaro ido tace ai kyauta nayi ba sai ka biya ba ? Yace pls ki bari na biya mana sai ya marairaice fuska, tayi ya suɓuce mata 😂 tace toh ka biya sai yace ok

Mika mata wayar shi yayi yace tasa account details inta.. sai tace gaskiya bazan sa ba, kade biya da wani abun ba kudi ba yace Ni yanzu wannan da kudi zan biya tunda kin amincewa na biya toh pls na roke ki da kisa account details inki.. ya kara marairaice fuska a karo na biyu

Babu yadda ta iya haka ta sa anan take yayi Saving in account details inta a wayar shi kuma ya tura mata da 100k. 

Alert suka shiga wayan ta babu bata lokaci sai ta zaro ido tace Dr ai wannan kudin sunyi yawa me zanyi dasu ? Yace "tambaya na ma kike yi? Hmm lallai my baby ai baki rasa yin abu da kudi ke fa macce ce, tace still sunyi yawa yace toh ki barsu watarana zasu kare komin yawan su. Godiya tayi mashi sosai yace yasa haka basai kin gode ba..

Sallama suka ji su Rabi ne da sauran sabbin ma'aikata suka shigo suka fara shirya kayan abinci. Shi Dr fahad yawan good warmers in da yake ta gani ne da drinks yayi tunanin kilan akwai wani bako da zai zo daga baya bayan ya wuce don shi kaɗe dai bazai iya cinye abubuwan da aka kawo mashi ba.

Bayan sun wuce ne ta bude cooler guda sai kamshi ya zageye dakin, coolern fried rice ne da liver gashi yaji su spices don colour in rice in Yana daukar idon, ga wani chiken x egg salad. Sai pepper chicken da different chapman, gasu nan dai tsayawa lissafi ba zai yi ba.

Mamaki ya cigaba da cika shi, haka dai jadwa ta dauko serving tray mai kyau ta fara zuba abincin da ta gama tace Dr bismillah..

Dariya yayi yace my baby idan na cinye wannan abincin ai bazan iya tashi ba tare zamu ci ko?  Murmushi tayi tace a'a sai ta rufe fuska, uhmm yace ya fara ci amma yasan bazai iya cinyewa ba.. kadan yaci ya sha ruwa ya ma kasa shan chapman in ganin yace ya koshi.

Nan take jadwa ta bata rai ya bata hakuri ya dauko trayn abincin ya kara cin abincin ya sha chapman. Ta kara nuna mashi sai ya cinye duka nan ya ta magiya yana bata hakuri yace wlh idan ba so take yi cikin ya fashe.

Bayan ya gama suka yi fira ya gaya mata zancen lefe akan aunty tana so ta hada komai amma ya nuna mata cewa tare yake so yayi da amaryan shi saboda ita bata san choice inta ba..

Dariya sosai jadwa tayi tace "lallai Dr yanzu sai ka fadaa Aunty hakanan" ? Yace eh mana ai gaskiya akwai abunda baza ki son ba ita kuma ta ga ya mata kyau shi take so kinga ba choice inki bane kenan" sai tayi shiru ta kama murmushi. Sai chan tace "Ni wlh da kabar Aunty tayi komai nasan duk abunda tasa zai yi mun. Toh bari na bata kuyi waya dama sun ce yau na hadu suyi kuyi waya ana ta shirin biki har yanzu basu ji muryan surukar su a picture kawai suka ganta..

Da karfi jadwa ta ɗago kai tace "innalillahi wlh Dr bazan iya ba kunya nake ji don Allah ka bari sai munyi aure sai na nuje na gaisa da su." Dariya yayi ka yace jadwa Sarkin kunya toh ni Allah ya bani hakuri da na zo gaida mommy watau ni banda kunya kenan? A'a ta fada hmm yace toh shikenan zan fada masu surukar tana jin kunya.

Harda ajiyar zuciya jadwa tayi tana hamdallah.  Murmushi yayi yana kara jin son ta acikin zuciyar shi yana kara gode ma Allah.

Bayan sunyi fira kadan ya fara tuna mata akwatin da zai yi oder daga dubai sai ta zai bi wani light purple mai kyau. Shima wanda ta zaba ya mata mashi kyau yace "lallai amarya na ta iya zabi" sai tayi murmushi ta kama wasa da hannun hijabin ta.

Shiru yayi yawa a tsakanin su sai ta ɗaga waya ta kira mommy tana ce mata mommy mun gama ga mu nan zuwa. Mommy tace toh sai kun zo muna zaune parlor ai. Ok sai ta kashe waya ta juyo ta kalli Dr fahad tace Dr sweet muje koh? What did you just said ?? Wow sweet name I really like it.. sai ta ce da gaske ba tare da ta kalle shi ba sai yace sosai kuwa my baby

And In'sha'Allah I will continue calling you with it. Yace "I will really appreciate my wifey. Sai tayi dariya sosai sai suka mike suka bi har kofar hanya fita guest room suka wuce parlourn da sallama suka shiga jadwa ce a gaba..

Ma'assalama 🦋❤️
Unedited chapter, pls ignore mistakes
Don't forget to vote and comment

Yours khadss ❤️❤️

JADWA (Completed)Where stories live. Discover now