1-5

3.6K 160 5
                                    

*NAJWA*

BY *MARYAM S INDABAWA*
*MANS*

🌐HAJOW📝🌐

👩‍👧‍👧👩‍👧‍👧👩‍👧‍👧 HAKURI DA JURIYA ONLINE WRITERS✍🏾✍🏾✍🏾


*1-5*

Bismillahir Rahmanir Rahim
Alhamdulilah Allah kulli Halim.

Da sunan Allah mai rahama da jin kai duk kan yabo ya tabbata ga Allah da kuma annabin sa Muhammad (SAW).

Ina godiya da Allah da ya baninikon kammala *MIJIN UMMUNAH* Ya bani damar fara wani sabon littafi *NAJWAH*

To Alhamdulillah ina godiya ga rabbil samati wal ardi. Kuma ina rokan Allah ya bani ikon farawa lafiya tare da kammalawa lafiya
*Ameen*

Ya Allah ka jagorance ni wajen mika sakon da nake son mikawa. Allah ka shigen gaba.

Allah ka sa mu gama lafiya.
*Ameen!*

Yau gani na shigo da wani sabon littafi me suna *Najwa*

*ASMA'U HUSNAH* nayi niyar farawa to Allah yayi *Najwa* ne zai fara zuwa ina fatan zaku biyo ni cikin dan jin me ya kunsa

*Najwa* labari ne wanda na kirkire shi bakoyi rayuwar kowa ba.

Ni na zauna na tsara ban juua labarin wani ko wata ba. Hasali.ma sai zama da nayi na tsara.

In wani yaga nayi irin rayuwar sa to banyi dan shiba.

Ni na kageshi kuma ina fatan ya fadakar sannan ya nishadantar.
Allah yasa Ameen.

*Nagode*


.

Dedicated to u Sis *Rashida A Kardam.*
*Aunty Rash*

Allah ya daukakai ya sa kifi haka yasa ki gama da duniya lafiya. *Aunty Rash!*

Allah bar mu tare ya kara mana dankon soyayya da zumunci Sis *Rash*




Addu'ar ta gareki baza ta taba karewa ba. *Mahaifiya ta abar alfahari na a ko ina*

Allah sanyaya miki zuciyar ki yasa miki farin ciki ya saki a gidan aljanna.
*Mommy nah.*

Ur love make me feel like crazy.
So much love u dear tah.

Tnx for all ur supporting *Mamah!*

Kanwqta bazan manta dake ba. Kina sona kina taimakona. Kina ddamin gwarin gwiwa Nagode sosai.

*---*--*--*--*--*--*
Babban falo ne wanda ya hadu iya haduwa, Manyan kujeru ne a dakin bakake da ruwan zaiba.

Haka nan komai na adon dakin ruwan zaiba akai masa ado dashi.

Zaune take akan kujera, sai danta dake Kwance akan cinyar ta sai shaggwaba yake zuba mata.

Baki ne amman bakin nasa me mkyau ne, wanda ya dace da tsarin halitar sa ta ba fulatani.

Dogo ne sannan yana da faffadan kirji, Yana da manya idanu da dogon hanci bakin sa karami dashi, sai girar sa dake cike kansa ma gashi ne kwance irin na yan indian.

"Mami ni dai gaskiya muje kano wannan satin kinsan fa muna da bikin abokina."

Ya fada cikin shagwaba. Mami ta ce,
"Naki, bazani ba ince wancan satin ki kayi muje."

"Kiyi hakuri. Dan Allah!"
Najib ya fada yana daga kan kafar ta,

Mami ta ce,
"Aah in Dadyn ka ya yadda."

"Nasan zai yadda ma tinda sauran sati biyu ya dawo."

"Kai ni na fasa ma."
Mami ta faa tana kallon fuskar sa.
Fuska ya bata.

Ya ce,
"Mami na please kinji,"

Murmushi Mami tayi, ta ce,
"To shikenan zan fadawa Dadyn naka sai yadda mukayi."

Dariya yayi dan yasan Ddy ma kamar ya bari ne.
"Zan ma same shi tukunna."

Murmushi tayi Kawai.
"Wai kai sai yaushe zaka fito da matar auren taka."

Murmushi Najib yayi, ya ce,
"Mami ai kema kin sani. Addu'ar ki nake jira Allah ya bani irin wacce nake so."

Itama Mami murmushi tayi, ta ce,
" *Najib* kenan! Addu'a kullum munayin ta sai dai lokaci da muke jira."

Dariya Naijb yayi, ya ce
"Yauwah Mami na. Mami ina da son samun mace ta gari wacce zata kula da tarbiyar yara na."

"Allah baka *Najib* "
"Ameen!"

"Son kayi hankali da har kake hangen yarinya me tarbiya dan samun tarbiyyar yaran ka."

"Wallahi Mami, kyau bai dibata nidai nasamu yarinyar yar mutunci me hankali da nutsuwa, mai ilimi kuma me amfani da shi"

"Masha Allah! Nima zan samu zuri'a ta gari kenan. Allah ya baka mace ta gari."

Juyar da kansa yayi, yana kallon ta, sannan ya ce,
"Ameen! Mami nah. Bari naje nayi wanka zan fita."

"To *Najib* "

Fita yayi ya nufi bangaren sa. Waje ne guda wanda yake kamar gida. Daki ne guda daya na bacci sai falo da ban daki a falo da cikin daki.

Dakin a gyare yake sai kamshi dake tashi. Komai na dakin fari ne tas dashi. Kamar a lokacin aka zuba su.

Ban dakin sa ya shiga yayo wanka ya dauro alwala.

Yana fitowa ya goge jikin sa ya zauna ya shafe jikin sa da mai me kamshi ya feshe jikin sa da turaruka.

Farin jeans ya dauko da farar T-shirt sai takalmi boot da ya saka shima fari. Glass ya dauko, fari tas dashi ya saka.

Turare ya kara fesawa sannan ya fito falo. Gefen Mamin sa ya zauna.

Mami ta kalle shi, sannan ta ce,
"Masha Allah gaskiya yaron ya hadu, kyaun sa ya kara bayyana.

Murmushi yayi, yace,
"Mami nayi kyau kenan."
"Masha Allah! Kayi kyau yaro na."

"Nagode bari naje."

"Ince gun suruka ta zakaje,"
Mami ta tambaya da tsokana.

Murmushi yayi, ya ce,
"Mami ban da ita ai. da nayi Budurwa ke zan fara fadawa"

"Allah ya sa."
"Insha Allahi!"

Ya fada yana mikewa. Kumatun sa ya mika mata.

Sumbatar sa tayi. Murmushi yayi.
"Nagode Mami na sai na dawo.

Harabar gidan ya nufa, katon waje ne wanda zaici akalla motoci guda goma.

Wajen wata mota ya nufa, baka wulik da ita, sai sheki take yi.

Drivern gidan ne, ya nufoshi da sauri
"Barka da zuwa Alhaji. Dan Alhaji."

Murmushi yayi, ya ce,
"Ya akayi dan juma."

"Ranka ya dade ina zuwa kuma."
"Gari zan dan zaga."

"Nazo na kai Kane."
"A'ah aboki na. Nagode sai na dawo."

"Toh dan gidan Alhaji. Allah kiyaye hanya Allah ya dawo dakai lafiya."
"Ameen! Ga wannan."

Ya zaro kudi a aljihu ya mika masa.
"Nagode Alhaji nah."

"Ba komai."
Ya bude masa kofa, ya shige.

Baba me gadi na hango sai ya bude masa gate
"Sannun ka dan Alhaji. Allah kiyaye hanya."

"Ameen Baba ya aikin."
"Lafiya Alhamdulillah."

"Kai ma ga wannan kaci goro."
"Nagode Alhaji Allah kara budi da daukaka."

"Ameen!"
Ya fice.




*INDABAWA*

NAJWA Complete ✔Where stories live. Discover now