142

676 44 0
                                    

*NAJWA*

BY *MARYAM S INDABAWA*
*MANS*

🌐 *HAJOW* 🌐
*Hakuri da Juriya Online WRITERS*

DEDICATED TO *RASHIDA A KARDAM*
*AUNTY RASH*

*ALLAH DAUKAKAKI YASA KI GAMA DA DUNIYA LAFIYA.*

*REALLY LOVE U ANTY NA*

*THANKS FOR UR LOVE ND SUPPORTING*

*PAGE*
*142*

Maman Nur, tnc for ur love nd supporting. Reallly appreciate.


"Hamma na zata mun gama wannan maganar."
"Akan me muka gama?"

"Nace mu hakura ko?
"au bama kiji abinda na fada ba kenan. Ni bazan iya ba toh."

Zatai magana ya ce,
"Bana son kice komai, kuma ni bazan taba barin ki ba."

Mikewa yayi, ya kalle ta, ya ce,
"Tashi mu tafi."

Mikewa tayi jiki a sanyaye, tabi bayan sa.

Mami da Dady har dasu Salim suna falo suka shigo.

Basma ce tayi gun ta a guje tana, cewa,
"Adda sannu ya jikin?"

Hannun ta, ta kama ta ce,
"Naji sauki."

"Sannu Adda!"
"Yauwah."

Suka karasa cikin dakin. Mami ce ta mike ta kamo ta sukai sama.

Ruwan wanka ta hada mata sannan ta fito mata da kayan da zata saka.

Kasa ta sauka ta hado mata abinci, sannan ta kawo mata.

Tana fitowa ta shirya ta haye gado dan baza ta iya cin komai ba.

Har karfe goma Najib na gidan, da ya tashi zai tafi Dady ya ce, sai ya kwana a gidan.

Kafin ya kwanta sai da ya leka dakin da take, tana kwance ta juyawa kofa baya.

Shiga yayi a hankali, leka fuskar ta yayi yaga hawaye na zuba.

Juyawa yayi ya tafi daki  Salim. A ransa yana mamakin Najwa, a ce mutun yana son abu amman ya gwammace ya hakura da abun.

In har ya biye mata akan a rmabun yasan daga shi har ita baza suji da dadi ba.

Wayar sa ya dauka ya kira ta. Sai da ta kusan tsinkewa ta daga.

"Me kike yi?"
"Ba komai."

"Aah Najwa ban sanki da karya ba."
"Hamma dan Allah ka bari."

"Me zan bari me nayi?"
"Ni zaka bari, kuma ka daina damuwa da halin da nake ciki."

"Tayaya zan barki, bayan kina kuma ko bamuyi aure ba dole muna tare. Tayaya ma kike son na daina damuwa dake. Dan ke zaki iya shine kike son nima na daina...."

"A'ah haba Hamma amman kasan nima na  damu dakai da duk lamuran ka, kasan dai ina son ka ko?"

"Anya? Gaskiya ban tabbatar ba tinda kike neman sani a wani hali."

Kuka ta fashe masa dashi ta ce,
"Basan ya zanyi ba. Ni wallahi ban sani ba."

"In fada miki abinda za kiyi."
"Eh!"

Ta fada da sauri.
"Kicire damuwa aran ki, ki bar ni na saka miki farin ciki a rayuwar ki. Ki bar komai a hannu na."

"Hamma..."
Katse ta yayi ya ce,
"Bana son jin komai. Kije ki kwanta sai da safe."

Ya kashe wayar, kasa kukan ma tayi, ta rasa me yake mata dadi da tunanin da zatayi.

Ji take kamar bata da damuwa, to amman bata san me zaije ya dawo ba.

NAJWA Complete ✔Where stories live. Discover now